12

117 11 5
                                    

*(12)*
Ashe gwaruwar kawunan da muka yi da Yaya Haidar ashe ba ƙarama ba ce, dama kansa kaftarere, sosai kaina ya shiga juyawa nayi sauri na dafe bango ina ganin wasu abubuwa na wucewa a duhun idona, na ɗaga ƙafana zan ɗora saman steps sai idona ya rufe gaba ɗaya, nayi baya zan faɗi sai gani na faɗo a hannun Yaya Haidar, caraf ya cafeni kamar wata ƴar Baby, to ni kam tunda na buɗe ido na kalle shi dishi-dishi na mayar da murfin idona ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai dai kamar na jiyo salatin Gwaggo.

Shuɗewar wasu awanni na farka, na ganni shimfiɗe a ƙirjinsa Ya kewaye ni da hannayensa, kuma a cikin ɗakinsa, na rufe idona yafi sau ƙirgen hannu ina kuma buɗewa don tabbatar da abinda na ke gani, ni ce dai a tsakankanin cinyarsa kuma kwance bisa ƙirjinsa, bacci yake ko mene oho, idonsa dai a rufe yake, da sauri kuwa na miƙe daga jikin nasa a zabure na dira ƙasa daga kan gadonsa, domin zuwa wannan lokacin dukkan wani tashin hankali ya gama bayyana a zuciyata da gangar jikina.

Duk tsoro ya gama cika ni, idona ya taru da ƙwalla yana shirin zubar da hawaye, Dama ni Allah ya horen ruwan hawaye kamar ruwan famfo, sai na koma kamar wata taɓaɓɓa, kaina fa ko ɗankwali babu kuma ba a yanda na ke ɗazu ba da rigar t-shirt a jikina, wannan riga ce doguwa aka zumbula min ta material, bama ta ɓangarenmu ba ce, don ko Gwaggo rigar nan tayi mata yawa, sai da na ƙare mata kallo kana na tuna wani matrial na sallar bara da Baba yayi mana, kenan ta Umma ce ma, ƙofa na nufa gadan-gadan sai na jita a rufe da key.

Zubewa nayi a wurin na ɗora hannu aka na kurma ihu ina faɗin, "Innalilllahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga ukuna Gwaggo tah, wayyo Allah na shikenan Yaya Haidar ya ɓata ni, Gwaggo ki zo ki taimaka min, ya rufe ƙofar, ki zo kar ya ƙarasa abinda bai cimma ba".

Ni dai iya sanina a irin nasiha da faɗan da Gwaggo ke min, cewa take ko hannuna wani da ba Yaya Abba ba ya kama to shikenan yay min fyaɗe kuma na ɗauki ciki. To kuma yanzu ba kama hannu ba kawai, shimfiɗe fa na ke a jikin Yaya Hydar, me ya aikata min Allah masani, dama shi ga kalarsa ruwan ta ƴan iska.

Ihu na ke sosai ina shure-shuren ƙafa kamar ƙan-ƙanuwar yarinyar da aka hana shan nono. Jin yadda na ke kurma ihu ina buga salati cikin fizgar numfashi, shi ya farkar da Yaya Haidar, Ganinsa nayi a gabana a tsugune don ko tasowarsa ban sani ba, ƙoƙarin saita min yanayin da na ke ciki yake, kallon da yake min sai naga kamar da tsoro a cikinsa, abinda yake kawowa a ransa daban, abinda nima na ke kawowa a nawa ran daban.
Sai matsawa baya na ke ina ƙanƙame jikina, shi kuma yana daɗa matsowa kamar zai shige jikina, amma fa gefe guda idan na gasgata abunda idanuwana ke gani cikin idonsa tausayi ne tsantsa, sai da na kai maƙura a mannuwa da jikin ƙofa kana na haƙura, jikina nata karkarwa, wallahi tsoronsa na ke sosai, inda za'a auna jinina a wannan yanayin tabbas jinina ya hau, shima ɗin sai da ya kawo gab da ni numfashinmu na gauraya da na juna tukunna naji ya kamo hannuna guda ya damƙe, ya ɗaga kofin ruwan da ke ɗayan hannunsa ya watsa min, ba shiri na rumtse idona tare da kurma wani sabon ihu ina roƙonsa.

"wayyo Allah nah, Allahumma ajirni fi musibati waklifni kairan minha, don girman Allah Yaya Haidar kar ka yi min komai, kaga dai ni ƙanwarka ce".

Sakin hannuna da yayi shi ya dakatar da ni daga ihun da na ke kwaɗawa, ban dai buɗe idon ba sai shashsheƙar kuka da na ke ina daɗa faɗin,"Yaya Haidar babu kyau kaji tsoron Allah, duk wanda ya ɓata ƴar wani shima za'ai wa tasa bare ni da na ke ƙanwarka, idan ka lalata min rayuwa kai kanka ba zaka sami kwanciyar hankali ba, ka saka rigarka bana son ganinka a haka, babu kyau kallon tsiraicin wani, ko riƙe hannuna da kayi haramunne, Yaya Haidar kasa rigarka ba kyan gani ƙirjinsa...".

Ina kuka sosai ina faɗin hakan, Saukar marin da naji a kuncina ya katse sauran surutan da na ke yi, a zabure kuma na miƙe tsaye ina rarraba ido ina neman hanayar fita, don duk Yaya Haidar ya gama razana ni.

Kuma cikin abunda bai wuce sakan huɗu ba naji muryarsa na fita da ɓacin rai yana faɗin,"wallahi idan ba ki rufe min wannan shegen bakin naki ba sai na zare belt na zane miki jiki a wurin nan, mahaukaciya kawai, an gaya maki kowa ɗan iska ne irinki".

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now