Gwaggo kuwa na fita naji raina fes, murmushi kuwa idan ka kalla fuskana kai ka ce gonar auduga ce saboda yadda haƙorana suka gagara rufewa. Har sai da Gwaggo ta dawo ɗakin ta iske ni kwance kan gado still dai murmushin na ke, ina kuma ta faman juyi akan gado, sai da ta ƙare min kallon tsaf kafin ta samu gefen gadon ta zauna kana ta ce.
“Allah mai girma da ɗaukaka, yau naga Mace. Anya Sabina lafiyarki kuwa, na fita kina dariya haka zalika na shigo kina dariya, to ki dai yi a hankali don wallah dariya illa ce, kuma kin san bana son dariya”.Matsowa nayi kusa da ita, na kuma sakin murmushi. Sai naga ta miƙe tsaye zata nufi hanyar fita nayi caraf na riƙe hannunta, ina ƙunshe dariyar da ta ciyo ni, don nasan sarai abinda ke ranta na ce,“wai Gwaggo me kika gani, ina zaki je da na ga kin miƙe?”. ta ce,“yo Sabina na sani ko aljanun ki ne suka dawo, wannan dariyar haka sai kace an maki bushara da shiga aljannah”.
“yo Gwaggo kika sani ko busharar aka min, kinga ai sai mu tafi tare”.
Sai kuma na kwaɓe fuska na ce,“amma fa gaskiya Gwaggo ki bar cewa ina da aljanu, waye ke son su, amma ke duk magana ɗaya sai ki ce aljanu, mutum ba zai yi dariya ba sai ya zama jinnu”.
Na faɗa ina yin ƙasa da kaina tamkar zanyi kuka. Ganin haka yasa Gwaggo kamo hannuna ta ce,“haba ƴar lalen Gwaggo, kinga ke ce naga sai murmushi kike ke ɗaya kuma kin san Allah da yayi ni ina da tsarguwa shisa kika ga nace haka, ko kuwa akan maganar ɗazu shi ne duk kike faman wannan murmushin, ko dai a makaranta kin samu ɗan..”.
Bata ƙarasa maganar ba muka haɗa iɗo, sarai na gane inda ta nufa sai na waske na ce. “Gwaggota kenan mai abin mamaki, ki bama mutum daɗi ki ba shi haushi, na san fa abinda kike nufi, to ni ba shi yake sakani nishaɗi ba, kawai dai ina son zuwa Kano saboda naga Farhana, kuma naga dangin Mama shi ke sani nishaɗi wallah. Kuma duk lokacin da na tuna yadda Kike tattalina kamar ƙwai sai hakan ya kuma tsundumani cikin nishaɗi da jin daɗi, ke dai Gwaggo Allah kaɗai zai biyaki ya kuma ƙara maki nisan kwana mai amfani ya ɗora ki kan maƙiyanki. Ina son ki Gwaggota”.
Na ƙarasa faɗa ina bata sumba a goshi. Gwaggo ita ma ta shafa bayana tana saka min albarka tana faɗin, “ai kema kin san indai akan kine sai inda ƙarfina ya ƙare, Allah dai ya haɗaki da miji nagari. Oh Allah ka nuna min wannan rana, gaskiya ranar akwai shagali, ke ranar sai na kwaso shoki, don ma wai babu Sahibina a kusa da na ke faɗi maki abin sai yafi armashi”.
Dariya nayi na janyo kwanon abincin da ta kawo min ɗazun na fara ci kafin na ce,“ɗakko wata hirar don yanzu idan kika fara labarin Sahibin kin nan sai mu kwana mu yini baki gama ba, sai kace Sahibin kin nan yafi kowa”.
Ta ɗan dungure min kai, “munasira!, yo har kya faɗi min wani zancen Sahibina, baki ji akace kowa da bazarsa yake taka rawa, to ni tawa rawar da ta Sahibina ce, yo Allah na tuba ke har kya yi min zancen zan ɗakko maganar Sahibi, kema fa idan kika samu wuri tsaf nasan sai kin zarce ni, yarinya ba ki san loɓe ba(love)”.
