_Page 2_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*M* uhammad Muhriz, kyakkawan matashine kuma saurayi maiji da kansa da bazai haura shekaru 32 ba aduniya, hamshaqin mai kud'ine d'an kasuwa kuma d'an boko da yayi fice acikin garin na katsina, inda yafi bada qarfi ga kasuwanci gida da wajen qasar nan, iyayensa sun rasu tun yanada shekara goma sha biyar aduniya shi da qanwarsa Razina alokacin ita kuma tanada shekaru biyu kacal, sun rasu sanadiyar fashin da b'arayi suka kaimasu awani qauye da ake kira charanchi acan cikin jahar katsina, inda suka karkashe duka mazajen dake qauyen da kuma wasu matan da suka saka taurin kai wajen yunqurin tafiya da sukayi dasu, wanda alokacin mahaifiyar su Muhriz da Razina na mai suna Bilkisu na cikinsu, yayinda shi kuma mahaifinsa suka kashesa bayan d'auki ba dad'in da sukayi dashi wajen ceton rayuwarsa data iyalinsa da yayi, shi kansa Muhriz saida suka tafi dashi amma ALLAH yabashi ikon guduwa ya dawo ba tare da sun ganesa ba, koda yadawo gida ya tadda qanwarsa Razina a tsakar gidansu zaune cikin rana tanata faman kuka, da sauri yaje ya d'aukota had'e da fad'awa cikin d'akin mahaifinsa, inda ya taddasa kwance cikin jini anyi masa yankan rago, saurin saka tafin hannunsa yayi ya kwantar da kan Razina dake faman kuka a saman kafad'arsa ya durqushe agaban gawar ta mahaifin nasa ya saka wani irin kuka mai cike da ban tausayi wanda bayada mai rarrashinsa alokacin aduniya, babu babban tashin hankalinsa irin yanda kukan Razina ke ratsa kwakwalwarsa had'e da huda masa zuciya, yayi kuka irin kukan dake tabbatar da rashin gata da maraici da kuma hauhawar nauyi ga wanda keyinsa, yayi mintuna talatin awajen yana abu d'aya kafin yamiqe rungume da Razina data kasayin shiru har yanzu tamkar wacce tasan masifa da quncin da suka fad'a na rayuwa a yanzu, qarar bindigar daya jiyoce tasashi saurin fitowa daga gidan aguje cikin firgici da tashin hankali, yayinda itama ta sake fashewa da wani kukan,
Ba tare daya san inda zai nufa ba yakama hanya domin neman ceton rayuwarsa da kuma ta qanwarsa, yana kaiwa bakin qofar fita qauyen yayi tuntub'e da wata gawa ya kife ya fad'i qasa dashi har Razina, yunqurawar da yayi yamiqe idanuwansa suka sauka kan gawar, tsananin tashin hankalin da yake ciki ko kad'an baiyi tasiri ba wajen mantawa da fuskar mahaifiyarsu, ko shakka babu ita d'in ce, shed'arsa ce tafara kaida komo tana neman kucce masa saboda firgicin daya sake shiga na ganin gawar jigo kuma ginshiqin rayuwarsu akaro na biyu agabansa, cikin sheshshekar kuka ya samu damar furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirrajiun da qarfi ya fad'a ajikin gawar ba tare daya damu da mutanen dake fitowa cikin qauyen aguje suna wucewa ba wasu har suna takinsu, rarrafowa Razina tayi wajen itama ta haye gawar mahaifiyar tasu gaba d'aya tana kuka ganin d'an uwan nata awajen, tamkar dai yanda suka kashe mahaifinshi itama sun kasheta tahanyar dab'a mata wuqa aciki, amma da yake rai mai alfarma ne bata ida qarasa mutuwa ba tana jin sautin kukan daya tabbatar mata na yaranta ne ta farfad'o tare da jan wata irin shed'a dake nuni da ran be ida fita ba da sauri ya d'aga daga jikinta yana fad'in,
"Inna kada ki mutu, ki tashi Inna ga Razina na kuka, don ALLAH kada kimutu inna kibarmu kamar yanda baffanmu ya mutu ya barmu" yaqare zancen tare da jawo Razina daketa tsala kuka ya kara mata a fuska, riqo hannunsa tayi dake fuskarsa yana qoqarin goge hawaye ta sake zagaye jikin Razina dashi ma'ana ta d'ora saman wanda ya rungume Razina, cikin qarfin hali ta d'ago hannu tasa afuskarsa ta goge masa hawayen dake kwance akai tace,
"Ku gudu sannan ka kula da qanwarka Muhriz..." Kafin tarufe baki hannunta dake saman fuskarsa ya fad'i qasa alamun rai yayi halinsa, nan take Muhriz yaji tamkar ana rura masa wata irin wuta acikin jinin dake yawo a jikinsa, duk wani tsoro, tashin hankali da kuma fargaba sai yaji ya gushe masa, gaba d'aya yaji zuciyarsa ta bushe ta yanda zai iya fuskantar kowane irin qalubalen rayuwa a halin yanzu, hannu yasa ya shafe idanuwan mahaifiyarsu da suka kakkafe tare da d'aukar Razina dake kuka yasa hannu ya goge mata hawaye yana fad'in.
