_Page 59_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
Kuka take yi sosai kai ka ɗauka mutuwa akayi mata, Zarah da Umma sunyi rarrashi har sun gaji sun samata idanuwa, sosai umma ke jin takaicin kukan nata a ranta amma babu yanda ta iya dole tasa mata idanuwa, saboda tasan ba ita ta ɗorawa kanta soyayyar yaron ba don haka duk abunda za tayi bata isa ta dakatar da ita daga abunda take ji ba, sai da tayi mai isar ta ta gama sannan bacci ya yi awon gaba da ita, amma duk da haka ba abun da takeyi cikin baccin banda ajiyar zuciya tamkar wata ƙaramar yarinya, ita dai umma na zaune kan dardumar ta tana faɗawa ALLAH damuwowin ta har aka kira sallar asuba, sabbatu kuwa da buge-buge Amira ta shasu tsakar dare don har sai da taso karewa Umma sallah, hakan ya sa koda ta tashe su sallah da asuba gaba ɗaya jikin ta ciwo yakeyi, yanda take faman yatsinar fuska ya sa umma yin murmushi haɗe da cewa,
"Sannu Sarkin yaƙi in jin kin fanshe duk abunda ke zuciyar ki"
Kallon Umma ta yi da kumburarrun idanuwan ta da tasha kuka daren jiya haɗe da ɗan turo baki ta ce,
"Me yafaru Umma? Ni gaba ɗaya ma ji nake duk jikina nayi mun ciwo"
"Ai dole, wannan buge buge da kikayi jiya kamar mai faɗa da wani, ni dai in ya tsaya cikin bacci ɗai ai mun gode ALLAH" murmushi ta yi sannan ta miƙa haɗe da cewa,
"Umma kenen, ai kuma nariga dana haƙura, in sha ALLAH ba abun da zai faru, dama mun gama practical exam ɗin da za muyi zan roƙeta ta yafe mun duk abunda ke tsakanina da ita don nayi mata abubuwa da yawa akansa, kuma na tabbata ta sani kawai ta ƙyaleni ne, saboda daga yau umma ina mun rabu da ita ban san ta inda zan kuma sake haɗawa da ita ba"
"Kin yi tunani mai kyau Ubangiji ALLAH yayi maki albarka"
"Amin ya rabbi Umma" ta faɗa tare da ficewa daga ɗakin tana jin wani kuma na sake zo mata, yanzu shikenan mm ya yi mata nisa, data haƙura dashi dama kar ta haƙura babu yanda za tayi, ta faɗa cikin zuciyar ta tare da jin kukan ya kucce mata, da sauri ta rufe bakin ta cikin muryar kuka tana faɗin,
"Ya ALLAH kai ka jarabce ni da son bawan ka ba tare da nasan dalilin yin hakan ba, ALLAH na roƙeka ka bani dangana da haƙurin mantawa dashi" ta ƙare maganar tana share hawayen dake kwance kan fuskar ta da hannu biyu,
Bayan ta gama Sallah ta ce Zarah ta miƙo mata wayar, saboda tana so tayiwa Janan fatan alkhairi kamar yanda taga sauran abokanan karatun ta nata yi mata, nan umma ke faɗa mata cewa sai dai tayi haƙuri wayar ta riga data shahe jiya data faɗi a hannun Zarah,
Bata ce komai ba ta tashi ta nufi tsakar gida tafara sabgogine data saba yi akoda yaushe, bayan ta gama ta watso ruwa tare da dawowa ta ɗauko littafan ta tana sake dubawa tunda jiya bata samu tayi karatun ba, dama sai umma ta tashi sallolin dare take ta data itama tayi karatu idan suna exam,
Kasancewar sai zuwa sha biyu zasu fara exam ɗin ya sa bata fita ba sai da taga ƙarfe sha ɗaya har da kusan rabi tayi sannan ta miƙe ta saka hijab ɗin ta tare da kallon Umma dake tsintar wake zata ɗora girkin abincin rana ta ce,
"Umma na tafi"
"To adawo lafiya, in sha ALLAH kafin ki dawo zan sa Zarah taje shagon can na _ya mu samu communication_ ta tambayo ko nawa za a gyara wayar, zuwa ƙarshen wata idan ALLAH ya hore sai na bayar a gyara maki"
"To Umma Nagode"
"ALLAH ya baku sa a ku duka yasa ku fito da kyakkyawan sakamako"
"Amin Umma na" ta faɗa tare da rungumeta sannan ta fice, a ƙofar gida ta haɗu da Zarah ta dawo daga wajen sayen omo za tayi wanke wanke,