9

115 13 1
                                    

*(9)*
"Sabina tun a washegarin ranar da idanuwanki su ka sauka akan ɗan sigarin kan bola na kalli wani abu a cikin ƙwayar idonki akansa, sai ga shi ayau abunda na gani a saman fuskanki ya ƙara tabbatar min da shi...Sabina a haƙiƙanin gaskiya ba iyaka tausayinsa kike yi ba, tausayinsa kike me haɗe zazzafar soyayya, irin son da kika kasa ganewa balle har ki gasgata shi".

Nayi mata wani kallo na rashin fahimtar maganar tata sannan nace,"Ina kika dosa kenan? i din't get you well".

Tayi wani guntun murmushi da ya tsaya iyaka leɓenta sannan tace,"Wanda kike kira da Yayanki mana...Sabina ki yarda ko kar ki yarda kina sonsa, Kuma irin son da kin yi zurfi a ciki, tunda har za ki iya shiga wannan yanayin na tashin hankali becouse you are going far away from him. Tun a ɗazu fa ina lure da yanda Mood naki ya sauya lokaci guda bayan kin gama murnarki, kuma da na gama karantar fuskanki, i saw nothing beyond love full of compassion".

Na ja wani uban dogon tsaki, wanda yasa har mai napep ɗin da ke janmu sai da ya juyo ya kalle ni. Cikin masifa na ke ce mata,"Kina raina min ajawali da yawa Farhana. Wai me kika ɗauke ni ne hala ma tukunna, kawai kin bi kin haɗa wani hasashenki mara kan gado kin dage akan cewan Sonsa na ke. To naji, amma ki sani ba sonsa na ke ba, kawai dai ina matuƙar tausaya masa ne, kuma zan iya yin komai wajen ganin na canja rayuwarsa zuwa duniyar farim ciki, ba irin wadda yake a ciki ba yanzu".

Wata ƴar banzar dariya ta saki. "Au Allah ƙawata, Jihadi za ki kenan, to ta ya?".

Na ƙara harzuƙa, na wulla mata harara na ɗauke kaina, ina kallon waje nace da ita,"I just told you kar ki kuma cewa ina sonsa, otherwise kuma zamu yi faɗa da ke".

"ke wallah ba zan bar cewa kina sonsa ba, ai labarin zuciya a tambayi fuska, ba wai na ƙirƙiro na faɗa ba ne".

Na kaɗa kaina ban kuma ce mata komi ba, the way I heard her hypocritically laughed, sai na tsaida mai nepep ɗin na sauka, dan ba zan iya tafiya da ita tana ci gaba da faɗan wannan banzan zancen nata ba. Allah ya so na fito da sauran kuɗi a hannuna na babshi, ina jinta tana min magana nayi mata banza, saboda ma karnta takura ni nayi saurin tsallaka titi, har cikin ranta nasan ba taso hakan ba, to amma kuma ya ta iya, dama ni na nema mu tafi tare kuma nace na fasa.

Wani mai napep ɗin na kuma tara na faɗa masa unguwarmu, yana sauke ni ƙofar gida mu kai karo da Yaya Abba, shi ya biya kuɗin motar saboda ni babu a hannuna. Fuskata a turɓune na shigo ina sallama a ciki, sai dai duk ɓacin ran da na ke ɗauke da shi, diramar da na tarar Gwaggo da Baba nayi sai ya kawar da shi, take na fara ƙyalƙyala dariya. Sai a lokacin ne ma suka san da shigowata, Baba ya dube ni zai yi magana Gwaggo ta riga shi tana ce min,"mlMutan kan naki sun sauya miki ra'ayi kenan?".

Ina zama kan kujera nace,"Ɓata min rai tayi shi yasa na fasa binta, dama ba wata uwar zata tsinana min ba, bare ta sani gaba tana min dariya kamar taga mahaukaciya sabon kamu".

Tace,"Oho miki dai, mai jure ma halinki sai ita ɗin. Ke ni fa da ni ce ita da tuni mun jima da gama ɓaɓewa da ke, yo ina dole a nan, zamaninmu idan naga ƙawa na min iya shege saboda taga ina sonta sai na nuna mata ba'a haifi wanda ya haife ta bama".

"To su Hajiya Gwaggo Allah yasa ba ke ɗin ba ce, kuma Allah yasa bata nan bare ki zugata. Nima fa Gwaggo ko ni ɗin, da ke ce ƙawata yasin ba zan iya zama da ke ba tuni zamu raba hanya".

Ai tun ban rufe bakina ba tace,"Yo ga mai mugun halin kaf duniya ke kuwa ai dole ki ce haka. Yanzu ai idan baki zauna da ni ba kya zauna da matan ubanki da basa ƙaunarki".

Yaya Abba da ke shigowa yace da ita,"Don zamu koma can ai ba yana nufin zamu zauna gida ɗaya da su bane".

Gwaggo ta taɓe baki tace,"To ɗan masu iya magana ai ba ni na faɗa ba, ubanka shi ya faɗa ga shi nan a zaune sai ka tambaye shi kafin ka ƙaryata ni".

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now