PAGE__28

132 5 1
                                    

_Page 28_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*
______________________________
Ganin yanda nan take hankalin sa ya tashi gaba ɗaya har tsantsar damuwar dake zuciyar sa ta bayyana a kan fuskarsa ya sa Momy ta dafa kafaɗarsa haɗe da juyo da fuskarsa suna kallon juna ta ce,

"My son, kana son yarinyar ne sosai?"

"Upcouse Momy, bazan iya jurar rashin ta ba"

"Shikenan, ka kwantar da hankalin ka kuma kayi ƙoƙarin yin addu'a akoda yaushe kana mai roƙon ALLAH ya za ɓa maka mafi ƙololuwar alkhairi akan ta, ni kuma zan sake wai wayar dangin mahaifin Jabir a karo na biyu a dalilin ka saboda bana son ganinka cikin irin wannan damuwar, wataƙil i zuwa yanzu sun jaye ƙiyayya da kuma tsanar da suke yi mana ni da ɗana"

Da sauri ya riƙo hannayen ta yana kallon cikin ƙwayar idanuwan ta haɗe da cewa,

"Pls don't do that Momy, a tunanina ba yanzu ne lokacin daya kamata kije masu ba, hakan zai iya sake lalata al'amarin gaba ɗaya, musamman idan hasashen da kike yi akansu bai tabbata ba, ma'ana, ina nufin idan har yanzu basu haƙura da abinda ke ransu ba game daku, kiyi haƙuri yau munyi magana da Janan akan za muje gidan grandma ɗin su gobe saboda ta gabatar dani a wajen ta, idan na je zan lura wane irin sauyi aka samu daga wajen ta yanzu, na tabbata a yanda Janan ke bani labarin ta ta daɗe dayin nadama akan abunda ya faru, idan kuma batayi ba zanyi ƙoƙarin shiga jikinta na sauya mata tunani na kuma nuna mata kuskuren abunda suka aikata maku a baya, fatana kawai shine na samu karɓuwa a wajen ta, kinga idan hakan ta faru shikenan zamu jefi tsuntsu biyu da dutsi ɗaya"

Shiru tayi kamar mai wani nazari kafin tace,

"I don't think zaka iya sauya su kamar yanda kake tunani matuƙar har yanzu basuyi nadamar abinda suka aikata ba, hakan kuma ba abu bane mai sauƙi, but zanyi addu'a sosai akan ALLAH ya baka nasara, nima na gaji da rayuwa hakan ba tare da kowa dangi na kona mijina ba, aduk lokacin dana tuna hakan abun yana damuna sosai" ta ƙare zancen kamar za tayi kuka, a hankali mm ya shiga shafa bayan hannuwan ta dake riƙe da nasa alamun rarrashi haɗe da cewa,

"Calm down Momy, by God grace komai zai zo ƙarshe, You see, atimes abubuwa na cakuɗewa mutum waje ɗaya adaidai lokacin daya kusa cimma nasara arayuwar sa, to a wannan lokacin shi kuma sai yayi ƙoƙarin tsanan ta haƙurin sa sosai saboda cimma nasara, yanzu haka jikina na bani cewa lokacin yin farin cikin ku ya kusa bayyana da yardar ALLAH" cike da tausayin halin da suke ciki gaba ɗaya ta ɗora hannunta a gefen fuskar sa tana faɗin,

"How my son? bayan yanzu ne damuwa ke sake ƙoƙarin fuskan to ni saboda halin da yarona zai iya faɗa wa akan soyayyar sa?"

"Kar ki damu da hakan Momy, ai dama farin cikin wasu na wanzuwa ne a yayin da wasu ke cikin baƙin ciki, na tabbata wannan damuwar tawa da sannu zata zomo mana farin ciki da yardar ALLAH, domin alamu sun nuna cewa cike take da abubuwan da zasu zamo silar walwalewar matsalolin mu baki ɗaya" ya ƙare zance yana murmushi tare da ɗora hannunsa akan nata dake kan fuskarsa, jiki a mace ta ce,

"Ina fatar haka my son, amma su ɗin ne suna da matuƙar matsala sosai"

"Momy karki dami, in Sha ALLAH, ALLAH zai shige mana gaba" yana gama zancen ya miƙe ya bar falon shima jikin sa ba ƙwari,

A taƙaice dai dashi har Momy daren basu runtsa ba saboda tunanin me zai iya faruwa aduk lokacin da Abba ya san cewa shima mm ɗin matsayin ɗa yake a wajen ta, ganin ba suda wata mafita banda addu'a yasa kowanen su ɗauro arwala suka shiga faɗawa ALLAH dukkanin damuwowin su da buƙatocin su saboda shi kaɗai ne zai iya yi masu maganin su, washe gari misalin ƙarfe goma da rabi mm na bacci Janan ta kirawo wayar sa, miƙa hannunsa yayi ya lalubo wayar haɗe da ɗaga kiran ya aza akunnen sa yana cewa,

"Hello janany tawan" cikin muryar bacci yake maganar duk da bai kalli wanda ya kira wayar ba amma ya gane cewa ita ce saboda ringing ɗin daya saka mata daban yake dana kowa, murmushi tayi da har sai da ya jiyo fitar sautin sa a kunnuwan sa sannan ta ce,

"Barka da hutawa yallaɓai, kar dai ace har yanzu baka tashi bacci ba?"

"Kamar kin sani, amma dai gashi kin tadani yanzu, ya kike?"

