6

113 15 0
                                    

*(6)*
Masu jin haushin alaƙarmu da Farhana sai zugata suke yi, mu kuwa lokacin shaiɗan ƙara buga mana ganga ya ke a kunnuwa, faɗa kamar ƙananun yara, abunda zamu iya rantsewa bamu taɓa yi ba tun wayonmu. Muna haka Malam ya aiko ayi kiran mu, amma kamar bamu ji me ake cewa ba ƙara cakumar juna muke yi.

Ga dai shi haushin hakan na ke ji a ƙasan raina, don ba wai a son raina ne faɗan namu ba, amma kuma na rasa dalilin da ya sa ko na nemi na huce sai zuciyata ta kuma ingizoni da zugar kar na raga mata, wataƙila shi Yayan da take zagi tana aibatawa dalilin wani alkhairi Allah ya turo shi cikin rayuwata, balle a irin yanda na ke ji ya tsaya a raina tamkar muna da wani connection da shi.

Kuma a hakan bakin Farhana bai mutu ba, dagewa take tana ƙara zaginsa, ni kuwa ina ƙara ƙuluwa har na rarumo wata kujera zan buga mata Allah ya kawo Malam Isma'il.
Office ya kaimu, raina idan yayi dubu to kuwa tabbas ya ɓaci, sai cika nake ina faman batsewa.

Malam Hamza firinsifal ya shigo office ɗin ya gyara zaman shi akan kujera da hular shi irin tashi ka fiya nacin nan, ya dube ni tsaf, sannan ya juya ya duba Farhana, a iyaka saninsa da mu yasan duk ɗinmu bamu da hayaniya, wani lokacin idan har ana faɗa da ɗaya, to sai fa inda ƙarfin ɗaya ya ƙare don shigarwa junanmu faɗa muke yi, sai ga shi a wannan karon abinda ya ba shi mamaki mu da kanmu muke faɗan, har ana rabamu muna ƙin rabuwa.

Ko ada saboda irin kyawun alaƙar da ke tsakaninmu da yawan Malamai da ɗalibai zaton su gida guda muke. Malam Hamza yayi gyaran murya ya dubi inda nake tsugunne yace,  “Sabina lafiya yau kam, ku da ba’a jin kanku sai kuma ga shi yau anji?”.

Ban ce da shi komi ba, saboda ina da saurin hawaye duk da na kan mayar da martani, amma a wannan karon muddin nace zan buɗe baki nayi magana to fa zan iya yin kuka, saboda irin kalaman cin mutumcin da aka dinƙa faɗa min, ana cewa Farhana wai dama tsiyar abota da ɗan talaka kenan, shi yasa tuntuni su ke ankarar da ita munafukarta ce ni, ba dan Allah na ke zaune da ita ba sai dan kuɗin gidansu, ita kuma lokacin ban san me ke shiga zuciyarta ba har ta ɗauki huɗubarsu ta yaɓo min maganar da ta tsaya min a rai, wadda ba dan da kunne na naji daga bakinta ba, wallah ba zan taɓa yarda ba.

Malam Hamza ya dube ni ya kuma faɗin,“Ko ba za ku iya magana ba ne sai nasa muku bulala, sanin kanku ne ba ku fi ƙarfin hukuncin makaranta ba, banda rashin hankali da rashin tarbiya manya da ku sai ku kama yi mana faɗa a makaranta, makarantar ma cikin aji".

Farhana zata yi magana kenan nayi caraf na tari numfashinta, saboda nasan idan na barta tsab zata iya faɗin abin da ya haɗamu.
“Malam yau dama ban koma gida ba, na zauna ba da hadda wurin Malam Ibrahim, tana ta tambayata, ni kuma yau bana jin magana, ita kuma ta takura min da magana shine muka fara faɗa, kuma kaja mata kunne idan ta kuma ganina a irin wannan yanayin ta daina kula ni”.

Malam Hamza yace,“to shikenan ke Farhana kinji abinda tace saboda haka ki kiyaye karku ƙara bari shaiɗan ya shiga tsakaninku, ku tashi ku bani wuri. Haba da girmanku da wayonku, ina muku kallon masu hankali kaf ɗaliban makarantar nan”.

Farhana zata yi magana Malam Hamza ya dakatar da ita, na faki idon shi nayi mata gwalo wanda nasan ya sosa ranta, ta girgiza kai tare da yin ƙwafa muka nufi hanyar fita. Bayan fitar mu shi kuwa Malam Hamza murmushi yayi gami da girgiza kai. Kafin mu ƙarasa aji kuwa, muna tafe ina banka mata harara itama tana aikomin da martani a haka har kowa ya isa ajinsu. Ƙarfe shida saura kwata aka tashi, kamar kullum tana inda ta saba jirana, ni kuma na gama cin alwashin ko ita ne mai mota ɗaya a duniya wadda dole sai na hau zanje gida sai dai na shekara ban isa gida ba ko ma in mutu a hanya.

