_Page 45_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
Bayan sun kammala Sallah mutane duk sun gama fita dattijon ya juyo ya hango mm zaune ya ɗaya hannayensa yana addu'a hawaye na saukar masa a fuska, da alama sai a sahu na ukku ya samu yin sallahr, ɗan tsagaitawa ya yi har saida ya gama addu'ar sannan ya miƙe tsaye haɗe da jawo sandar sa ya nufo inda yake, miƙewa tsaye yayi shima yana ƙarasowa ya miƙa masa hannu sukayi musabiha sannan ya gaishesa cikin girmamawa,
Hannunsa dattijon ya ja suka fita cikin masallacin zuwa gidan sa ya ƙwalawa ƴar autarsa Maryama kira ya ce ta kawo masu tabarma da ruwan sha anan soro anyi baƙo,
Bayan sun zauna ya bari har sai daya sha ruwa ya sauke ƴar ajiyar zuciyar gajiya dake tattare dashi sannan ya dubesa haɗe cewa,
"Bawan ALLAH ka ce daga katsina kake amma kuma baka yi mani bayanin ko kai waye ba da kuma abun daya kawo ka?"
"Haka ne baffa" ya faɗa tare da lanƙwashe ƙafafuwan sa yana fuskantar dattijon fuska da fuska tamkar mai shirin ɗaukar karatu sannan ya ci gaba da cewa,
"Da farko dai sunana Muhammad Muhriz, mahaifina kuma ana kiransa da malam Muhammad, manomine a wannan garin kuma yana sana'ar saida dabino da ashuwaki, na zo wannan garin ne neman dangin iyayena bayan kuɓutar da nayi a shekaru goma sha takwas da suka wuce sanadiyar shigowar da ɓarayi sukayi a wannan ƙauye suka kashemun mahaifi da mahaifiyata, guduwar da nayi ta ceton raina dana ƙanwata mai suna Razina har wani bawan ALLAH ya taimake mu shine silar zamana Katsina, kuma shine dalilin daya sa na ce maka daga katsina nake" tun kafin ya rufe baki dattijon da hawaye suka cikawa idanuwa ya shiga ƙwalawa mutanen dake cikin gidan kira, "indo, Atika, Talatu Mariya...kuzo kuga abunda nake faɗa maku koda yaushe, kuzo ga jinin ɗan uwana Muhammadu ya dawo gareni, kuzo ku gasgata mafarkin da ako yaushe nake faɗa maku inayi, ALLAH akbar ALLAH kai ne mai iko, kuma kai ne mai yin yanda ka so aduk lokacin da kake so" ya ƙare zancen yana kuka haɗe dayin sujudush shukar, mm kuwa a hankali ya runtse idanuwa wasu hawayen farinciki na saukar masa, tabbas yayi kuskuren rashin neman dangin iyayensa tuntuni, da wataƙil izuwa yanzu farincikinsa ya lunku fiye da yanda yake ji,
Dattijon kuwa yana ɗagowa daga sujada mm yaji ya rungumo sa ajikin sa yana faɗin,
"Taya akayi ka manta baffan ka haka Muhammad, taya ka kasa tunowa dani bacin kullum tare kake da mahaifin ka shi kuma tare yake dani" hannaye mm yasa shima ya rungume sa haɗe da cewa,
"Kayi haƙuri baffa Ali, kallo ɗaya nayi maka na tuna zuwan da mukeyi a wajenka ni da mahaifina, wayon riƙe ko wane irin matsayi ne kake dashi awajensa kawai na kasa tunowa"
"Za kace haka tunda kana can cikin birni hankali kwance, tashin hankalin daka barmu aciki kuwa ya kasa sa ka iya waiwayo mu"
"Ba haka bane Abba, tunanina ne bai kawo hakan ba sai yanzu, amma daidai da rana ɗaya ƙauyen nan da duk mutanen dake cikinsa basu taɓa fita a raina ba saboda nasan duka ƴan uwana ne"
"Haka ne, ALLAH yayi maka albarka, to ina ƴar uwar taka take ne?"
"Bari nayi har sai na fara zuwa na gano ƴan uwanmu tukuna daga baya sai na kawota ita"
Ɗago kai Baffa Ali yayi yana kallon ƴan uwan nasa mata dake tsaitsaye fuskokin su ɗauke da farinciki, ya ce
"Indo kinga abunda nake faɗa maki ko?, jikina na bani cewa duk inda jinin ɗan uwana Muhammadu suke suna raye da yardar ALLAH, to gashi ALLAH ya bayyana mani akan da kansa" wacce ya kira da indo na matsar ƙwalla, ta ce
"Na gani malam, ALLAH gagara misali ne huwar Rahmanu a lamurransa" mm ya ɗan rissinar da kai ƙasa ya shiga gaishesu ɗaya bayan ɗaya, murmushi indo tayi bayan sun amsa tare da matsowa ta shafa kansa tana cewa, "ALLAH mai iko sannu Muhammadu yanzu kai ne ka girma ka koma haka?" Daga shi har baffan murmushi sukayi kafin Baffa Alin ya sake juyawa gefen da sauran matan ke tsaye sun zubowa mm idanuwa suna kallon ikon ALLAH daya sake maido masu da ɗan-ɗan ɗan uwansu , ya ce