_Page 4_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
"*T* saya daga waje!" Janan taji malamin nasu dr. Ingaski ya fad'a ba tare da ya juyo ba adaidai lokacin da take qoqarin aza qafarta ta shiga cikin aji, runtse idanuwanta tayi tare da komawa baya batare data aza qafar tata ba tana jin wani irin qunci da kuma sululi acikin zuciyarta, dama tasan za'a rina, mutumen daya takura rayuwarta ba tare da tayi masa komai ba balle yanzu data aikata laifin da tasan ko bashi bane hakan zata iya faruwa, ALLAH dai ya kyauta ta furta cikin zuciyarta had'e rolling idanuwanta tana furzar da iska abaki sannan takoma a gefen qofar ta tsaya,
"Sorry sir, I got an accident on my way coming that's way"
Ba tare daya damu da juyowa ya kalleta ba balle har ya saueari uzurin da take qoqarin kawo masa yaci gaba da yiwa d'alibbai lecture d'insu hankali kwance, saida ya kammala lecture d'insa tsaf sannan ya juyo yana qare mata kallo tun daga sama har qasa, hannayenta tasa ta jawo mayafin abayar dake jikinta tarufe qirjinta daya qurawa idanuwa tana turo baki, murmushin gefen baki ya sakar mata had'e da d'aukar teaching materials d'in daya shigo dasu yana fad'in, "meet me in my office Janan" sannan ya fice fuskarsa d'aure tamkar bashi bane yagama yimata kallon qurulla don kar d'alibbai suga damarsa, murgud'a baki tayi bayan ya wuce tare da qarasawarta cikin aji hankali kwance ba tare da tadamu da binsa baya ba kamar yanda ya buqata,
D'aure fuska tayi ganin yanda 'yan uwanta d'alibbai ke binta da kallo bakunansu d'auke da alamar tambaya akan qin bin bayan Dr ingaski da tayi,
"What?" Tafad'a tana zaro idanuwa tare da ware hannuwanta gefe gefe, alokacin d'aya daga cikin qawayenta da suke zama tare Amira ta samu damar yin ajiyar zuciya had'e da cewa,
"Janan bakiji me dr. Ingaski yace ne ba?"
"Naji man, sai akaye me?" Tafad'a had'e da zaunawa,
"Sai akayi me ma kike tambaya Janan, halama kin manta ko waye shi?
"ALLAH ne shi?"
"Ko d'aya, mutum dai ne mai tsananin iko akan karatunku, don girman ALLAH kirufa mana asiri ki tashi kije kada kishafa mana kashin kaji awurinsa"
"Tab! Wlh bazani ba, me zanje nayi masa bayan 'yar lecture d'in tasa da nake kwad'ayin samu da attendance don gudun matsalarsa ya hanani?, Kawai ki qyalesa na manta ne shiyasa banje ba, dt's zit"
"Hmm! Gamu ga ALLAH" Amira tafad'a tana zabga wani uban tagumi,
Dariya janan tayi had'e da dukan bayanta, "Amira kenan, dama ke a hannun Ingaski kike ba'a hannun ALLAH ba?"
"Mts...kidena don ALLAH, wlh gaba d'aya a tsorace nake, ban cika son kina shiga 18 d'in malamin nan ba" taqare maganar tare da cire hannun janan d'in daga bayanta.
"Matsoraciya kawai" Janan tafad'a tana jawo takardun dake gaban Amira da tayi jotting.
"Naji dai koma meye zakice, tsoro ai gaskiya ne, musamman na irin wud'annan malaman da basa fatan gamawa lafiya da dalibbansu"
"Kyaji dashi nidai, dame dame yayi maku ne?, pls help me and explain it for me"
"Bazan iya ba, jeki keda ba matsoraciya ba yayi maki, bama wannan ba, meya sakaki latti Janan keda bakya son abunda zai had'aki dashi?
"Bari kawai, ai daga yau angama don bansan meye amfanin da tsoron nasa ke haifarmun ba, kinafa ji nake fad'a masa accident nayi kafin naqaraso amma yayi banza dani, shiyasa nima nayi banza dashi saboda duk abunda yafaru yau shine silar dana aikata hakan, don haka wlh munsa qafar wando d'aya dashi kenan Amira"