PAGE__63

260 7 6
                                    

_Page 63_

*TUKUICIN SO💞*

*NA*

*BILLY S FARI💎*
        
                      *END*

Duk da taron bana dinner bane ba kuma anyi sane don casu ko wani abuba hakan bai hana sound ɗin kiɗa mai taushi tashi daga cikin hall ɗin ba, sauti ne mai tsananin daɗin saurare da kuma ratsa jiki sai hasken fitillu dake haska wajen da wasu irin launona masu matuƙar ɗaukar hankali, waje ne na musamman da aka tanada domin iyayen ango da kuma amarya aka kai su Baffa da mutanensa da kuma Abba da Ambassador da sauran manyan baƙin su, dama tuni ma aikatan hotel ɗin sun cike kowane benci da zai ɗauki aƙalla mutane takwas da manya manyan tireruwan snacks naman rago gasashshe, naman kaji soyayye, tsire priderice da tasha haɗi da kayayyakin lambu, da sauran cimakar da idanuwana baza su iya cewa ga ko meye ba, ga kuma juice juice masu matuƙar tsada da ruwan gora a gefe, sai ƙwanƙwon sakace haure da tissue paper dake ajiye a tsakar bencin, haka kuma agaban kowane mutum ɗaya akwai plate da spoon da pork haɗi t da irin ƴan yuƙaken nan da turawa ke amfani dasu wajen cin abinci tare da cups ajiye, kowa sai abunda ya yi masa zai ci kuma zai sha, ba nan abun ya tsaya ba a gefen kowace kujera da mutum ya zauna zai tadda matsakaiciyar jikka dake ɗauke da, biro, handcachip, ceremonial books da kuma cups dake ɗauke da hoton amarya da ango aciki, iya naka kawai ka ɗauka idan zaka tafi, haka kuma ma'aikatan basu zauna ba sai round suke yi incase ko akwai wanda zai buƙaci wani abun, banan abun zai baka shawa ba, yanda abokanan ango gaba ɗayan su suka taru inda aka tanada domin iyayen amarya da ango suna yimasu sarving abinda duk da zasu ci da kansu, acewar su wannan wata hanya ce ta girmama iyayen nasu da kuma mika godiya agare su, dukkan su saye suke da fararen shaddodi da suka matuƙar yi masu kyau, hatta abokanan sa turawa da suka zo suma shaddodin ne ajikinsu suka sa abun tubarkallah sai ɗaukar idanuwa suke yi, wani iska ambassador Hussain ya furzar ta baki haɗe da sauke ajiyar zuciya ya juya yana kallon Abba da har lokacin sai faman goge gumin yakeyi da gefen babbar rigar sa yana faman raba idanuwa,

Muryar Jabir ya jiyo ta kansa cikin girmamawa tamkar ba shi ba yana faɗin,

"Haƙƙin mu ne kula da jin daɗin duk wani baƙo daya hallara a wannan bukin namu, don haka zaka iya yin magana Abba idan akwai wani abun ko kuma abunda kake buƙata, na tabbata yanzun nan za'a sama maka shi" yana rufe baki ya tafa hannu sau biyu sai ga masu aikin hotel ɗin duka sun iso wajen, cikin bada umurni ya ce,

"Iska ya yi kaɗan ga mahaifin ango mu da amarya, don haka za a iya ƙara gudun na'urorin ɗakin" kamar jira suke ya gama bada umurni nan take duk suka rarraba zuwa wajen maku nan na'urorin a.c dana fanka, kan kace me tuni yanayin sanyin wajen da ƙamshin sa ya ƙara sauya wa, ɗari kai Abba ya yi ya kalli Jabir da kyau kafin ya maida kan nasa ga plate ɗin dake gabansa dake shaƙe da abubuwan morewa da tun ɗazu ya kasa taɓa ko guda, kusan gasasshen rago biyu ne akan dogon bencin nasu amma komai ya kasa ci, gorar ruwa kaɗai ya iya miƙa hannu ya ɗaukahaɗe da buɗe bakinta ya aza ga baki, sai daya kusan shanye ta tas sannan ya iya ajiyewa tare da kallon ambassador Hussain da shima ya kasa cin komai ya matsa kusa dashi zai yi magana, Jabir ne ya sake ƙarasowa wajen da sauri yana faɗin,

"Akwai wani abu da kake buƙata ne Abba?" Tare dayin tsaye akansu, runtse idanuwa Abba ya yi haɗe da girgiza kai yana furzar da iska ta baki sannan ya gyara zaman sa daidai don maganar daya so suyi da ambassador bazai iya yin ta agaban Jabir ba, gaba ɗaya yabi ya takura sa da sunan kulawa ko motsi mai ƙarfi baya da ikon yi sai ya zo ya ishesa da tambayoyi, ganin haka yasa Jabir yin murmushi haɗe da duƙowa kusa ga Abba ya ce,

"Sorry sir" sannan yabar wajen, ko second biyar bai yi da jaye wa wajen ba sautin microphone ya mamaye wajen ana faɗin,

"Hello, hello" don janyo atteniɗin mutane a wajen, ba tare da mai maganar ya bayyana ba yafara bayanin cewa suna yiwa kowa sannu da zuwa tare da fatar komawa gida lafiya, sannan ya gabatar da cewa ango zai iso wajen don yin godiya bisa amsa gayyatar su da kuma taya su murna da suka zo yi, wani lallausan sautin aka sake sawa haɗe da canja launin hasken fitillun wajen zuwa masu ɗan duhu, amma duk da haka za a iya hango abokanan ango dake biye dashi sun sanyo sa a gaba zuwa gaban hall ɗin, suna isowa wajen duk suka koma bayansa suka tsaitsaya, cikin sanyin murya ya fara maganar kamar haka,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now