Wata dariya ce ta suɓuce min wadda yayi sanadiyar zubar da abincin da na ke ci waje, Gwaggo ta min duban sheƙeƙe kafin ta ce,“kinga ba nayi magana kice ke baki san zance ba, yo meye abin dariya anan?”.
Ta tambaya babu wasa a fuskar ta, da alamu ta ƙulu, don haka nayi gaggawar tsayar da dariyar da nake yi kafin nace,“yo Gwaggo ke ce da fama, sai kice sai kinyi turanci kuma baki iya ba, ai sai ki haƙura haka, idan kuma ba haka na ce maki zan fara koya maki haruffan hausa shima kinƙi da duk kin san yadda ake faɗan words a hankali”.“ke kika san wani was(words), hakan ma tunda zan faɗa a gane ai shikenan tunda ba wurin wani naje na faɗa ba, bare naji kunya ato”.
“yo ai kuwa wataran zaki faɗa a wurin wani wallah idan ba ki daina ba”.
Gwaggo tace,“yau naga iya shege, ke Sabina fice min da gani”. Daga haka na miƙe ina dariya har na fice a ɗakin, dama yau na gama shiri na ba zan kwana wuri guda da Gwaggo ba duk tabi ta dameni da hayaƙi. Kai na tsaye na ke tafiya dariya na cin cikina, har na isa kwanar da zata sadaka da kitchen kaina a ƙasa naji nayi tuntuɓe da abu da sauri na ɗago kaina ina duban meye ne, karaf muka haɗa ido da Yaya Haidar, da sauri na zaro ido shima ni yake kallo da irin kallon wanne abu zan maki na huce.
Ni kam ganin kallon da yake watso min tuni na sauya hanya, nayi gefe da niyyar wucewa ya ce,“dutsen da kika taka hala bai ji maki ciwo ba?”.
Na ɗan ɓata fuska nace, “eh bai jimin ba”.
Ina faɗar haka na kuma niyyar wucewa. aiko a zafafe ya damƙo hannuna, tuni ido na ya raina fata, duk lokacin da muka haɗu sai naga kamar zai kuma tsotsen baki ne, fuskata ta cika da tsoro, baki na fal in-ina nace,"ka..kaj..kaji tsoron Allah kaga dai ba abinda nayi maka”.
Ina gama faɗar haka hawayen da suka cika ido na suka samu nasarar sauka kan ƙafar Yaya Haidar ya kuma ƙulawa fuskarsa tamkar ta bijimin sa ya ce,“an faɗa maki kowa ɗan iska ne kamar ke, da za’ayi tayin abu guda, ko an faɗi maki kowa maye ne kamar ke sha uku kawai, goge min ƙafa na ko na zane maki ƙaramin mazaunanki nan”.
Takaici ne ya ishen, a zuciyana na ce, _wallah kamar na zabga maka mari na ke ji._
Zaro idon da Yaya Haidar yayi yasa ni tsorata ba ƙarama ba, don wata iriyar damƙa ya kuma yima hannuna ya matsa min ya kuma galla min mintsini, take na buga tsalle idona ya cigaba da zubar da hawaye da ƙarfi ya buga min tsawa ya ce,“ni sa’an ki ne, Sabina ina wasa da ke ne, ni zaki kalli tsabar idona ki ce za ki mara?”.Ya ƙarasa maganar yana nuna kansa. “wallah zancen zuci ne ya fito fili ban san na faɗa ba, don Allah kayi haƙuri please Yaya Haidar Allah ban san ya fito ba”.
