Maganar da Malama Muhsina tayi min yasa gabana faɗuwa, na dafe goshi cikin fargabar abunda ka iya faruwa da ace basu lura da rashin rubuta sunan nawa ba. Shikenan na jawa kaina matsala sai na ƙara maimaita course ɗin duk uban sauqin da yay, wallah shaf ni na manta da batun suna saboda zumuɗin fara amsawa, daɗin tambayoyin ya mantar da ni. na bawa Malama Muhsina haƙuri na amshi script ɗin na duƙa ina rubutawa, haka kawai sai na tsinci gabana da ƙara tsananta faɗuwa a lokacin, ga kallon da na ke ji a jikina yay yawa, naja tsaki ni ɗaya, sannan na ɗaga kaina sama nayi harare-harare da murguɗe-murguɗe, yanzu kam dai koma waye me min wannan uban kallon nasan ya gani ya kuma san da shi nake, haba su mutane ba su iya kallo kaɗan ba.
Na ɗago hannu na rawa na miƙa mata.
Rannan nata a haɗe kaman ma so take ta zaneni. Sai na ƙara jin haushinta ya kama ni, ni dai adu'a kawai na ke a raina kar ta janyo jalli joga in shiga uku a gida, don nayi carrying course ɗin nan ai na mutu.Buɗar bakina zance "Sorry Maa". Sai ta riga ni da cewa,"Give me your ID card".
Ta faɗa tana miƙo min hannu, na miƙa mata ta duba abinda zata duba ta bani na wuce na fita. A ƙofar class na tsaya jiran Intisar, babu daɗewa itama ta fito, hangoni ya sata ta fara dariyar da ke ƙunshe da murna, tana ƙarasowa muka tafa da ita, exams dai tayi mana daɗi gaba ɗayanmu, muna tattaunawa akan wata question sai ga wata ƙawarmu ƴar carryover ta fito, muka jera muna tafiya.Intisar ta ce,"kalla wani bawan Allah, kyau iya kyau sai dai babu ƙafa, Allah kenan".
Muka juyo ni da Rahinat don kallon mutumin da take magana akai, ana tura shi a kekensa na guragu, har sun wucemu, kamar ɗazu dai bayansa kawai na gani, cike da tausayawa na ce,"Allah sarki wallahi nima ya bani tausayi, har ƙwalla sai dana masa ɗazu, kamar shine muka yi exams tare ko?".
Na faɗa da muryar tausayawa ina daɗa bin bayansa da kallo.
"ehh shine".Intisar ta faɗa."baki ga akan stage aka ɗora shi ba daga shi sai halinsa, wannan exams idan baka yi karatu ba ai kana tsakiyar ruwa".
Rahina ta ce,"ku he is not a student woo, He is the Financial Accounting lecturer, baya ɗaukan ƴan Level one lectures sai level two, bayani ne zai zo yay maku verbally using projecter, ita Malama Muhsinar ai ƙanwarsa ce, ita ke karɓa masa a L1 nd also she is the one taking care of him at school".
"Eyyah Allah sarki, Allah ya ba shi lafiya".
Muka faɗa a tare ni da Intisar.
"Amma dai bai da mugunta ko?".
Na tambayi Rahina ina waro ido waje."ehh to gaskiya ba shi da mugunta, amma fa ya iya tsara questions, ai ma kun gani yanzu, kuma ga shi da fara'a murmushi har tunbuɗinsa yake, kuma ba'a faɗuwa course nasa gaskiya saboda kunga yadda ake dagewa, nima ƙaddara ce ta dawo da ni".
Muka ci gaba da tafiya muna hirarmu, daga bayanmu muka ji ana mana magana, muka dakata da tafiyar muka juyo. Saurayin ya ce da ni,"Beauty Malama Muhsina is calling you".
Ya faɗa yana nuna ni. Na kallesa ina yamutsa fuska saboda ranar data haskemu. ina nuna kaina na ce,"kuma ni ta ce ka kira, ai ba sunana Beauty ba, sai dai ko ƴan gabanmu ta ke nuna maka".
Na faɗa ina maida kallona ga ƴan gabanmu da ke tafiya. Murmushi naga yayi yana cewa,"na san ba ainihin sunanki bane, nima ce tayi min na kira mata beauty gata can tana tafiya with pink veil, ai farko da na kira ku Sisters ku ka ji ina cewa ko?".
Su Rahinat suka ce masa "ehh". Ya kuma cewa,"to da ku ka juyo na kalleki sai naga ehh lallai kin cancanta da a kira da suna Beauty, hakan yasa nima na ɗana. Allah ya tsare miki wannan kyawu naki".
Ya faɗi hakan yana wucemu. Na kalla su Intisar da suke kallona suna murmushi, na sauke numfashi cikin damuwa na ce.
"sarai kun san Malama Muhsina bata da kirki, maimakon ku tayani jimami ku abin ma daɗi yay maku, ban san kiran akan mene ba Allah dai yasa ba laifi na mata ba".
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...