_Page 19_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1237455446?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=PYGQ%2BdOO8e%2BCwsNwn9fb5e1%2BzLxKjUxQ96n8c%2FLnmLxdmMcOcGqbBGiAMZKGkI91RPQWQMCjqhSn7rSSvPO8Db%2BTYr74tNLrPYhmznvY9Z1ZkJLEu5JQu27aPuIJ7ZQs_
*KIN SAYI SHIRINMU NA TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B?, IDAN BAKI SAYA BA MAZA KI HANZARTA KI MALLAKI NAKI TA HANYAR WUƊANNAN LAMBOBIN DOMIN SAMUN ƘARIN BAYANI
+447894142004, 07065283730, LITTAFAI BAKWAI DA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU MASU MATUƘAR ƘAYATARWA AKAN NAIRA DUBU ƊAYA (1000) KACAL, ƳAR UWA GWADA KI GANI IDAN KINA CIKIN WUƊAN DA SUKAYI RASHIN BATCH A ƊIN MU, NA TABBATA BAZA KIYI NADAMA BA😍*
______________________________
Cike da farin ciki ta ƙarasa gida, yau ma sai da ta fara biyawa party ɗin Hajiya zee tayi mata ya jiki suka taɓa 'yar fira wacce hakan ba ƙaramin farin ciki ya saka Hajiya zee tayi ta saka mata albarka sannan ta wuce party ɗin su, tana shiga ta tadda madame florence a kitchen ita da Nihal suna girka abun da za a ci da daddaren,"Wow! Adda Nihal kice kinji sauƙi" Janan ta faɗa tana yiwa Nihal wani kallo mai cike da burgewa saboda yanda taga tayi kyau, support wears ne a jikin ta pink colour and white, wanda da riga masu dogon hannu sai p-cap data saka, tasowar ta kenan tana tambayar Madam florence ko Janan ɗin ta dawo, shine fa ta shiga tana ɗan rirriƙa mata aikin sai gata ta dawo, murmushi kawai Nihal tayi ba tare data juyo ba don fushi takeyi da ita, haka yasa Janan lallaɓowa ta bayanta ta rungumeta haɗe da ɗora kanta saman bayanta,
"So much missed you Adda Nihal, pls kada kiyi fushi da Janany sister ɗin ki bazata jura ba?" ta ƙare zancen tare da saƙalo hannayenta a wuyanta ta turo fuskarta tana kallonta, ɗan juyo da fuska Nihal tayi itama har suna shaƙar numfashi juna haɗe da cewa,
"Ba wani can, ni cikani tunda kin manta dani"
"Laaa..inji waye? Ai in zan manta ki Adda zan manta da kai na, kawai wani abun ne mai matuƙar muhimmanci a school ya sakani zama busy, but i'm sorry pls..."
Ta faɗa haɗe da sakinta ta haye cabinet ɗin dake cikin kitchen ɗin tana gaida Madam florence dake faman kallon damar su tana murmushi, hannu ta saka ta ɗauki samosa ƙwaya ɗaya da take soyawa ta saka a baki tana ci tare da kallon Nihal dake faɗar,
"Ehmm!, Janany sister ashe har akwai abunda ya fini muhimmanci a school ɗin taku!" Ta ƙare zancen tana wanke hannayenta a jikin fanfon dake cikin kitchen ɗin haɗe da jawo ƙaramin towel dake sagale ta goge tana ƙoƙarin ficewa, don dama ita ke naɗawa Madam florence samosa ɗin,
Saukowa Janan tayi daga kan cabinet ɗin ta ɗauki wata samosar ƙwaya ɗaya tabi bayanta tana faɗin,
"No Adda Nihal ba haka bane, kawai dai abun nada muhimmanci ne shiyasa ma kika ga nakai wannan lokacin ban dawo ba, ya ƙarfin jikin naki?"
"Am just little fine dear, ya karatun?"
"Alhamdulillah Adda ALLAH ya ƙara sauƙi"
"Amin ya rabbi"
"Adda gaskiya wannan yayan nawa da zan ganesa yanzu saina makashi a kotu kafin ayi komai na wahalarmun da yaya da ya yi"
Murmushi Nihal tayi suna yi suna taka matattakalar hawa saman zuwa ɗakunan su haɗe da cewa,
"U'uhm Janany Sister, kibar nono yayi bacci, ai ba dukan ruwa zan sha ba ko dukan 'yan sanda zan sha saboda shi bazai yuyu a ma kashi kotu ba, wanda kuma yayi hakan ko waye zamuyi baraa'a dashi, ko kuwa dai kin manta da irin girman soyayyar da nakeyi masa ne shi yasa kika daɗi hakan"