*(3)*
Da wannan tunanin ya samu wuri ya zauna, zuciyarsa tana cigaba da tunani iri-iri, tunanin duniya, tunanin rayuwarsa da tunanin yarinyar da ta fara raɓarsa tun bayan sanin ciwon kansa da yayi.
Motar Farhana na tsayawa ban ce komai ba na buɗe murfin motar na fita cikin fushi ba tare da na dubi inda take ba, can ƙasan murya na furta,"Nagode ki gaida su Momi".Tace da ni,"Zasu ji insha'Allah, amma ba ki ɗauka kayan da muka saya ba”.
Wani irin kallo na bita da shi ta ƙasan ido, ban ko yunƙurin amsa mata ba, dan abunda ta yiwa wancan bawan Allah'n ji na ke tamkar Yaya Abba da muke ciki guda ta yiwa, shi yasa tun tahowarmu na ke fushi da ita, kuma ina ganin kaman ba zamu shirya ba har sai mun koma wajensa ta ba shi haƙuri yace ya haƙura tukunna.
Ban rufe mata ƙofa ba sai da na ja tsaki tukunna na fara tafiya na ɗauki hanyar gida, ganin hakan yasa Farhana fitowa daga motar ta buɗe but ta ɗakko kayan da muka saya ta biyo bayana da shi.A ɗan ƙaramin tsakar gidanmu wanda yasha shara baka ganin ko da ɗigon datti na tarar da Gwaggo tana goga kuɓewa, sallama kawai nayi na shige ciki, ban ma san ta amsa ba ko bata amsa ba, kuma ajikina nake jin yanda Gwaggo ke bin bayana da kallo, kuma shirunta ya bani tabbacin tana tunanin yanayin da ta ganni a ciki ne. Farhana ta shigo, Gwaggo ko amsa sallamarta ba tayi ba tace mata,“Yauwa yanzu kuwa zance to ya akayi ba ki shigo ba, ashe kina bayanta, meye sameta ne? Naga daga sallama ta shige ciki, Allah yasa lafiya ne".
Farhana tace,"lafiyarta lau, ai kin san halinta da ɗan banzan saka damuwa a rai, wai fa wani mahaukaci ta gani a hanyarmu ta dawowa gida shi ne ta ɗaga hankalinta haka".
Ta duƙa a gaban Gwaggo ta aje ledar hannunta da cewa,"Ni dai zan wuce Gwaggo sai wani lokacin, ga shi wannan nata ne”.Gwaggo ta maida hankalinta kan kuɓewar da ta ke gogawa tace,"To madalla, kyace ina gaida Hajiyarku”.
Daga haka Farhana ta gyara zaman glass nata ta fice. Maganar Farhana ta tsayawa Gwaggo a rai, don kuwa sarai ta san halin Sabina, zata iya yin komi akan wannan mahaukaci kamar yadda Farhana ta faɗa mata, to amma meye nata na damuwa haka, koma meye dai zata ji.
Ina kishingiɗe jikin pillow naji Gwaggo na Ƙwala min kira, kaman ba zan amsa ba sai kuma na buɗe baki nace da ita ina zuwa, na miƙe jiki babu ƙwari kamar mara lafiya na fito. Na rakuɓe gefe guda ina jiran abinda zai fito daga bakin Gwaggo, abunda naji tana faɗi ne yasa na ɗaga ido ina dubanta."Wanne Mahaukaci ne wannnan har da zai ɗaga maki hankali haka?, Sabina kin san halina fa sarai, ina da sauƙin kai amma bana son shashanci, waye shi?”.
Sai naji zuciyata tayi min nauyi saboda kalmar mahaukaci da Gwaggo tayi amfani da ita wurin kiran Yaya da shi, na turo baki gaba ina daɗa dubanta ta cikin gilashi nawa nace. “Don Allah ku daina kiran shi da mahaukaci, baku san yadda zuciyata ta ke duka ba, kalmar mahaukaci ai bata danganci mutum musulmi ba, mahaukaci ai sai dabba, shi kuma mutum ne mai kamala, don a maganar shi bata yi min kama da mai taɓin hankali ba, kawai halin rayuwa ne ya mayar da shi haka”.
Zuru Gwaggo tayi tana dubana, maganganuna sun bata mamaki matuƙa gaya, cikin faɗa-faɗa ta kama cewa,"Yo wai ke shin kin yi hauka ne, a ina ma kika ganshi ne tukun har kike faɗin haka, kin san dai Farhana ba zata maki ƙarya ba ko?”.
“Gwaggo Allah ba mahaukaci bane, kawai dan ta gan shi a cikin kango kan bola shikenan sai ta kira shi da mahaukaci, idan ita aka faɗawa ɗan uwanta haka ai ba zata ji daɗi ba, ni idan bata yi wasa ba ma sai na daina kulata akansa wallah”.
Gwaggo ta wurgo min daƙuwa tana faɗin,"Ungo wannan, nace ungo, yau naji Mace, ke anya ma kuwa da kike je wurin shi bai shafa maki haukan ba, wannan wace irin macece ke, wai ke ba ki san duniya ta lalace haka ba, waye ke yadda da irin su musamman ma masu zama cikin kango, wannan waya san adadin yaran da ya lalata da ya fake a cikin nan, kar na sake jin wannan maganar a bakinki, kar in kuma jin kin amabace shi da sunan Yayan ki balle damuwa akansa...ince ko kin jini da kunnen fahimta?”.
ВЫ ЧИТАЕТЕ
AL-HUSSAIN Complete
Исторические романы*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...