26

78 12 3
                                    

*(27)*
Iya ƙularwa mun ƙular da Umma amma babu yanda ta iya, kuma na san da marasa kunyan yaranta suna wajen sai sun rama mata, don ma dai suna shakkar Yaya Abba.

Muna shiga parlo muka zube kan kujera, abun mamaki ba ya ƙarewa tare da Kakarmu, na kalla Yaya Abba ya kalle ni muka fashe da dariya. Gwaggo ce zaune kan carpet tasa Yayana a gaba tana barbaɗa magani a abinci, gefenta kuma wasu ɗaurin magunguna ne na daban suma iri-iri. faɗi take tana cewa,"yanzu kaga idan Allah ya taimaka sai kaga cikin kwanaki kaɗan kayi kuɓulɓul da kai, saboda maganin matar nan akwai kyau sosai, so nake na gama da kai sai na koma kan Abba, kai fa Yaya yanda ka san sandar suluka haka kake don dai baka kallon madubi ne".

Yaya Abba ya ce,"to ni kuma Maganin me za'a samo min?".

"shegen cinka da yake damuna shi zan shiga fafutukar neman maganinsa, domin wannan babbar lalura ce kake fama da ita, yawan cinka har tsoro yake bani Abba". ta faɗa tana kuma kunce wani ɗaurin ta ɗibi garin maganin ta barbaɗa acikin abincin.

Sai da ta gama tas tukunna tasa cokali ta juya, sannan ta tura ma Yaya plate ɗin abincin gabansa tana cewa,"ga shi nan maza kaci, kaga sau uku a rana aka ce, kuma kai da ba ƙaunar abinci kake ba ga shi har yamma tayi ko ci ɗaya baka yi ba. gaba ɗaya ni na rasa wanna irin ciki ne da kai wallahi, na so ace ma an haɗa maka da ɗurar ƙwai yanda za ka dinƙa ci babu ƙaƙƙautawa, to matsalar ba bina za ka yi ba Yaya, tunda kai ba sanin ciwon kanka kayi ba".

Shirun da taji ya mata ne yasa ta tsaya tana masa wani duba ta ce,"wai ba da mutum na ke magana bane?".

Gaba ɗaya hankalinsa na kan waya, ba wai jinta ne bai yi ba, sarai yana jinta ya shareta, kofi ta raruma ta wurga masa ya sauka a goshinsa, ya ɗago cikin sauri yana sosa wurin yana kallonta.
"Gwaggo me nayi miki? Da kin fasan goshi fa".

Harara ta zabga mishi ta ce,"kai dama baka da mutunci, yanzu duk maganar nan da na ke ashe ba saurarena kake ba, ka barni sai zuba nake kamar tsohuwar kanya, su kuma waɗancan mahaukatan suna min dariya. to ni duk wanda yay min dariya kansa ya cuta saboda rage imani ta ke. yanzu da ka ɗago aika fahimci ina magana da kai ko, zaka ɗauka abincin kaci ko ƙaƙa?".

Ya ce,"kai Gwaggo, wai fisabilillahi ta ya za'ayi da girmana na kama cin abinci da wani maganin ƴan yaye, ni fa ba yaro bane. gaskiya ni bazan sha wannan magungunan ba da ban san daga ina aka samo su ba".

Tayi galala tana kallonsa cikin jin haushi ta ce,"to kana so kace min kasheka zanyi kenan, to ka sani ni ba azzaluma ba ce, dan ko kishiyoyina ban cutar da su ba bare kai da kake jikana. kuma dan ubanka Auwalu banda ma ina ƙaunarka kai har kaga na damu da kaci ne, amma saboda baka yo gadon arziƙi irin na Sahibina ba shine kake faɗa min son ranka. kasan irin wahalar da nasha wajen neman gidan mai maganin nan kuwa? Da ace kana da imani wallahi sai ka tausaya min, ka duba ƙafafuna tun yammacin jiya da na dawo suke min ciwo har yanzu, amma sam bai dame ni ba saboda nafi so na ganku kullum a cikin ƙoshin lafiya".

Ya tankwashe ƙafa ya matso kusa da ita, sai da ya rungumeta ya ce,"Hajiya Gwaggo tah ina so ki fahimci su kansu masu maganin hausan nan ba lallai sun san abinda suke badawa ba. da maganin bature ne zan sha, amma wannan da babu Nafdac ta ya zan aikawa cikina shi, garin neman gira a rasa ido".

Kaman ya tsikareta ta juyo ta kalle ni ta ce,"ke maye Nauduk ɗin da ya faɗa?".

Irin kallon da take aika min yasa na gimtse dariyata na ce,"kai Gwaggo ba Nauduk ba Nafdac, hukuma ce ta tace magunguna da kayan abinci, duk wani magani ko abinci ko nasha idan babu nafdac a jiki ba'a so ayi amfani da shi".

"hmm". ta ce tana taɓe baki, ta ture Yaya daga jikinta, ta yunƙura tana tattara magungunan tana ce wa,"naudok mata shegiyo dan uwar ubanta, da ma'aikatar, da masu aikinta da masu bin umarninta na haɗasu na kankantsa musu mari. shegen tsirfar banza da wofi, kai wannan bature anyi ɗan jaraba billahillazi. daga yau ɗin nan indai ni ɗin masoyiyar Sahibina ce, babu ɗan banzan da zan kuma cewa yasha magani a cikinku, ku rayu ko kar ku rayu ba damuwata ba ce, ana tausaya muku amma ba kwa gani. to ni daga yau babu ruwana na fita a sha'anin kowa. masu shegen ci idan sun mutu ta dalilin haka Allah ya jiƙan rai, suma marasa ci idan ciwon yunwa ya kwantar da su a asibiti iyakata na bi su da Allah ya kyauta amma babu mai sa ni zaman jinya, nima kunga tattalin arziƙina ya ƙaru, dama wannan ma jiya dubu uku haka nasa na karɓo maganin nan, to ajiye shi zanyi idan Hajara ta haihu na bata in ta tashi yaye, an huta da kuma ɓarnatar da kuɗi".

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now