PAGE__41

123 5 0
                                    

_Page 41_

*TUKUICIN SO💞*

*NA*

*BILLY S FARI💎*

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*
______________________________
Wata irin muguwar faɗuwa gabanta ya sakeyi lokacin da suka haɗa idanuwa da Jabir dake ƙoƙarin ƙarasuwa daga ciki, tsaye yayi cak yana ƙare mata kallo, tabbas itace, matar da har ya mutu baya mance wulaƙancin da akayi masu sanadiyar zuwa gidan ta, duk da alokacin bai fi shekaru goma sha huɗu ba aduniya ba, zai iya tuna yanda komai ya faru a wannan ranar, bai sake gasgata ita ɗin ce ba sai da yaga tanufato wajensa jikin ta na rawa, magana take son yi amma ta kasa cewa uffan sai hawaye dake silalo a fuska, duk da baya da hasken fata irin ta mahaifinsa kuma bai ɗauko kamar shi sak ba, ta tabbatarwa kanta cewa wannan jininta ne saboda abubuwa guda uku, muryarsa, yanayin tsayuwarsa da kuma satar kamannin mahaifinsa da yakeyi, a hankali Jabir ya fara ƙoƙarin ja da baya ita kuma tana matso shi,

"Jabir wai meye haka?" Mm ya faɗa tare da ƙoƙarin matsowa kusa dashi, fashewa da kuka grandma tayi haɗe da cewa,

"Tabbas shi ne, Jabir ne jika na ɗan ɗan Jamal" wani irin mugun kallo Jabir ya watsa mata tare da juyawa zai bar falon tayi saurin kamo hannun sa,

"Don ALLAH kada katafi Jabir, ina mahaifiyar ka?, Na roƙeka kadawo nayi nadamar abunda aka aikata maku"

Fizge hannunsa yayi tare da juyowa yana kallonta da idanuwansa da sukayi jajir, ya ce

"Na dawo?, Wai acikin gidannan ake roƙon nadawo na zauna, ban san ko waye keba ban kuma san wace alaƙa ce tsakanin mahaifiyata daku ba, kamar hakane a waccan ranar mahaifiyata tadinga roƙonku kina kallo aka wulaƙantata aka koreta, ko sau ɗaya kinyi tunanin tsaida mu ko dakatar da wanda ya koremu, ko kuma hanamu tafiya? Bakiyi ba, don me yanzu zaki dakatar dani kuma har kiyi tunanin zan tsaya?, Wlh da nasan wannan gidan ne Muhriz zai kawo ni da ban yarda nazo ba, don tun a waccan ranar na kashe gidannan da duk wanda ke cikin sa acikin rayuwata"

"Kada kayi haka Jabir, kai jikan ne kuma ina tsananin ƙaunar ka, waccan ranar fin ƙarfi a akayi amma duk tsawon shekarun nan zuciyata bata taɓa hutawa daidai da rana ɗaya ba akan tunanin ka da mahaifiyarka, nayi kukan safe nayi na rana nayi na dare duka akan nadamar abubuwan da akayi maku, na nemeku a inda nayi tsammanin samun ku amma hakan ya gagara, don ALLAH kasamaman gurbin komai ƙanƙantar sa azuciyarka da zaka ji tausayi na kayafe mun"

"Idan har ni jinin ki ne to tabbas bazaki taɓa samun wannan gurbinba a zuciyata, saboda jininki basada imani ko tausayin iya yafe kuskure komai ƙanƙantar sa, na tabbatar da haka ne a waccan ranar da aka wofantar dani da mahaifiyata a gabanki ba tare da ke ko shi wanda ya aikata kunji tausayin mu ba" yana gama faɗa haka yafice daga falon yana jin ɗari da ɓaƙin cikin takowa gidan da yayi alƙawarin bashi baya har duniya ta naɗe, da sauri mm ya biyo bayansa yana faɗin,

"Haba Jabir, meye haka ka aikata, ALLAH ma fa munayiwa kuskure ya yafe balle ɗan adam, sannan a waccan ranar da kake magana bafa ita ta aikata laifin ba"

Cikin ɓaci rai ya juyo yana kallonsa da rinannin idanuwansa kafin yace,

"A'ina aka aikata laifin?, da sanin ta ko bada sanin taɓa?, Shin tanada ikon hanawa ko batada?, A gaban idanuwanta ne ko ba agaban idanuwanta ba?"

"Jabir..."

"Look kaje idan kasamo amsar tambayoyin dana yi maka sai kazo kayi ƙoƙarin tabbatar mun da cewa batada laifin kamar yanda kake iƙirari yanzu, kuma wlh da nasan Janan nada alaƙa da waɗan nan mutanen da ban taɓa bari ka faɗa soyayya da ita ba, don basu san meye so ba? Kuma basu san darajar sa ba" yana gama faɗar haka ya juya yabar gidan ba tare daya koma saurarar mm daketa faman kiransa ba,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now