"Lafiya klw, ai mun abufuwa in tuba, ko da yake alamu sun nuna cewa ka daɗe baka kwanta ba jiya shiya saka kaiwa wannan lokaci baka tashi ba, saboda haka na ƙalubalance ka akan haka, me yasa?"

"Tunanin ki mana ranki shi daɗe, ke san ke ce duniya ta, shiyasa matuƙar tunanin ki bai barni runtsawa ba to fa ban isa nayi hakan ba"

Duk wannan wayar da suke yi tana kan shirin ta na zuwa makaranta ne wanda daga nan take so su haɗu a can gidan grand ma dashi, kallon kanta tayi ta madubi don shigar yau da tayi ta musamman ce wa masoyinta shi kaɗai, man baki dake ajiye akan madubin ta ɗauka ta muttsiƙawa bakin ta tare da rolling idanuwanta ganin yanda tayi kyau gwanin burgewa, murmushi ta saki jin abunda ya faɗa, cikin shagwaɓe murya ta ce,

"Kai hubbin ruh, kada ka fasa mun kai da yawa fa!, ni Janan ni nafi cancanta dana kira ka duniya ta domin babu wanda nake gani sai kai, haka kuma kullum wayewar safiya tunanin ka shike zamowa annurin dake haska duniya ta"

"Hmmm! Naki kika sani yarinya, bari rai da lafiya suyi mana faɗa sannan mu jira yi zuwan lokaci, a sannan ne zaki tabbata kuma ki faɗa da bakin ki cewa tabbas ke ɗin nan ke ce duniya ta saboda yanda zan mallaka maki duka ragamar rayuwata, Janan yanda nake jin soyayyarki araina zan yarda na rasa komai a duniyata in dai zan same ki, Ni Muhammad Muhriz ina matuƙar sonki sosai" lumshe idanu tayi cike dajin daɗin kalaman sa ta ɗauki jikkarta ta rataya tare da saka takalman ta masu ɗan tudu sannan tace,

"Ya Muhriz, nima ina son ka irin son da nake da tabbacin babu wata macce aduniya da zata taɓa iya yima wani namiji shi, haƙiƙa ni ɗin mai sa a ce aduniya dana sameka matsayin masoyin raina, haka kuma ina godeya ga ALLAH daya zaɓa mun kai acikin jerin maza je, wanda na tabbata hakan ba iyawa ta bace ba kuma cancanta ta bace, bisa haka nake roƙon ALLAH daya ci gaba da bani tsaro da kariya acikin burnin zuciyar ka ni kaɗai domin na samu damar yi masa cikakkiyar godiya da ni'imar daya yi mani ta samun ka"

"Janan kenan, ai kisa aranki Ubangiji ya riga daya amsa addu'ar ki da daɗewa, domin gaba ɗaya gangar jiki, ruhi da kuma zuciya sun gama shaida cewa ke ce ta farko kuma ke ce ta ƙarshe azuciya ta, ni ɗin naki ne ke kaɗai bada kowa ba, sannan zaki ci gaba da kasancewa aburnin zuciya ta ba tare da kin samu karɓar baƙuncin kowace irin halitta ba har abadan abada"

"Madallah da wannan kyakkyawar safiya mai cike da kyakkyawan albishir daga bakin masoyin daya zamo mamallakin wacce ke sauraron sa, kunnuwa sun gaskata zancenka haka kuma zuciya ta yarda da kalaman ka, shi yasa baki yanke shawarar yin godiya agare ka bisa wannan karamci da halacci da kayi mun , ina roƙon aminci da yardar ubangiji su lulluɓe dukkanin rayuwar ka da kuma tawan ya kai sadaukin zuciyata, amma kafin muci gaba da magana zan so ka taimaka mun ka tashi baccin nan haka yallaɓai, ko ka manta ne da inda zamu je?"

"Ko ɗaya ban manta ba, domin na fiki buƙatar ganin mun isa wajen, sanin da nayi cewa sai kin taso daga makaranta za muje shiyasa baki ji nayi zancen ba, amma bara na tashi yan zun nan na watsa ruwa sannan sai na gyara, zuwa ƙarfe nawa kike sa ran zaki gama lectures ɗin yau?"

"Ƙarfe biyu daidai, badon nasan mun fara haɗa C.A ba ma da babu inda zan je sai dai nazo na ɗauko mijina"

"To ayi haƙuri dai aje tunda an riga an san da hakan, ina son matata tafito da first class ta yanda itama zata karantar da wasu kamar yanda aka karantar da ita" Dariya tayi tare da rufo ƙofar ɗakin ta sannan ta nufo upstairs ɗin.

A hankali take saukowa daga kan upstairs ɗin tana sauraren muryar sa har ta ƙaraso ƙasa, ɗagawa Madam florence kai tayi tana mai faɗaɗa murmushin dake kwance akan fuskarta tare da nufar ƙofar fita tana ɗaga mata hannu, Nihal kuwa dama tuni sun yi breakfast ɗin su da ita tun safe, shiyasa bata tsaya bi takan ta ba ta wuce abunta, wayar ta na a kunnen ta har ta kai bakin motar suna ta ɗanɗasa soyayyar su hankali kwance, tana saka makullin ajikin motar taji muryar mahaifin ta daga can jikin window ɗin ɗakin sa dake sama na faɗin,

"Dakata anan ban amince kifita ba!" cike da mamaki ta ɗago kai tana kallonsa kafin ta ɗan ja baya daga jikin motar tana cewa mm dake kan waya,

#COMMENT PLS.

*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now