PAGE__61

171 5 0
                                    

_Page 61_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

Kamar kullum yau ma Umma ta shirya don taje police station duba Amira duk da ba barin ta ganin ta akeyi ba, kallon ta Zarah tayi haɗe da cewa "Umma ya kamata kiyi haƙuri haka ki zauna gida ki huta, kinga ba ko wata isashshiyar lafiya ne dake ba, tunda har ba barin ki sukeyi ki ganeta ba kibari naje na kai mata abincin"

"A'a Zarah, bazan iya barin ki kije wannan wajen ba, nima don ta kama dole nake zuwa, Al-amin bai kai girman da zan iya turasa ba ai dashi zai riƙa zuwa, sai yanzu nake ƙara jin ɗacin rashin ya yanku a tare dani domin wajen maza ne suka fi cancanta da zuwansa ba mata ba"

"Umma dama muna da yaya bamu sani ba?"

Share hawayen da suka zubo mata tayi haɗe da cewa,

"Ƙwarai Zarah, kuna da yaya da kuma ya macce, sai dai ba mahaifin ku ɗaya dasu ba?"

"Amma Umma ya akayi baki taɓa sanar damu ba?"

"Meye amfanin sanar daku tunda ban sani ba suna raye ko sun mutu, wannan cikin da nake fama dashi shine silar daya sani ɗaukar wa mahaifin ku alƙawarin bazan koma ɗauko zancen su ba, saboda aduk lokacin da nafara tunawa dasu ko kuma zancen su komawa nakeyi tamkar wata zararra saboda damuwa, mutum ne shi mai son farinciki na da kuma damuwa da dukkanin lamurra na shiyasa aduk lokacin da na shiga cikin irin yanayin sai ya zamana damuwar sa ta kere tawa damuwar saboda shima yana fama da matsalar hawan jini da diabetes, dalilin daya sa kenan na ɓoye wannan damuwar a raina don wanzuwar nasa farincikin"

"Tirƙashi! Amma umma tunda ba kida tabbaci akan mutuwa sukayi ko kuma ɓata me yasa baki kai cigiyar neman su ba agidanjen redio ko television da kuma gidajen jaridu ko ALLAH zai sa a dace a gane su"

"Ba muda wannan ƙarfin ni da bayin ALLAHn da suka taimake ni, bayan haka tun lokacin dana gudu daga ƙauyen daya kasance asalin mahaifa ta ni da mahaifin su ban koma waiwayar sa ba saboda bana son tunowa da abubuwan da suka faru balle na samo hotunan su, ALLAH na barwa cigiyar su ta hanyar addu'a, nasan matuƙar suna raye wata ran zasu dawo gare ni"

"Duk da haka Umma...." Tari ta fara yi haɗe da dafe saiti zuciyar ta tana jin wani irin zafi, hakan ya sa Zarah dakatar da maganar da take son faɗa tare da miƙewa ta riƙota daga tsayen da take ta zaunar da ita tana faɗin,

"Sannu Umma"

"Yawwa bani ruwa nasha"

Haɗowa tayi har da maganin ta ta ɓaɓɓalla mata ta bata ta sha, a hankali take sauke lumfashi har ta samu ciwon ya lafa mata, miƙewa ta sake yi Zarah ta ce, "Umma don ALLAH ki haƙora da tafiyar nan"

"A'a Zarah, bari naje ai na samu sauƙi"

"Shikenan, amma kuke tare da Al-amin sai ya riƙa maki kwandon"

"To ba laifi" ta faɗa Zarah ta ɗan daki Al-amin a ƙafa dake bacci ta ce ya tashi ya ɗauki kwandon ya raka Umma,

Har sun kai bakin ƙofa Umma ta juyo haɗe da cewa, "Zo kije gidan baba mai ƙuli kafin mu dawo kar ki zauna ke kaɗai"

"To Umma" Zarah ta faɗa tare da ɗaukar mayafinta ta rufo ɗakin suka fita tare, sai da ta raka su har bakin titi sannan ta nufi gidan baba mai ƙuli,

Kasancewar yau Lahadi mafiya yawan police ɗin dake aiki wajen Christian ne duk suna coci ya sa police station ɗin yin tsit sai ɗai-ɗaikun hausawan ƴan sanda dake kai da kawo wajen kula da masu laifi da kuma masu kawo ƙorafi, Sajan Maryam ita ta karɓi abincin Amira ta kaimata sannan ta dawo ta zauna tana kallon Umma da kallo ɗaya zaka yimata kasan ba tada cikakkiyar lafiya cike da tausayi, cikin harshen Hausa da bai zauna a bakin ta sosai ba don yare ce ita ba bahausa ba ta ce,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now