*Kano.*
"idan ka gama ka kulle masallacin". limamin masallacin da ke tsaye akan Alhussain ya ce da shi. Alhussain da kansa ke ƙasa idonsa akan ƙur'anin da ke hannunsa yana karantawa bai ɗago ba sai da ya kai aya tukunna. sana ya ɗago da kansa da ke masa bala'in nauyi ya kalli Liman ya amsa mishi da,"Tom Malam".Har Liman ya kai bakin ƙofa sai ya dawo ya duƙa ya ajiyewa Alhussain naira 200 a kusa da shi. tsawon wucewar mintuna talatin sannan ya kammala karatun ƙur'anin, ya shafa adu'ar da yay sannan ya mayar da ƙur'anin ya kai cikin durowa ya aje. Ya dawo ya tsuguna ya ɗauki kuɗin da Liman ya aje masa yana tayi masa adu'a cikin ransa. sannan ya fita ya rufe duka ƙofofin masallacin ya ɗora mukullin a inda ake ajiyewa. bayan sallar isha'i ne lokacin, dan haka unguwar ta daɗa yin shiru sai haushin karnuka da ke tashi, haka kowanne layi duhu saboda rashin wutar nepa. tafiya yake yana takawa a hankali saboda yanda ƙafafunsa ke yi masa tsananin ciwo, haka har ya fito bakin titi, anan ya hangi wata ƴar tsohuwa mai siyar da tuwo ya ƙarasa wurinta ya saya tuwo da miya na ɗari, a wurin ya zauna yaci sannan ya tashi ya koma bakin masallaci inda yake kwana anan yanzu tun bayan fitowarsa daga cell.
Kuma a wannan zaman da yay ne gyangyaɗi ya fara ɗaukarsa, cikin baccin da ke neman ɗibarsa yaji kamar hayaniya, don haka ya buɗe idonsa da sauri, dai-dai lokacin da motar ƴan sanda ta tsaya a wurin, a gabansa, ƙwayar idonsa akansu ta sauka. bakinsa da zuciyarsa suka shiga furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un lokacin da yaga Ƴan Sanda na tunkaro shi, wasu matasa kuma a tare da su na faɗa musu cewar,"ehh shine, wallahi shine".
Kalmar shine ta bada tartsatsin tsawa acikin kansa, yaja numfashi ya sauke tare da lumshe ido. a cikin duhun idonsa abunda ya faru da shi kwanakin baya da suka shuɗe ya shiga haska masa, ko kaɗan baya fatan hakan ta ƙara maimaituwa masa, ko da a mafarki ba ya fatan ƙaddara ta ƙara kaishi hannun ƴan sandan. zuciyarsa a yanzu faɗa masa ta ke akan ya tashi ya gudu, ya tashi ya gudu tun kamin su cimmasa, bai san dame suka zo ba wannan karan, idan har ya ƙara shiga hannun hukuma ta ya za'ai ya fito?.
Ya buɗe idanuwansa ya suke kan ƙafafunsa biyu, ɗaya ta kumbura suntum ɗayar kuma ta ɗan sace ba kamar da ba. ya ƙara maimaita kalmar innalillahi a cikin ransa, ko da ace ya miƙe tsaye, ko da ya ce zai gudu, la shakka babu inda zai kai ga ɗora ƙafarsa zasu cimma masa, da ƙyar yake takawa, irin takun da ko kusa ko kaɗan ba zai iya yin gudun kirki ba. maimaituwar kalmar innalillahi a bakinsa ta haɗe da damƙwar kwalar rigarsa da ɗan sanda yayi, ya fizgo shi ya miƙe tsaye, sannan ɗayan ɗan sandan da ya ƙaraso shi da wasu mutane ukun da bai san su ba ya kama hannunsa ya saka masa ankwa. sannan suka tasa ƙeyarsa zuwa cikin mota suka tafi.
_"Gani nan Yaya, Yaya gani nan, ba zan bari su maka komai ba, kai fa jarumi ne kar ka bari ƙwallar ta zubo don Allah"._
Maganar da ya ji na shiga kunnensa kenan, muryar Sabina ce, amma Daga ina? Tana ina? Ya akai ta san halin da yake ciki? Ko kuma imagination ɗin da ya saba ne? A hankali ya rumtse ido da ƙarfi ya kuma buɗesu, a cikin motar dai yake, cikin motar nan dai da ya ji ana faɗar direct gidan gyara hali za'a kai shi, kuma a wannan karon idan yaje babu me fito da shi yasan da wannan.
Bai san lokacin da ya daki kansa da jikin motar ba, in ace tasan abunda ta ke haifar masa a ruhi da dukkan jiki da ta hana ganinta da jinta suna yi masa gizo, da ta hana sunanta ambatuwa da maimaituwa acikin zuciyarsa da ƙoƙon kansa. kuma buguwar da yay a wannan lokacin shi yay sanadiyar ɓallewar jini daga kansa, saukar jinin da yay sanadiyar tsayawar komai acikin kansa, ya daina ji da ganin komai sai ɗaga hannu a hankali yana miƙa shi alama na yana buƙatar taimako.
*Abuja.*
"Haka za ki fita ba ki ci komai ba?"."Ina tsoron layi ne shiyasa, idan naje can ɗin na samu resturant a kusa sai na saya na ci".
"Hakan yayi, a dawo lafiya. Idan kinga mutane ba sauƙi a wurin ki dawo ya ba ki kuɗi a hannu kawai sai ki amfani da shi".
"Amin..tom Gwaggo". Na amsa ina gyara yafa mayafina. Da sauri na fito compound, ina zuwa na tarar motana babu mai, na daki ƙafa ina jan tsaki, ni yanzu ya zanyi? Shine tambayar da nayi ma kaina, ga Yaya Abba ba ya nan, ni kuma bana son kula Yaya Haidar bare na ce ya ara min tasa, to ya zanyi dole haka zan haƙura na je wurin nasa tunda dai babu wata motar a ajiye sai ta matan gidan, su kuwa ba shiri muke ba bare na ce zan ari tasu, shi yasa nacewa Baba a ɗaukar mana driver a aje, yace a'a bai da amfani tunda dai kowa ya iya motar nan kuma ga Yaya Abba da Yaya Haidar ma, shi bai fi ya yarda da direbobi ba.
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...