PAGE__29

122 4 1
                                    

_Page 29_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*
______________________________
"Bye hubbin ruh, muyi waya anjima kaji" ta faɗa cikin sigar yanga da shagwaɓa, dariya ya saki don ba kaɗan yake samun nishaɗi ba idan tana yi masa iren-iren wannan shagwaɓar sannan ya ce

"Ok babynah bye, I luv you..."

"Luv you too hubby" itama ta faɗa tare da kashe wayar, daidai lokacin mahaifinta ya ƙara so wajen don yana gama yi mata magana ya sauko, sadda kai tayi cikin girmamawa haɗe da cewa

"Good morning Abba" ba tare daya amsa taba ya miƙa mata hannu yana faɗin,

"Miƙo mun makullin motar nan"

"Abba saboda me?, Meyasa zaka ce kada nafita ko ka mantane akwai school yau" ta ƙare zancen tana miƙa masa makullin motar ba tare da tayi masa musu ba tamkar zatayi kuka, fuskarsa ɗaure ya amsa haɗe da cewa,

"Ban manta ba, ki jira Asgar zai zo ya kai ki, daga yau ban yarda ki sake fita ke kaɗai ba shiyasa na yanke hukuncin Asgar zai zauna anan domin yaci gaba da kai ki makaranta har zuwa lokacin da zaki ƙare"

"What?" ta faɗa da ƙarfi idanuwanta na kawo hawaye, Muryar Nihal ta jiyo da bata san lokacin data ƙaraso wajen ba na faɗin,

"No Abba, kada kayi hakan domin kuwa kuskure ne, samarin yanzu ba abun yadda bane musamman waɗanda sukayo cuɗanya da 'ya'yan turawa, inaga kuskure ne kace zaka haɗa janan dashi ya riƙa kaita makaranta saboda komai zai iya faruwa, don haka Abba kabata makullin motar ta ta tafi don ALLAH" ta ƙare zance tare da warware hannayenta dake naɗe akan ƙirji ta haɗe waje ɗaya alamar roƙonsa, sinne kansa ƙasa yayi na tsawon saƙwanni kafin ya ɗago yana kallon Nihal ɗin sannan ya juyo ga Janan ya miƙa mata makullin yana faɗin,

"Shikenan kiije, amma ki sani idanuwana na akan ki akoda yaushe, idan kika kuskura kika yi wani abun ya dawo kunnuwana zaki sha mamaki" yana gama faɗar hakan ya ƙwalawa Jazz dake tsaye a bakin gate kira, da gudu ya ƙara so wajen cike da girmamawa ya ɗan rissina kai yana gaishesa, ko ta kan gaisuwar sa baibi ba ya ce,

"Jazz kubi bayan Janan, kuma ku tabbata daga makaranta babu inda taje har ta dawo, sannan idan wannan yaron yayi kuskuren tunkaro inda take, to ina so kuyi masa abunda ya dace dashi kafin ku dawo"

"Ok sir" Jazz ya faɗa tare da tafa hannuwan sa sai ga sauran guard ɗin duk sun fito,

Ita kuwa Janan abun ma ɗaure mata kai ya soma yi, duk da tasan haka zata iya faruwa, amma bata taɓa tsammanin Abban nata zai ɗauki matakin da ya yi girman hakan ba, tsaye tayi ta zuba idanuwa tana kallon ikon ALLAH sai faman jawo motoci guard ɗin suke yi kuma wai duk wa ita, murmushi mai cike da takaici ta saki tana kallon mahaifin nata dake tsaye yana jiran su gama cika umurnin daya basu, cikin muryar kuka ta ce,

"Abba wai duk wannan abun na meye?, Janan ce fa 'yar ka, ko ka manta ne?" A hasale ya juyo yana nuna ta da yatsa haɗe da cewa,

"Wannan sunan tana amsa shine a lokacin data tabbatar wa da kanta cewa ita ɗin 'yata ce, amma a yanzu da take ƙoƙarin bijirewa umurnina bana tunanin cewa ta yarda har yanzu ni ɗin mahaifin tane"

"Abba.." da hannu yayi saurin dakatar da ita haɗe da cewa "ya isa haka Janan, bana son jin komai daga bakin ki, kuma daga yau in har kina son fita dole ayi cikin ɗayan cikin biyu, ko Asgar ya riƙa kai ki duk inda zaki je ko kuma su Jazz su kasance atare dake a duk inda zaki, wannan shine" yana ƙare faɗar hakan ya wuce cikin gida abinsa saboda yasan dole guard ɗin zasu aikata abunda ya sa su, da sauri tabi bayansa kamar zatayi kuka Nihal tayi saurin dakatar da ita,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now