_Page 40_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
______________________________
Murmushi tayi cike dajin daɗi ta miƙo masa hannu, ƴar hararar ta yayi irin ta masoya ɗin nan kafin ya miƙa hannu yana ƙoƙarin riƙo hannun nata tayi saurin janyewa tana dariya,"Sorry mr.man, har yanzu da sauran lokaci, yi ƙoƙarin jajircewa akan wannan tayin dana yimaka, don kuwa farashin nasa tsadaddene" saida ya shafo haɓarsa yana ƙare ma kyakkyawar halittar ta kallo sannan ya ce,
"Duk girman tsadar sa a shirye nake dana siya koda kuwa komai nawa zai ƙare, ciki har da rayuwata amma bayan na aureki" ya ƙare zancen yana nuna ta da ɗan yatsa haɗe da kashe mata ido ɗaya, murmushi ta saki tare da sakin marfin motar da take riƙe dashi ta juya ta rufe sannan ta juyo tana kallon sa,
"Ka yanka kuwa?"
"Me ya faru?"
"Kayi masifar kyau, kamar na saka maka niƙab" buɗe baki yayi haɗe da zaro idanuwa yana tafa hannuwa kafin ya riƙe haɓar bakin sa,
"Liƙabi kuma ni Muhammadu?, Don ALLAH rufan asiri tunda dai ba macce nake ba" Janan na dariya ta shiga takawa a hankali ta nufi inda ta hango Jabir tsaye yana dannar waya,
"Ina kwana?" Ta gaida mm kafin su ƙarasa wajen,
"Lpy klw my princess, kin ganki kuwa?" ta ɗago kai tana murmushi ta kallesa haɗe da cewa,
"Za ka rama kenan!"
"Ko ɗaya, kinfi kyau kyaune nagani shiyasa nayi magana"
"Na kai ka?"
"Wake zancena ranki shi daɗe, ai kyan ma kin fisa kyau nake faɗa maki, badon kar na takuraki ba da nace ke yakamata ki riƙa saka niƙabi kina ɓoyemun kyakkyawar fuskar nan taki ni kaɗai"
"ALLAH hubbin ruh"
"Sosai ma kuwa"
"Ya Adda Nihal?"
"Tana gida na baro, lafiya klw"
"Ta huta abunta, ita sam bata gajiya da zaman gida"
"Haka rayuwar ta take, bata son mutane shiyasa bata fiye son mu'amala dasu ba, har aiki Abba ya nema mata amma ta ce bata so, kuma ya ƙyaleta"
"Tab, ai kuwa mutum rahama ne, kuma data daure tayi amfani da damar ta tun yanzu, nidai a nawa fannin banga laifi ba don macce tayi aiki, at least kodta zata zama dependant kaɗan ne ko ba haka ba?"
"Haka ne kam, amma rayuwar tace, kuma tunda haka ta zaɓa babu yanda zamuyi da ita"
Daidai lokacin suka iso inda Jabir ke tsaye ya ɗago kai ya kallesu, sannan ya ce,
"Ai nazata ma bazaku ƙaraso ba, kuna wata tafiya a hankali sai kace wuɗanda basa son taka ƙasa" ya ɗan ja tsaki haɗe daci gaba da cewa,
"Ni nafara gajiya da wannan tsayin malam idan ku bakwa buƙatar zama" kallon Janan dake kallon Jabir cike da tsantsar so irin na ƴan uwantaka mm yayi haɗe da cewa,
"Kin ga halin mutumen naki ko?"
"Ai da gaskiyar sa, tuba muke ya Jabir ayi haƙuri"
"Ƙyalesa Janan, ai nasan duk laifin nasa ne, ya kike?"
"Lpy klw, ina kwana"
"An tashi lafiya mrs.mm" ya faɗa cikin sigar tsokana yana gyara tsayuwar sa, Janan dake ji tamkar ta bayyana masa matsayinta awajensa don suyi shearing farincikin ta ce,