Bakin wani tangamemen gate motar tasu ta tsaya ƙirar lexus, kallo ɗaga zaka yiwa gidan kasan ba ƙanan mutane ke rayuwa cikinsa ba, dan tun daga farkon estate ɗin zaka san its not possible ma talaka ya shigo shi, iyakan tsaruwa gidan ya tsaru kamar a ƙasar turai, ƙaryar baki yace zai fasalta haɗuwar ginin, gaba ɗaya wajensa kewaye yake da wasu irin flowers masu ƙawata kyawun wuri.
A yayin da mutanen da ke cikin motar fuskokinsu ke cike da annashuwa. driver ya danna horn da sauri gate man yazo ya buɗe, suna shiga kai tsaye wajen entrans shiga main part na gidan driver yay parking motan, ƙasan wajen gaba ɗaya shimfiɗe yake da grass carpet sai hasken fitilu multi colour da ke haska wurin sai kace hotel, driver ya fito cikin sauri ya buɗe booth ya ɗauko wheel chair, sannan ya zo ya buɗe ma Muhsin murfin motar, sai dai bai fito ba yana zaune ya ɗauko waya a aljihunsa yana dialling number. daga cikin kantamemen parlon gidan irin 100 by 100 ɗin nan, parlon ya gaji da haɗuwa kamar ba za'a mutu ba, kewaye yake da wasu lumtsatstsun cushions na alfarma, a cikin ɗaya daga cikin cushions ɗin mai zaman mutum guda, farar dattijuwar Mata ce kyakykyawa da ka ganta ka ga shuwa arab, ta dubi agogon gwal ɗin da ke hannunta, ta sauke numfashi, damuwa a tattare da ita ta ce,"Muhsina do you look up the time? Your brother is still not yet back, duba ki ga har da additional five minutes on his return time".
Muhsina na zaune kan ɗaya daga kujeran dining tana cin fruit ta ce,"Mom! Abinda ke raina tun ɗazu kenan, but he might be on his way back ko kuma ya tsaya wurin seminer da Daddy yace zai je".
Mom ta ce,"I don't think so, he could have informed me if that was the case. wayansa ma fa not recherble gaba ɗaya, fatana Allah ubangiji yasa lafiya".
She spoke in anxiety way har tana jin ƙirjinta na beating faster.
"Ni fa am worried da rashin dawowan yaron nan har yanzu, is everything alright? Baba he's a determined boy, banda haka mene zai sa shi fita aiki? Ya zauna wuri guda tunda ubansa ya tara dukiyar nan ya ajiye musu. anyway to ya dawo yau ɗin ya same ni".Tsohuwar Matar da ke sakkowa daga stairs ke wannan maganar cikin faɗa, sanye take da lapaya orange colour fuskarta kuma ɗauke da glass me yanayin na fashions amma kuma medical ne, kana kallonta kaga mahaifiyar Mom saboda tsananin kamansu, Mom da Muhsina suka maida duban su gareta. ta kuma cewa,"Fa'iƙa zaman me kike da ba za ki tashi muje dubo shi ba? Yaran da ba cikakkiyar lafiya gare shi ba".
Mom ta ce da mahaifiyartata,"Anie ai driver ya tafi ɗakko sa, not knowing the reason for their returning early shine yafi damuna, bai taɓa kaiwa wannan lokacin a waje ba. ga wayoyinsa duka basa tafiya".
Anie ta numfasa ta ce,,"shi drivern babu waya hannunsa ne da aka gagara tuntuɓarsa aji halin da suke ciki?".
Dukansu basu kai ga kuma furta ko wacce kalma ba wayar Muhsina ta fara ringing, ta ɗauka da sauri tana cewa,"yauwa Mom ga shi ma ya kira".
Daga ɓangaren Muhsin ya ce,"Sister am back".
Yana faɗin hakan ya kashe wayan. dukansu suka sauke ajiyan zuciya, sai yanzu nutsuwa ta samu a gare su hankalinsu ya kwanta, lallai ba ƙaramin ji da shi ake a wannan gida ba, minti biyar kawai ya ƙara akan lokacin dawowansa amma hankalin kowa ya tashi, ana tunanin ko ba lafiya ba, tabbas shi ɗin ɗan gata ne gaba da baya.
Anie ta ce,"lamarin Hassan sai shi, wato har yanzu idan ya dawo dole dai sai Muhsina taje tarbo shi tukunna zai shigo".Mom ta ce,"ai haƙurinsa ɗaya idan bata nan anan kuma dole ni ce zan fita. ya ce damuwa yake shiga indai yagansa shi ɗaya yana tafiya a keken nan, kuma baya so yake saka ma'aikata turo shi".
Muhsina na isowa entrance ta iske Mami na balbalin masifa, ita dai wannan mata kwai jarababba, ko da yaushe a cikin masifa ta ke muddin wani abu zai shiga tsakanin ƴaƴanta da na kishiyarta, Muhsina tayi tsaki taja ta tsaya cike da takaici, ta tsaya ne kawai saboda Mom ta hana su saurarenta idan tana wannan haushin karen, amma da bata isa ta tsaya kan Brother tana masa wannan hargowan ba. Khaleesat ita dai ƙuri tayi ta rakuɓe daga bayan keken Muhsin, ita kanta yarinyar bata son wannan halin na uwarta, sai noƙewa takeyi gudun karta kawo mata duka, muryarta a hankali ta ce,"Mami kiyi haƙuri please".
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...