Ina kallonta ta gefen ido tana bina da kallo, ni kuwa har wani sauri na ƙara tamkar zan kifa, ƙafafuwana har sarƙewa suke yi, amma hakan bai sa na daina sauri ba. Ina tarar mai napep nayi sauri na shige don ko bayanin inda zai kai ni ban samu damar yi ba sai da na shiga muka fara tafiya.
A ƙofar gida ya sauke ni inda ina sauka su Adda Karima suna fitowa ita da Mardiyya daga gidan mu, ko kallo Addan bata ishe ni ba bare nasan Allah yayi ruwan halittarta a wurin, da hanzari na ƙarasa da fara’a fal shimfiɗe kan kuncina na shiga gaida.

Itama anata ɓangaren Murmushin baƙin cikin tayi asanda ta kafe ni da ido tana neman inda zata samu makusa, saboda macece wadda Allah ya dasa mata zuciyar kushe, akwai fara’a amma fa irin mai ɗauke da taɓe bakin nan.
Ta dube ni sannan ta dubi Gwaggo tace,“Wai ni Yaya me kike bama yarinyar nan ne gaba ɗaya sai ƙiba take kamar ana hura ta, billahillazi idan baka santa ba sai kace ba ita bace, ke duba min yadda take kumatu ta ke cika tana ɓatsewa kamar wadda take shan sha ka fashe”.

Yadda ta ke yaɓa maganganun ni kuma yana saka ni nishaɗi, ita kuma idan duniya akwai abinda ta tsana tana faɗa ina dariya, duk da kasancewar ta itama Kaka ce a gare ni, Gwaggo tayi murmushi ta dube ni tace,“Karima wannan kuma ai gaki gata, yo me zan bata ni kuwa, abin ma da ba wani ci take yi ba, gaba ɗaya makaranta ta saka ta gaba, ni da nake ta so ma ta samu hutawa”.

Adda Karima ta gwame baki tace,“kuma fa haka, ita wai al huda-huda, gara dai ayi aure duk sa’anni sun yi sun dire ku kuma kunce karatu to ayi dai mugani lafiya ƙalau, mutuncin ɗiya mace dai gidan aurenta”.

Saboda tsabar gulma nacinta bata samu damar amsa gaisuwar da nayi mata ba sai da ta gama habaicinta. ni kuwa ina dariya nace,"Adda Karima kenan, ke dai ba’a raba ki da abin faɗa, to abinda kema kina da iko akaina, miji ai sai kiyi min wannan abu ɗan sauƙi..”.

Kafin na ƙarasa tuni Adda Karima tace,"Abu ɗan sauƙi fidda wando ta ka, Sabina ai shikenan tunda haka kika ce”.

Ina jinta na shige ciki, duk bakin Gwaggo idan Adda Karima tana wuri to fa nata mutuwa yake yi muɗus. Napep ɗin da na sauka shi ya ɗauke su, ita kuma Gwaggo ta dawo ciki daga rakiyar su. ina ɗaki ina canja kaya Gwaggo tayi sallama ta shigo ɗakin, gefen gado ta zauna tana faɗin,“Ina raba ki da mayarwa Karima martani idan tana maki magana, kin san dai kaf dangi babu wanda ya kaita shiga abinda babu ruwanta, saboda haka ki kiyaye ta wallah”.

Ina gyaran zaman rigata, na miƙa hannu na ɗakko hula na sanya akaina sannan na dubi Gwaggo nayi mata kallon tsaf nace,“To kar ki damu Gwaggo zan kiyaye, wai da naga itama matsayin Kaka take a wurina shisa ma na ke yi da ita, baki ga ita wancan ko kallo bata ishe ni ba”.

Gwaggo tace,“Au yo to ni ai na zaci ba ki ganta ba ne, kinga fa bana son iya shege, sai kace baku san juna ba, kai ku dai ko miji kuka haɗa iyaka abin da zaku yi kenan, Allah ya shirye ku to”.

Miƙewa tayi tana faɗin bari nayi alwala, har ta kai bakin ƙofa ta ɗaga labule ta dawo tana faɗin,"Au ke la ɗazu kuwa Farhana ta zo zaku tafi, nace mata ba ki dawo ba, ƙila ko kin tsaya bada hadda ne”.

Saboda kar taja zancen da sauri nace,“Eh, hadda na bayar saboda jiya ban bayar ba, kuma bana son tayi min yawa shisa”.

“Au to madalla, ai na zaci ko wurin ɗan iskan yaron can kika koma, dan ta kawon ƙorafin hakan”.

Sai da zuciyata ta buga, bugun da ban taɓa jin tayi ba, zuciyata bata son ana zagin bawan Allah'n nan ko kaɗan. Rumtse ido nayi na dubi Gwaggo da wani irin kallo, da ƙyar leɓena na ƙasa ya samu nasarar motsawa kana na sama ya motsa suka haɗu suka samu nasarar furtar kalmar,"A'a ina makaranta ni kam".

Bata kuma yunƙurin cewa komai ba ta saki labulen ta fita. ni kuwa na dafe kaina saboda yanda naji yana sara min na furta,“Ya Salam!”.

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now