*(13)*
Baba ya ɗaga waya ya kira su Umma, babu ɓata lokaci duk sai ga su. Anty ce ta fara shigowa sai Umma da ta biyo bayanta. Su ka nemi wuri suka zauna, Umma ta wani karkace sai faman hure-huren hanci take, ta ɗauke kai tana kallon gefe daban kamar bata ga mutane a wurin ba, sai da taji Anty ta miƙa gaisuwa ga Gwaggo kana itama ta juyo tana kumbure-kumbure ta gaidata."lafiya". ta amsa musu babu yabo babu fallasa.
Gwaggo ta miƙe ta gyara ɗaurin zaninta tukunna ta koma ta zauna, kamin ta kalla Umma ta Kalla Anty, sannan ta maida kallonta ga Baba cikin murya mai bada umarni tace.
"ka sami damar yi musu bayani, yau ɗin nan nayi magana da yawa bakina ya gaji, tsakanina da abinda Haidar ya aikata ai sai kotun ubangiji".
Tana gama faɗa ta jefa goronta a baki tana ci. Baba ya zayyane musu kaf abinda Gwaggo tace akan zarginsu da take na faruwar ciwona. Yana gama bayani Anty ta rushe da kuka kamar wadda aka yowa aiken mutuwa, faɗi take. "wallahi ina ga kaf duniyar nan bayan iyayen Sabina to duk wani mai sonta ya biyo bayana domin ni zanzo a bayan Gwaggo, amma sam-sam kin gagara fahimtata Gwaggo, gani kike kamar ba ƙaunarta na ke da gaskiya ba, ina so na cutar da ita ne. Bayan ba haka bane, Ko abubuwan da suka faru a baya sharrin sheɗan ne, Gwaggo har yanzu kina min mummunar fahimta akan yaran nan. Yanzu fisabilillahi ta ya za ai na yiwa ƙaramar yarinya turen aljanu kamar dai bani da ilimi".
Ta ƙarasa maganar tana kuma fashewa da kukan munafurci, kai ka ce gaske abinda take faɗa. Sai kuma taci gaba da ce wa.
"tunda na ga abinda ya samu yarinyar nan hankalina ya kai ƙololuwar tashi, har zuwa yanzu ban samu natsuwa ba saboda damuwar da na shiga, ko ba komai itama ai ƴata ce, abinci wannan gagarata yayi ina zaune suku-suku saboda hankalina na kan Sabina da kuma hanyar da za abi ai mata maganin wannan lalurar da ta sameta. Amma ƙarshe sai zargi ya shiga tsakani".Hmm ni kaina ban san lokacin da na sa ki baki galala ba, lallai Anty ta ƙwarai a iya kissa, tab wannan kafce nata sai ka rantse gaske ne. Umma da ke zaune a shirge ta ce,"to ai ni gaba ɗaya na rasa abun cewa, yanzu kayi magana ne abun yafi haka tsauri. Sai dai na ce Allah ya kyauta ita kuma ya bata lafiya, Allah kuma yayi gaggawar bayyana gaskiya, domin ni gaskiya an shiga da hakkina. Ko wani daban ba zan iya cutarwa ta hanyar masa turen aljanu ba bare Sabina da take ƴar mijina, to ni ina nasan ma hanyar wurin bokaye, ai duk rashin son da na ke mata bana ɗora mata wannan ciwon wahalar ba, amma Allah yana ji yana kuma gani".
Ai inaaa Gwaggo sai ta saki Baki, hanci da idanu ta zuba musu tana kallon sarautar Allah, duban mamaki takewa Umma, kamin ta dubi Baba ta ce,"kaga irinta ko, idan na faɗa maka baka yarda, yanzu tunda Allah ya haɗa mu gida ɗaya ka dinga gani kenan ai, ka kalla fa a gabanka nema ta ke tayi min rashin kunya, to dama ta ina zata kalle ni da gashi ni ba Asiya(mahaifiyar Umma) ba, amma dai ko ba komai ai ni na haife ka, ta girmamani idan tana neman albarka aure, ta inda na ke yabon Halima kenan, Har ta mutu kamar uwar da na tsuguna na haifeta haka ta ke girmamani, babu fitsara ko ɗaya a maganganunta, ga ƴaƴanta nan ma sun ɗebo halinta, dama hali ai tushe ne".
Umma ta zumɓuri baki ta ɗauke kai, Gwaggo ta dubi Baba ta ce,"wai baka ji irin maganganun da ta yaɓa min bane, kana jinta fa wai Allah yana ji kuma yana gani, to me take nufi da hakan? Kai kuma kaga solon namiji ba zaka iya tsawatar mata ba".
Allah sarki Babana bawan Allah, cikin muryar nan tasa ta rashin son magana ya ce,"Hajara ki iya bakinki a wurin nan, da mahaifiyata kike magana ya kamata kisan irin furucin da za ki dinga yi".
Gwaggo tayi siririyar dariya, ta shiga magana ita kaɗai. "hmm wai faɗa yake yi ahaka, yana magana a hankali kamar matsoraci, ta inda na ke takaicin haƙurinka kenan, Kai dai anyi dolon namiji, da ace Sulaimanu ne sai ta karɓi hukuncinta wallah, in bai lakaɗa mata shegen duka ba ai sai kwanan gidan iyaye a yau".
BINABASA MO ANG
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...