5

117 13 2
                                    

*(5)*
Haka na yi ta masa zuba kamar aku sarkin magana, bai fiya tanka min ba sai dai in ta tsintar sautin murmushinsa. Ina ta ba shi labarin irin ƙoƙarina a islamiya.

Jin shirun yay yawa na ɗago kai na kalle shi, karaf ƙwayar idonsa cikin nawa, kenan tun ɗazun ma kallona yake yi, a hankali na ce,"Yaya ka barni ina ta magana ni ɗaya".

Bai ce da ni komai ba, na kai hannu zan dage niƙab ɗina sai ganinsa nayi yasha gabana da sauri, yana kallon gefe da gefe yace,"Don Allah kar ki cire".

"Yaya zafi fa".

"Kamar an kusa fita titi, ki yi haƙuri da kinje gida sai ki cire ki ta shan iskarki".

"To ai Yaya kai ne ina ta magana baka ce min komai".

"Zan ke cewa komai ɗin, amma sauke niƙab ɗin kinga akwai mutane suna hangenmu, bana so su ganki tare da ni suyi miki mummunar shaida irin wacca suke min, ba zan iya yafewa kaina ba idan aka fassaraki saɓanin yanda kyawun ɗabi'arki su ke".

Allah ya sani duk abinda na ke yi ba son ina sanin ina yin ba ne, samun kaina na ke yi da aiwatar da komai kawai. Na marairaice fuska zan yi magana sai na ga ya kulle ido kafin yace,"Ki maida niƙab ɗin zan fi sauraron abinda kike cewa, ba kuma zan kara yi miki shiru ba har mu rabu, zan ta magana irin na ki".

Samun kaina nayi da yin murmushi me faɗi wanda har haƙorana sai da suka bayyana dukka a waje. Na saki niƙab ɗin, nan ya matsa daga gabana muka jera muna ci gaba da tafiya. Ni dai ban ce komai ba, shima ɗin haka har sai da muka kusa isa titi naji maganarsa kamar daga sama yace,"Allah ya ba da sa'a, da yardan Allah ke za ki yi nasara, fatan alkhairi".

Sosai naji daɗin adu'ar, na amsa ina me cike da farin ciki. kuma har muka isko titi ba wanda ya ƙara magana. Zuwan namu ne muryarsa ta fito a hankali da cewa,"Sai kin hau mota?".

Na ɗaga kai da ba shi amsar,"Ehh ai ba anan anguwar na ke ba, muna da ɗan nisa".

Na jiyo sautin sauke ajiyar zuciyarsa, kafin yace,"Ban taɓa tsayar da mota ba tunda na tsinci kaina a wannan yankin, yau ne zai zamar min karo na farko".

Da mamaki na ce,"Yaya to baka zuwa ko'ina ne?".

"Wani lokacin na kan ɗan gaji da zan wurin da na ke, to sai na yi ta yawo doguwar tafiya ma ba tare da na san ina na ke zuwa ba, wani sa'ilin ma wajen dawowa har hanya ta kan ɓace min".

"Memakon ka hau mota Yaya". Na faɗa cike da tausayinsa.

"Masu mota na ɗaukar mutum a kyauya ne? Na taɓa kama sana'ar sai da ruwa, idan na fita zan yini ina tura kura babu me siya, wataƙila ina da wani mummunan aibu a jinina ne, za ki ke saka ni adu'arki ta yau da kullum?".

"Ka ɗauka hakan matsayin wani babban nauyi da ya rataya a wuyana, daga yau kaman yanda na ke adu'a wa mahaifiyata, haka kai ma zan ke maka".

"Nagode, Allah yayi miki albarka".

Da jin daɗi na ɗaga ido na dube shi na ce,"Amin". Sai yace,"Nima ki faɗa min, ban taso na taɓa jin wani yace da ni Allah yay maka albarka ba".

"Allah yay maka albarka, Allah kayi ma Yayana albarka, Allah Yayan da ka bani ta wata silar ina roƙonka da ka lulluɓe rayuwarsa da Rahmarka da albarkar ka".

Yanayin da ya bayyana a saman fuskarsa ba zan iya tantance tarin ma'anar da ke cikinsu ba, sai da na san kawai yaji daɗin adu'ar.
Haka ya miƙa hannunsa na rawa ya tsaida me napep ɗin da ya taho, kana kallon yanda yake tsayar da me napep ɗin da yanda yakewa mai napep ɗin magana zaka san farin shiga ne, don tsoro ne fal a tare da shi, kaman dai wanda ya aika laifi ya gudu ya ke gudun a kama shi.

Ni na faɗawa me napep ɗin unguwar da zai kai ni FCE. Muka yi ciniki kana na ambaci sunan Allah na shiga. Nayi adu'ar shiga mota bayan na zauna, me napep ɗin na ƙoƙarin ja Yaya ya dakatar da shi. Naga ya tsare ni da ido yana kallona kamar ba zai ɗauke idonsa akaina ba. Yanayin kallon nasa yasa ni sadda kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuna ina murmushi, ji na ke kamar kar na tafi na barshi ko kuma kawai mu tafi tare, domin ina jinsa ne tamkar wani ɗan'uwana na jini, kamar mun ɗau tsayin wasu shekaru da sanin juna.

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now