Ɗan cif-cif gemunsa ya kama yaja kana ya kawar da kanshi gefe guda, ban ankara ba yaja hannuna fuuuuu sai ɓangaren shi. ina ta ba shi haƙuri amma sam bai kulani ba, saboda maganar tayi masa ciwo, yana shiga yasa key a ƙofar ya saki hannuna, nan na shiga ba shi haƙuri akan ya barni na tafi, sai kawai na tsinkayo muryar shi yana faɗin,“abinda yau yafi tsotsar maki baki shi zan maki, za ki gane shayi ruwa ne zalla, za ki san kin ce ni za ki mara tunda ke ba ki da kunya sam”.
Nan ta ke ya shiga cire rigar shi ya zama daga shi sai gajeran wando, na saka hannuwa na rufe idona, gabana sai dukan dubu-dubu yake yadda kasan ana surfe akan ƙirjina, zuciyata kamar zata faɗo ƙasa tayi dancing haka nake jin yanayin yadda ta ke duka. Ta cikin hannuna na ke ganin shi yana takowa, sai da ya iso har inda nake naji ya cafki hannuna, sai ji na kawai nayi ya wulla ni kan gado, yana ƙoƙarin hawa gadon na ce,“na rantse da Allah idan ka hawo gadon nan kamar a bakin Baba, tunda na kalla sam baka tsoron Gwaggo ka mayar da ita sakarya Kuma wallah Allah indai...”.
Ban kai aya ba na jiyo muryar Gwaggo tana ƙwalo min kira. Da sauri ya mayar da rigar shi da wandon shi ya samu wuri ya zauna ni kuma ya ce min,“tashi ki shiga toilet ki tabbatar kin wanke fuskarki ta wanku, zan ce ma Gwaggo kina wanke min toilet kuma wallah idan naji kin faɗa mata magana ɗaya akan abinda na maki”.
Ya nuna ni da yatsa alamun kin san sauran. Cikin hanzari kuwa na diro daga gadon na faɗa toilet ina shiga Gwaggo ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin,“a’a Zainab ta ce min Sabina tana nan, ko kuwa tayi wani ɓangaren?”.
“Eh tana nan, tana wanke min toilet ne”. ya bata amsa a taƙaice, kansa na ƙasa kamar me yankan farce.
“Tolet kuma?, yau kuma ƴar wankin tolet ka mayar da ita bayan wulaƙancin duk da kake mata a baya bai ishe ka ba sai ka haɗa da folishwan?”.
Ina toilet amma yadda ta faɗi kalmar Punishment ba ƙaramin dariya ya bani ba. Yaya Haidar ya ce,“Gwaggo wai yaran nan idan ba’a ba su aiki dame za su horu idan sun je gidan miji, ki riƙa kawar da kai akan Sabina mana bafa ita ɗaya ne ƴa ba”.
“au tou, haba sai ka ce min kai kayi ƴaƴan ai har da ka san horo, tunda har ka iya tsayawa tsegege ina faɗa kana faɗa, Aliyu ka shiga hankalinka da ni, wai ban ce ma ka daina zuwa ɓangare na ba har ka ganta ka saka min ita aiki, Aliyu ka fita idona na rufe billahillazi tun kafin nayi maka abinda har ka koma ga ubangiji bazaka manta ba wallah”.
Tana ida zancenta ta ƙwala min kira, ni kuwa dama ƙiris na ke jira na fito muna haɗa ido ta ce,“jakar uban can, kar ka ce min kuka ka bata, don wallah mai barinka ka ƙara kwana gidan nan sai ikon Allah”.
Da sauri na girgiza kai ina tuna sharaɗin da ya gindaya min na ce,"a’a fa Gwaggo, ina wanki ne ƙwaro ya faɗa min a ido, shine kika kalla yayi ja haka, amma na fitar sai dai bai daina min zafi ba, muje”.
Naja hannun ta muka wuce don na san zata iya fahimtar abinda ya faru.
________________________
#React,Vote,Comment
#Al-hussainBook1
#Gamjiwriter's
#Teamfitattubiyar
#2024
#February
#Share
#07018098175
#Halimahz
#Purchase₦300
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...