_Page 11_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_
👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730______________________________
*K* oda ya shigo sashen nasu kwance ya tadda mm a nan falo saman doguwar kujera yayi rigingine fuskarsa na kallon rufin saman falon ya ɗora hannayen sa akan ƙirji idanuwan sa a rufe, a zahiri za kace bacci yakeyi amma kuma idanuwansa biyu, zallar soyayya ce ta sashi faɗa wa duniyar tunanin da bai ma san da shigowar Jabir ba, kallo ɗaya Jabir yayi masa ya ɗauke kai tare da shigewa uwar ɗakin ya faɗa a kan makeken gadon dake tsakiyar ɗakin tare dayin wata irin ajiyar zuciya shima yana ƙoƙarin afkawa duniyar tunanin ta shi masoyiyar,
Ganin haka ya sashi miƙewa ya ciro wayar sa dake jone tana caji haɗe da kamo jerin lambobin dake cikin wayar sa ya dannawa lambar da aka rubuta wa *Sister Razy* kira, kasancewar har ta fara bacci yasa har kiran ya taimake bata ji ba har sai da ya sake kira a karo na biyu sannan ta miƙa hannun ta ta jawo wayar ta saka a kunne ba tare data tsaya duba ko waye ba har lokacin idanuwan ta na a rufe, cikin muryar bacci ta ce,
"Hel..lo, assalamu alaikum"
"Wa'alaikissalam, ba dai har kin fara bacci ba?"
"Eh Ya Jabir, ai na faɗa maka bacci nake ji sosai"
"Assignment ɗin da?"
"Zan yi koda da asuba ne"
"Noo..tashi kije ki wanke fuskarki kizo muyi kin ji ko"
"Pls..Yaya .."
"Ya isa haka, je ki wanke fuskar ki nace muyi bana son gardama."
Babu yan da ta iya dole ta tashi ta je toilet tana faman turo baki ta wanko fuskarta, har lokacin yana kan layi ba tare daya tsinke ba, murmushi yayi kamar yasan tutar baki take yi haɗe da cewa,
"ALLAH ya baki haƙuri, duk wannan dai bazai sa na fasa abinda nayi niya ba, hop kin wanko fuskar?"
A shagwaɓe ta amsa masa da eh tare da jawo jikkar tata ta makaranta ta fiddo littafin,
"Hello.."
"Ina jinki Mrs j" wani irin dimmm.. ta ji jin abunda ya faɗa haɗe da buɗe idanuwanta ta wartsake daga baccin ba tare da ta sani ba,
"Mrs j?" ta nanata a zuciyar ta kafin ta saki murmushi haɗe da basarwa ta ce,
"Ya Jabir gashi na ɗauki"
"Ok faɗomun question ɗin farko?"
"Write a Java program that execute 2 binary number.."
"Ok ciro biron ki da takarda"
"Wai yaya a waya zamuyi assignment ɗin? Kodai nayo maka snap ɗin assignment ɗin na turo maka?, ko kuma na turo maka ta watsApp?"
"Ban faɗa ba, hakan dai nake so nayi ta jin muryar 'yar ƙanwata ko kuwa?" Sake sakin wani murmushin tayi da har sai da ya jiyo sautin sa sannan ta ce,