"Ya Isa haka Razina, kidena kuka ya zame mana dole mu fuskanci qaddararmu, a halin yanzu mune zamu tunkareta bazamu koma bari ta riskemu ba" Yana gama fad'ar hakan ya nufi hanyar komawa cikin qauyen babu tsoro ko misqala zarratin a zuciyarsa, acewarsa zai rayu acikinsa koda shi kad'aine da qanwarsa babu inda zasu je,
Yana kaiwa a tsakiyar gari yaji muryar mahaifiyarsa nadawo masa akunnuwa, "ku gudu Muhriz sannan ka kula da qanwarka..." kallon Razina data fara bacci yayi sannan ya maida kallonsa ga gungun b'arayin dake tunkarosu zasu ficewa daga cikin garin suna ihu da shewa suna qarawa, sai kawai ya tsinci kansa da rugawa ya fad'a can wani dajin badon ya tsorata ba sai don kawai yacika wasiyar mahaifiyarsa akan qanwarsa, amma badon wannan ba a yanda yake jin zuciyarsa zai iyayin fito na fito dasu saidai su kashesa. (Hmmm Muhriz kenan, ai tunda manyanka da jami'an tsaro, gwamnati suka kasa da lamarin wud'an nan b'arayin kaima bazaka iya ba sedai kawai akai qararsu ga ALLAH shine zai iya yimana maganinsu, amma sam qarfin zuciya ko na jiki ko makamai bazai iya da lamurransu ba sai qarfin addua kawai)
Gudu yayi sosai da bai tsinci kansa ako ina ba sai tsakiyar titi, tsabar gajiya baya iya yin komai gashi riqe da Razina wacce ga dukkan alamu babu fitar lumfashi ajikinta, da sauri wani mai motar haya ya fito daga qauyen qanqara daya tashi kadesu ya faka gefen titi, kasancewar marece yayi babu motoci da yawa yasa har ya d'aukikkesu daga kan titin babu abunda ya samesu, tambayar Muhriz yakeyi lafiya daga ina suke amma ya kasa bashi amsa sai nuna masa Razina yakeyi dake riqe a hannunsa gam, cikin tsoro mutumen ya dubi gefe da gefen titi da kuma hanyar daya hango sun fito yaga ba kowa ya d'aukesu su duka ya saka cikin motar sannan yaja sukabar wajen, dama garin katsina yayi sai kawai ya nufi can dasu, hannu Muhriz ya miqa ya jawo 'yar jarkar swan daya hango acan gefen driven da ruwa, mutumen be hanasa ba ya bud'e gorar ya tuttud'awa Razina a fuska da jiki, tafi mintuna biyu kafin can yaga taja shed'arta da qarfe ta maido had'e da fashewa da kuka alamun suma ne tayi ta farfad'o, murmushin qarfin hali yayi hawaye na zubo masa sannan ya d'auketa ya bata ruwan tasha sosai sannan ya qarasa shanye sauran shima had'e da fad'awa jikin kujerar motar yana fidda lumfashi d'aya bayan d'aya, duk wannan abun da Muhriz keyi drivern na kallonsa ta gefen idanuwa amma bai ce dashi komai ba har saida sukayi nisa sosai sannan yayi gyaran murya had'e da juyowa yana kallonsa yace dashi me yake faruwa da sune ya gansa cikin wannan halin kuma d'auke da 'yar qanqanuwar yarinya?, Banda kallonsa babu abunda Muhriz keyi har suka iso cikin garin katsina ba tare daya ce masa komai ba balle yasa ran zai samu ya bashi amsar tambayar da yayi masa, waje ya samu yayi parking agefe sannan ya juyo da niyar sake yimasa wata tambayar akaro na biyu sai kawai yaga ya bud'e marfin motar ya fice aguje d'auke da qanwar tasa, sosai abun ya bawa mutumen mamaki da sauri ya bud'e marfin motarsa amma sai kawai yaja motarsa yayi gaba, dama yana tunanin ina zai kaisu? Gida ko wajen hukumar 'yan sanda tunda yayi tambayarsa meya faru dasu yaqi magana, gashi ga dukkan alamu wani tashin hankali suka yoma gudu don alamu sun nuna haka.
PLS *COMMENT*
*SHARE*
*LIKE**ALLAH KAJIQAN IYAYENMU 👏😭*