PAGE__16

164 8 0
                                    

_Page 16_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*

INA KUKE MAKARANTA??

INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️

TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B

INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.

DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA

(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_

👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
______________________________
Kusan mintuna biyar suka shuɗe a haka Razina bata ce komai ba shima yaya mm baibi takan taba yana ta latsar wayar sa, ganin tabbas baza tace komai ba gashi yana so ya tashi yasa ya ƙarasa shanye juice ɗin dake hannunsa haɗe da miƙa mata cup ɗin yana ƙoƙarin miƙewa da sauri ta ce,

"Amm...yaya magana nake son yi da kai fa" har tana miƙa hannu alamun tsaida sa, yana juyowa tayi saurin sadda kanta ƙasa cike da jin kunyar abun da take son faɗa masa,

"Emhim..ke nake sauraro Razina, akwai wata matsala ce a school?" Ta girgiza masa kai alamun babu,

"To meye? Faɗa mun mana ko kina da wani wanda ya fini banda Momy da zaki faɗa wa matsalar ki?" Nan ma sake girgiza masa kai tayi tana ɗan jan yatsun hannayen ta tamkar zata fizgesu, dariya ya yi tare dasa hannun sa ya janye hannunta da take faman jan yatsun ɗayan hannun dashi ya ce,

"Kinga, barsu haka kada ki tsinkasu Razina, ai dai iya wahl kin basu ko so kike ki ragewa kanki sadaki garin jin kunyar abunda kike son faɗa?, Idan baza ki iya ba shikenan tashi ki shiga gida, idan na dawo Sallah ko zuwa anjima ne nayi waya"

"A'a yaya, zan iya"

"To ina ji"

"Dama ni da yaya Jabir ne.." sai kuma ta kasa ƙarasawa,

"Ke da yaya Jabir ne kuka yi me?"

"Ya ce yana so..." Kafin ta ƙarasa sai ga Jibir ya shigo, idanuwansa kar a kanta har ya ƙaraso wajen, kamar da gaske ya ɗan rissina cikin girmamawa yana kallon mm daya juyo yana kallonsa ya ce,

"Yaya ina wuni? barka da mare ce" wata irin kunya ce ta sake rufe Razina da sauri ta miƙe ranta tana faɗin shikenan ya gama tona mata asiri tun kafin ta faɗa da kanta, har wani hahharɗewa ƙafafuwan ta keyi tsabar yanda Jabir ya ƙura mata idanuwa har ta shige, shi kuwa mm mazewa ya yi duk da irin daɗin da ya jiya a ransa haɗe da cewa,

"Mtssss, an dai yi abun kunya aboki ya koma yaya" tintsirewa da dariya Jabir ya yi haɗe da haye kujerar da Razina ta tashi yana faɗin,

"Na dai ji, so ne ya jamun, alƙur'an ma in baba kake so na kiraka zan kiraka, roƙona dai kasa mani hannu kuma ka buga stamp, da kayi hakan shikenan ka biya ni yayan mu"

"Wai da gaske kakeyi Jabir?, Razina fa ƙanwar kace kuma a nawa tunani tayi maka ƙaramar"

"Eh, ƙara dai da kace a naka tunani, ALLAH yasa yau aka haifi Razina a haka nake son abuta, in kuma buƙulu zaka yimun sai na canja wajen neman auren na koma wurin Momy"

"Ahh...kawai nasan dai kafi son irin riɗa-riɗan matan nan ne, Razina kuma sai naga kamar tayi ma ƙanƙanta"

"To ɗan baƙin ciki Renon ta zanyi, ina shikenan ko?" Jabir ya faɗa cikin 'yar ƙwagewa tare da ɗaukar gorar ruwan dake wajen ajiye ya tsiyaya a cup ɗin da ya gani yana sha, dariya mm ya yi da sai da duka haƙoran sa suka bayyana haɗe da cewa,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now