8

101 10 1
                                    

*(8)*
Ba zato muka ji Gwaggo ta rangaɗa wata uwar guɗa da ta amsa a gaba ɗaya cikin gidan, hamdala take ta jerawa ga Allah, har da miƙewa ta taka rawa irin tasu ta tsofaffi.

"Allah maji kukan bayinsa...kai gaba ɗaya ma na rasa wacce iriyar murna zanyi".

Yaya Abba da ya shigo yace da ita,"tsohuwa kina ta ihu fa dare ne, maganarki har soro, dama ke muryar kamar cakwaikwaiwa".

Tace da shi,"Umm Abba ai yau sai dai kayi da wata bada ni ba kam...dan lokacinka dai ban da shi".

Murna na ke yi sosai kamar babu gobe, ƙawata Farhana tamkar na ta mahaifin don tuni ta koma kusa da Baba ta zauna tana tayasa murna da adu'a.
Sai na ƙara jin sonta saboda yacca take ɗaukar kanta ba kowan komai ba, haka kuma ta ɗauki iyayena kamar nata. Ina tsaka da farin ciki haka kawai sai na tsince ni da faɗuwar gaba.

Lokaci guda kuma yanayina ya sauya, a sanyaye na nemi wuri na zauna, ni ba farin ciki ba kuma ni ba akasinsa ba, rashin jin daɗin da ya ziyarcen tamkar mara lafiya. Na rumtse ido ina mai kwantar da kai jikin kujera, kamar jira sai hoton fuskar mutumin can ya haska min, ba iyaka ƙwayar idona ba, hatta zuciyata sai da ta amsa dalilin tunawa da shi.

Na sani Allah ya haɗani da shi ta ayar da ban san fassararta ba, ina ji ne a jikina kamar ina da wata babbar alaƙa da shi, tun a ranar farko na ke jin tasirinsa a tare da ni a kullu yaumin na ƙaruwa, tunaninsa kaɗai na sakani taruwar ƙwalla saboda rashin sanin wanne hali yake ciki tun daga wancan ranar da ban ƙara komawa wurinsa ba.
Ba komai ya saka jikina mutuwa ba sai tunawa da nayi idan fa na tafi shikenan ni da shi wataƙila har abada, wannan gajeran tunanin shi wanzar da tashin hankali a cikin ƙwaƙwalwata da girgizar allon ƙirjina.

Yanda na ke jin sautin bugun zuciyata ban taɓa tsammanin ba fitowa waje zata yi ba, yatsu biyu na kai na goge guntun hawayen da ya sakko min, wai shin ya zan yi ne ni kam? Ta ina zan fara?
Bisa dole na daidaita nutsuwata saboda ina gaban wanda ba na son ya fahimci yanayin da na ke ciki. Dan duk wanda ya kallen a yanzu dole sai ya gane i already lost my mind. Na kai idona kan Farhana ina ganin yadda ta kafe ni da idanunta.

"Yauwa Baba bari na zuba maka ruwan alwala, na kalla magriba ta gaba to".
Ina gama faɗar haka na miƙe na nufi hanyar fita, idon Farhana na kaina har a lokacin, yayin da Gwaggo take ta faman zuba kamar kanyar da ta samu jeje da iska.

Ina fita na kifa a jikin bango, so na ke na hana hawayena zuba amma fa sam hakan ya gagara, don tuni hawaye sun fara zubo min, dama ni Allah ya hore min su kamar ruwan teku, hawayena a wajen tausayi da rauni ba su da wahalar sauka. ina zuba ruwan na dawo, na samu gefen Gwaggo na zauna ina sauraron hirar ta su, ba wani fuskantar hirar na ke ba, tunanina da neman mafita bai wuce yadda za'ayi tafiyar nan tare da Yaya ba.

Kallon Farhana nai, nayi mata sigina da ido, saboda mu fita mu samu abin faɗa, amma sai naga ta basar kamar bata ganni ba. Ganin haka yasa na miƙe na kama hannunta ina faɗin,"Tashi mu shiga ciki".

Muna shiga ɗaki ta dube ni sheƙeƙe tace,"Ya dai uwar ɗorawa kai damuwa".

"Ke kuma da fassara abu, ƴar rainin hankali to meye nufinki dama?".

Ta ɗan harare ni tace,"Oh oh ji min rainin tunani, ke zan tambaya dai meye ke damunki, na ganki sukuku, don tun ɗazu na fuskanci damuwar da kika shiga ana tsaka da farin ciki".

Na ɗan ja ƙaramin tsaki kaɗan na miƙe tsaye ina safa da marwa kana na kama ƙugu na tsaya nace,"Ba za ki gane ba Farhana, kin san halina sarai, ina da saka damuwa akan abinda nasa a raina but..".

Ban ƙarasa faɗin abinda zance ba Gwaggo ta bankaɗo labule tana faɗin,"An kira sallah ko baku ji ne wai, ko kuwa ba zaku yi ba ku duka?".

Nace,"kaii Gwaggo mai baiwa, yo banda abinki Gwaggo kuma anyi ta rashin sallar kenan?".

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now