PAGE__7

171 6 1
                                    

_Page 7_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

_Wattpad@billysfar9https://www.wattpad.com/1231887990?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=y3hZPXsR3hFuYm5xsZGdA7ie%2Bxtl6Je1fSdRjxdLY%2BRRYi%2FIiEGinlbsNrmL6MNpxDxsUoIbJ95KSwc9nFtd%2FQZBru%2B0vmFUYEe3iJQabmq5fLoickCYt6guQHzAZi96_

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*

INA KUKE MAKARANTA??

INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️

TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B

INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.

DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA

(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN

👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
---777778
______________________________

*S* aida ta ga ficewarta tukuna ta koma cikin gida itama ta nemi waje ta zauna ta ƙarasa sauran abin karin data ɗibama Janan, bayan ta gama ta koma cikin ɗakinta ta haye kan gadonta ta jawo system ɗinta ta shiga vedio call da ƙawayen ta dake ƙasar uganda da sukayi karatu tare, wanda mafi aksarinsu har yanzu suna can ƙasar a dalilin aiki daya kai iyayensu suke zama acan.

Janan kuwa da gudu ta fice daga cikin gidan rana ba motar wuta har ta kai bakin gate ɗin makarantar, a hankali ta soma rage wutar motar lokacin data isa kafin nan ta shiga ciki don gudun kar abun daya faru jiya ya sake faruwa, cikin yardar ALLAH har ta ƙarasa department ɗin nasu ta daidaita tsayuwar motarta haɗe da fitowa ta shiga cikin ajin malamin bai zo ba, lokacin har ƙarfe takwas da mintuna biyar tayi, ajiyar zuciya ta sauke haɗe da samun waje ta zauna tana kallon Amira da tayi tuƙun-tuƙun da fuska ta d'auke kai, saida ta jima da shiga sannan malamin nasu dake ɗaukarsu course ɗin (chemical-Ako-Carbony/compound) a fannin Chemistry/computer da take karanta ya shiga, cikin natsuwa da kwanciyar hankali ta fara sauraren bayanan da yake yi, kasancewar tanada tsananin kaifin basira yasa cikin ƙanƙanin lokaci ta gama fahimtar dukkanin abinda yake koyarwa, don indai ƙoƙari ne to Janan ba baya ba, irin ɗaliban nan ne da ake kira da intellegent, ba kowa ne zai fahimci hakan a tattare da ita ba sai wanda suka zauna tare, sai kuma su kansu malaman kasancewar ita ɗin tana ɗaya daga cikin sahun ɗaliban da ake kira introvert acikin aji, duk da tanada basira sosai basa fahimtar hakan har sai idan anyi mata tambaya ta amsa ko kuma idan anzo wajen test ko jarabawa  a nan ne take baje dukkanin basirarta da kuma baiwar da ALLAH yayi mata har suka gane irin talent ɗin da take dashi.

Bayan sun gama ta ɗago ido tana kallon Amira data ɗaure fuska ta kauda kai gefe tana ƙoƙarin miƙewa, da alama har lokacin bata daina fushin da takeyi da ita ba akan abunda ya faru, murmushi tayi tare da riƙo hannunta, ta ce

"Amira barka da safiya, kin tashi lafiya"

Ba tare data juyo ta kalleta ba ta ce "lafiya" can ciki ciki, murmushi Janan ta sakeyi karo na biyu tare da miƙewa tsaye ta dawo gabanta suna fuskantar juna, ta ce

"Amira kenan! Wai har yanzu fushi kike dani akan abunda ya faru jiya? To kiyi haƙuri don kuwa ni har na manta da hakan, kuma nasan ai duk wannan abun da kikeyi akan na kaɗe mm ne na kasa tsayawa na kula dashi ko? To kiyi haƙuri shima jiya na je na bashi haƙuri har ma na ɗaukesa a mota muka je clinic aka bashi magani, ina shikenan ai ko?"

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now