11

128 9 2
                                    

*(11)*
Shirin sauri na ke tayi Yaya Abba na jirana zamu fita koyan mota. Ba ki ɗaya na hargitso da kayan sawata na rasa wanda zan saka, saboda na riga na saba tun muna tsohon gida bana iya saka kaya idan zan fita sai wanda Gwaggo ta zaɓa mani, gashi ita kuma yau ta shige toilet tayi zamanta kamar ta shiga labour room.
Kiran wayar Yaya Abba ne ya shigo a karo na babu adadi, kai na dafe na share ban ɗauka ba, saboda idan na ɗauka fa raina zai iya ɓaci matuƙa, shi mutum ne wanda ya tsani delay a rayuwa, shi yasa ma ba kasafe ya fiya haɗa fita da wani ba.

Har lokacin ina tsaye kamar nayi kuka ba alaman Gwaggo zata shigo ɗakin, kayan na yayiba na fita da su zuwa ɗakinta, a bakin gado na sameta zaune ta riƙe baya tana ta sauke nishi, kayan na zube a gabanta bakina a gaba ina daɗa turɓune fuska. ta ɗago tayi min kallo mai kama da harara sannan tasa  ƙafa ta shure kayan.

A ƙufule ta ce da ni,"ke fa ba ki iya ganin mutum cikin wani hali ki masa sannu ba ko ki tambayi me ke damunsa, a'a ke fatanki a biya miki buƙatarki, to sai ki jira sai na gama wartsakewa".

"Eyyah Gwaggota wallah na aza ko kinyi training ne, ban kawo wani abu ke damunki ba".

Wani wawan kallo ta wurgo min wanda yasa na haɗiye sauran maganata. "To idan kin aza sai ki sauke ba training na ke ba, zawo na ke fama da shi, shiga ta banɗaki na huɗu kenan a cikin rabin awa. Ban yarda da abincin jiya da muka ci ba, ina tunanin waɗannan ƴan iskan sun fara mana barbaɗe a abinci".

Da sauri na ƙarasa wurinta cike da tausayawa, duba da yanda idonta ya faɗa lokaci ɗaya. "Subhanallahi, Gwaggo Zawo kuma? To taya akayi hakan? me kika ci da za ki kwanta?".

Ta ƙara kufula tana ce wa,"Da wanne yare nayi miki maganar da kika kasa fahimta, ba ki ji nace ina zargin masu kama da tantabarun can ba. Mutum na fama da kansa dole sai kinsa yayi magana".

Taja guntun tsaki,"ke sam ba ki da saurin fahimta, dole idan za'ai miki bayani sai an faɗaɗa shi, kisa ai ta doguwar magana".

Na ce,"Gwaggo to ai ni ban zargesu ba ne, tunda abincin nan dai nima na ci shi, wataƙila dai ko cikinki ne ya ɓaci kawai".

Wannan Ƴar maganar da nayi sai ta jawo masifa da sababi, faɗi ta ke,"Au to ni za ki gayawa cikina ya ɓaci da ke ban san takan cikin nawa ba. Da can da na ke girkina naci lafiya na miƙe lafiya fa? Da kika ganni sarai nasan takan lafiyar cikina, wannan girkin dai dole anyi wani barbaɗin a ciki domin nasan halin mugwayen matan Babanki, so suke su ƙarasa ni kuma ba yanzu ba, kema Allah ne ya kiyayeki, saboda haka bazan iya ci gaba da wannan haɗakar girkin namu da su ba, anyi an gama daga jiya, kowacce cikin su tayi nata taci da iyalanta, mu kuma yazo ya samo mana wadda zata dinga yi mana namu, wacce zuciyarta ta cika fal da tsoron Allah".

Ni dai ina dafe da bayanta nayi murmushi, saboda ban isa na hanata wannan mitar da masifar ba sai kuma ta samu lafiya, cike da tausaya mata na ce,"Sannu Gwaggo, bari a kira Baba sai ya turo likita".

"Ehh kirawo shi ɗin, dan cikina a ɗaure yake ni ɗaya nasan irin azabar da na ke ji. Ba don ina gudun haɗa rigima ba ai da sai na zayyane masa wannan muguntar da aka haɗa min, amma dai Allah...".

Sai kuma tayi shiru tare da yin ƙwafa. Cikin faɗata ci gaba,"Ni dai kaf cikin Yarana babu mai halin kirki irin Auwalu. haƙuri, mutunci, karamci komai ya haɗa, amma kuma duk cikin Ƴaƴana shi ɗaya ne bai yi sa'ar Mata ba, Mahaifiyarku kaɗaice ta ƙwarai, sauran Auran nasa kam sai dai a kira shi da auran ƙaddara, jiya na gama yarda da duk wani mugunta nasu da ku ke faɗa na ke ƙaryataku, saboda kwana nayi ban runtsa ba ina kokawa da cikina. dama duk wani iya shege da suke ina ɗaga musu ƙafa ne saboda darajar Auwalu da suke ci amma na kusa yiwa tufkar hanci, kaf ɗin su za su gane shayi ruwa ne. Hmmm banda ma dai ina da tausayi ai da sai naja musu Allah ya isa, to idan naja musu bin su zatayi su zo su ƙara lalacewa, ni kuma gyaruwa na ke so suyi kar a tafi lahira da tarin zunubai, tunda dai Allah ya ƙaddara auren su da Ɗana".

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now