_Page 20_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
*KIN SAYI SHIRINMU NA TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B?, IDAN BAKI SAYA BA MAZA KI HANZARTA KI MALLAKI NAKI TA HANYAR WUƊANNAN LAMBOBIN DOMIN SAMUN ƘARIN BAYANI
+447894142004, 07065283730, LITTAFAI BAKWAI DA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU MASU MATUƘAR ƘAYATARWA AKAN NAIRA DUBU ƊAYA (1000) KACAL, ƳAR UWA GWADA KI GANI IDAN KINA CIKIN WUƊAN DA SUKAYI RASHIN BATCH A ƊIN MU, NA TABBATA BAZA KIYI NADAMA BA😍*
______________________________
Mm kuwa leƙawa yayi ta jikin tagar mota yace da Jabir daya tasa Razina a gaba yana yi mata labaran ban dariya tana kwasar abutta hankali kwance,"Malam fito muyi Sallah"
"In bar matar tawa cikin mota ita kaɗai?"
"Ohon maka, in zaka fito malam ka fito tayarwa za a yi yanzu"
"Gaskiya jeka, ai addinun nasiha malam, ai isham ce, zan iya yi idan zan kwantawa"
Zaro idanuwa mm yayi ganin da gaske Jabir keyi har yana gyara zama, tsaki ya ja haɗe dasa hannu ya buɗe ƙofar da Razina take zaune ya ce,
"Ke fito ki jiramu anan tunda shi ɗin bazai fito ba, wannan ai kai ne mayen soyayya bani ba"
Habawa kafin mm ya rufe baki har Jabir ya fito ransa a ɗan ɓace ya zagayo ta inda suke yana faɗin,
"Wai meye haka mm zaka wani fiddo mun da mata kan titi kowa ya gama kallemun ita, ba fa na son haka, pls my wife taimaka mun ki shiga daga ciki kar zuciyata ta buga, don ga wani munafiki can na hango yana arwala yana kallon ki" ya ƙare maganar fuska a ɗauke tare da sa Razina ta koma cikin motar tana faman yi masa dariya, shima mm dariyar ya basa don haka sai kawai ya mere baki yabar wajen, dama da arwalar su ta magrib, sai ya faɗa masallaci kawai, Jabir kuwa sai da yaleƙa ya cewa Razina,
"Wato dariya ma kikeyi ko?, Zaki dena ne idan kika ji ance gani can ana dambe dani da shi a masallaci saboda kalmar mun mata da ya yi"
"Kayi haƙuri na dena, ni da bana kallon kowa a matsayin namiji sai kai, haka kuna nima bana da banbanci da namiji a idanuwan kowane namiji in ba kai ba, ƙyale yaya mm jeka kayi sallah kayi mana addu'a kaji zauji na"
Murmushi ya saki haɗe da shafa kai saboda jin kunyar yanda ƙaramar yarinya ke driving ɗin sa like crazy haɗe da barin wajen da sauri jin har anyi ruku'i, kusan mintuna goma sha huɗu suka shafe kafin su dawo daga wajen sallar, suna dawowa suka nufi hanyar gida suna tafe mm na bashi labarin yanda sukayi da Janan ɗazu, wai ta gane sa lokacin da suka shigo round, sosai Jabir ya s dariya haɗe da cewa,
"Kace kawai asirin ka ya tonu"
"Asirin mu dai malam, ai guguwar da bata barni ba bazata taɓa barin ka ba"
"Wannan kam dole sai ta barni, kai ne dai aruwa"
"To shikenan, ina ga dai zan rage fita da mota, hak kuma zan dena zuwa bebeji dama ɓarayin cikin garin nan"
"Kai ta jiyo malam, ni dai na faɗa maka tallan ma na kusa dena raka ka, zan koma shafi abunda kai kuma sai kaci gaba da gashi ko ba haka ba wifey?"
Ita dai Razina dariya kawai tayi bata ce komai ba, amma in son samunta ne gaskiya masoyin ta ya dena fita tallar nan haka rana na koɗa mata shi haka, ga shi 'yan mata kullum cikin kalle mata shi suke,
Bayan wata ɗaya da faruwar abubuwan da suka wuce tsakanin Jabir da masoyiyar Razina, Janan da masoyinta Muhriz, Amira da ƙawar ta Janan, Nihal da the charming ɗin ta, ingaski da kuma ɗalibar sa Janan, cikin wannan lokacin soyayya da shaƙuwa mai tsananin ƙarfi ce ta sake shiga tsakanin mm da Janan, inda suke jin baza su taɓa iya rayuwa ba idan babu junan, matuƙar bata da ecture ko kuma sun ƙare to fa suna tare maƙale da juna, haka zata zo su sha firar su cikin so da a guarding luv ko a motar ta ko kuma anan inda suke sana'ar su, a bayyane suke nuna juna soyayyar ba tare da wani shayi ko shakku ko kuma tsoro ba, inda nan take kowa yasan irin ƙauna da alaƙar dake tsakanin su, da irin tarin soyayyar da suke yiwa juna, da yawa sun taya su murna saboda ganin sun dace da juna, yayin da da yawan su ire iren Amira dake ƙaunar mm sun ji baƙin cikin taren ta su kuma sun nuna jin zafin su a fili tare da nunawa Janan ƙiyayya marar ɓoyuwa, don kuwa da wuya tawuce bata ji ana zaginta da tsincen ta ba akan ta maƙalewa wanda bai dace da rayuwar ta ba don taga yana da kyau, komai dai meye ita ko a jikinta don ba ta damu ba balle ma ta nuna masu tasn suna yi, Amira ma tayi hushin da ita har ta gaji ta dena don taga ba abun da ya rageta dashi sai ma ƙaruwar farinciki da taga tana samu ita da masoyin ta, a zahiri sun koma kamar yanda suke a da amma a ƙasan zuciyarta tana nan ƙullace da ita tare da neman duk wani abu da zai kawo kusanci tsakanin ta da mm yanda zata ƙulla mata makirci da ko yana so ko baya so sai ya rabu da ita, a ɓangaren Ingaski kuwa ko hanya baya fatan ta haɗasa da Janan, a class ma idan ya shiga yi masu lecture baya barin idanuwan sa su haɗu da nata, ita abun har mamaki yake bata, mutumen daya ɗauki alwashi akan yi mata wulaƙanci da tozar ta ta, sai gashi shine ko ido baya son haɗawa da ita, ko me yasa ta tambayi kanta a karo na ba adadi, ɗaya ɓangaren zuciyar ta ne ya bata amsa da cewa ƙarfin addu'ar da takeyi ne, don tun lokacin da abun ya faru tsakanin ta dashi take addu'a ALLAH ka shiga tsakaninsu ya kuma kare ta da dukkanin sharri da mugun nufinsa.