_Page 13_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1233714499?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=%2FZCXoGlLdbifSbATAz2UeuNRbhPFrpZVPNq3kNLZza%2FgPkeFJV9VLz7dzW3EBnlU9nks2qvKGiGfL2Iho68XT3LgMsgq%2BngDoogWVxyZOE9%2BipwLz1FYqd1pacbjPKT0_
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_
👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
______________________________
*B* ata tsaya ko ina ba sai a can bayan science theater in da suke ɗaukar lectures wani lokacin ta ci kukanta mai isarta sannan tayi shiru ta goge fuskarta da nan take ta yi jajir haɗe da bayyana halin da take ciki, haka ma idanuwanta da suke farare ƙal sai da sukayi ja har wata 'yar siririyar jijiya na ratsawa ta tsakiyarsu, cikin natsuwa da damuwar dake faman nuƙurƙusar zuciyarta ta nufi wajen su mm, don gaba ɗaya ma ta manta da zancen Amira ta ce zata karɓar mata, murmushi ta fara ƙoƙarin ƙaƙarowa lokacin data ƙara so wajen haɗe da kallon sa ta ce,"Sannun ku mm, kayi haƙuri kaga ban ƙara so karɓar saƙona ba sai yanzu ko?"
"Eh, akwai wata yarinya da nake ganinsu tare tazo ta karɓar, amma me yake faruwa dake ne haka Janan?" Ya faɗa yana kallon cikin idanuwan ta haɗe da ƙare mata kallo, sun kuyar da kanta tayi tana jan majina a hancinta haɗe da cewa,
"Bari inje muna da practical yanzu" ta juya har lokacin kanta na sun kuye a ƙasa, cike da damuwa mm da gaba ɗaya duk hankalinsa ya bi ya tashi ganinta cikin wannan yanayin tare da miƙa hannu alamun tsai da ta kamar zai yi kuka, ya ce
"A'a Janan, kada ki tafi cikin wannan yanayin hakan, don ALLAH idan zaki iya ki faɗamun me yake faruwa ne?"
Cak ta tsaya wasu zafafan hawaye na zo mata, haka kurum taji ta kasa yimasa musu ta tafi, a hankali ya juyo yana kallon Jabir fuskar sa ɗauke da damuwa ya ce,
"Jabir bani mintuna biyu ina zuwa?" Ya kaɗa masa kai don shima bai ji daɗin yanayin da yaga Janan aciki ba, sai daya fara zuwa wajen wata mata dake kusa dasu dake sayar da kunun aya da ruwan sanyi ya karɓi ƙwayar ɗaya sannan ya nufi wajen da take tsaye ta sinne kai har lokacin tana kuka ya miƙa mata ruwan,
"Ungo wannan kisha don ALLAH ba don ni ba Janan" ba musu ta karɓa ba tare data ɗago kanta ba ta fasa ladar ruwan ta sha sosai haɗe da cewa, "Na gode" cikin muryar kuka, sake rikicewa mm yayi yaji kamar ya buɗe zuciyarta ya yaye mata ɓaci rai da ƙuncin daya saka ta cikin wannan yanayin, amma da yake baya da hurumin yin hakan sai kawai ya kalli can tsallake titi inda guiding luv ɗin makarantar yake, ya ce
"Ko zamu iya zuwa can?" Ya ƙare zancen yana nuna mata wajen da hannu, ganin bata ce komai ba ya sa kawai ya wuce gaba ta bisa baya suka nufi wajen, Ɗaya daga cikin kujeru dake wajen ya nuna mata ta zauna shi kuma ya jingina ajikin iccen dake fuskantar kujerar yana kallon yanda take wasa da hannun ta, don agaba ɗaya jin ta tayi wani iri kasancewar su a waje ɗaya tare kuma alokacin da batayi tsammanin hakan zai faru a tsakanin su ba, ji tayi yayi gyaran murya haɗe da cewa,