_Page 8_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9https://www.wattpad.com/1232233680?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=UZ6w6%2B3P4SM9m%2B8oYMWOxC2OyAGths4uDQxLM3q6nPRYMbCLxiH1RNJcVgzJpQYUxW%2B5O%2BxuVk%2FFa7s%2Fxg8lt6kLSy9JyW7RbiViaLpuS7WywxghkDQgIFmxcG58ppYg_
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN
👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
---777778
______________________________"A'a 'yan mata, ai ba'ayi hakan ba tunda karo ne kukayi da juna, abunda kawai zan iya cewa shine kiyi haƙuri bisa zubewar da kayanki sukayi amma ba sai an kai ga duka ba" ya ƙare maganar tare da sakin hannun nata sannan ya ja Razina dake watsa mata wani irin mugun kallo cike da tsana ya maida gefensa, itama Momy haƙuri ta shiga bawa Nihal ganin yanda ranta ya ɓaci sosai, ga mamakin ta sai taga Nihal data kafe mm da idanuwa tana kallo tayi murmushi haɗe da cewa "ba komai mama" har lokacin idanuwanta na akansa har da wani kar kace kai tana ƙare masa kallo
Mm kuwa da bai masan abunda take yi ba duƙawa yayi da kansa ya kwashe mata duka kayan ya mayar mata a ledar da suke ciki sannan ya miƙa tsaye ya miƙa mata haɗe da kallon Razina ya ce,
"Kibata haƙuri"
Sai da Razina ta fara cuno baki kafin can ciki-ciki tace wa Nihal,
"Kiyi haƙuri"
Nihal da har lokacin idanuwan ta na akan mm ta d'agawa Razina hannu kawai haɗe da karɓar ledar da yake miƙo mata ta ce "Na gode" fuskarta a sake ɗauke da murmushi.
Murmushin shima yayi mata haɗe da jan hannun Razina suka ƙarasa shigewa daga ciki tana faman gunguni ita ala tilas taji haushi, a zahiri kuwa cewa takeyi, "ALLAH shiyasa bana son fita dakai ya Muhriz, da ya Jabir ne da yanzu ya koyawa matar can hankali musamman idan ta sake ta mare ni, kiji fa Momy ai gaba ɗaya mukayi karo da juna amma shine zata wani d'aga hannu tace zata maran"
"To ai dai bata mare kin ba tun da ALLAH ya taimakeki kyakkyawan yaron nan nawa ya tafi da hankalinta, badon hakan ba yau da sai dai a baki haƙuri a maimakon haƙurin da ke kika bata"
Sake cuno baki tayi cike da jin haushi abunda Momyn ta faɗa,
"Ai dama nasan haka zaki faɗa Momy, amma bari nakoma gida saina faɗawa ya Jabir, yanda gobe bazai bari muzo mu kaɗai ba idan zamu fita, don na gano indai yana tare damu shike maganin duk ire-iren wannan iskancin da yarinyar nan ta nemi yimana"
"Yi maki sai malama, kuma bari kiji dake har yayan naki sai kun sha duka wata rana garin wannan tsiwa da rashin jin naku, in banda abunki meye na jinini dakai ƙara tunda gashi cikin sauƙi an magance komai, koda yake dake har yayan naki duk halinku ɗaya, ALLAH kasa kada ku janyo mana duka wata rana" mm ya fad'a haɗe dayin gaba don ya fara gajiya da shegen jinini irin nata,
Dariya Momy ta saka haɗe da cewa,
"To kin ji dai, don ALLAH don Annabi kurufa mana asiri kar kusa da tsufana naci duka ba gaira ba dalili"
Dariya itama Razina tayi haɗe da rungumota ajiki ta ɗora kanta saman kafad'arta tana fad'in,
"Wa mutun inji mutuwa, ai babu wanda ya isa ya taɓa mana Momy da sunan duka bai kwana prizin ba, sha kuruminki ina gama karatun nan soja zan je, kinga kuwa taɓa uwar soja ba qaramin tashin hankali bane aka taddo"
Da wannan surutun nata har mm yaje ya fara d'aukar wasu abubuwan da yasan suna buƙata na rayuwar yau da kullum, koda suka ƙaraso har ya kusa gamawa sai kawai suka ƙarasa ɗaukar sauran suka saka ya kai inda ake biya aka yimasa bil ɗin kuɗin ya biya sannan aka saka masu a ledoji ya d'auka suka nufi wajen motar su, kai tsaye gida suka nufa don dama wannan sayayyar kaɗai ce ta fiddosu, itama babu yanda baiyi dasu su bari idan anyi sallar isha'i ya huta tunda dawowarsu kenan daga wajen tallar dabinon amma Razina taƙi ta aza rigima ita lallai sai dai yanzu zuwa bayan isha'i bacci za tayi, wannan dalilin yasa bayan ya gama sallar magrib tunda Momy tasa baki ya gyara ya ɗ'aukosu suka zo wajen sayayyar, Jabir kuwa dama cewa yayi babu inda zai je don ya gaji da yawa sosai, ashe rabon haɗuwar su da Nihal ne ya jawo hakan, don kuwa gaba ɗaya ganin mm yasa Nihal duk tabi ta susuce, tuƙin kawai takeyi amma babu wani ƙwari a jikinta har ta isa gida, ba abunda take tunan in banda fuskar mutumen da bata san ko waye shi ba, sunansa da kuma inda ya fito duka bata sani ba, amma ya bala'in shiga ranta fiye da tunani, kyansa, surarsa da kuma yanayin halittar sa sak irin ta mijin da ta daɗe tana yiwa kanta mafarki ne, murmushi tayi lokacin data ƙarasa shigowa cikin ɗakinta ta zauna bakin gado tana kallon hannunta daya riƙe, a hankali tayi kissing hannun haɗe da cewa,
"Mr.man!, son ka ya shigeni ba tare da nasan kai ko waye ba, amma jikina na faɗamun kai ɗin kana da duk wani abu da nake buƙata awajen ɗa namiji, kyau, arziqi, wayewa da kuma kyakkyawar sura, saboda haka zan nemoka aduk inda kake tunda son ka ya riga daya taɓani ya kuma shiga zuciyata yayi ginin da hannu bazai taɓa iya tureshi ba"
Ta bayanta Janan data shigo ɗakin tun d'azu ba tare data lura ba taje ta rungumota had'e da turo kanta ta gefen wuyanta tana dariya ta ce,
"Who's this lucky man da yayi wuff da zuciyar addatah daga fita har ya soma sakata sabbatu haka?"
Dariya Nihal tayi tare da juyawa ta gyara zamanta akan gadon daidai tana kallon Janan data dawo gabanta itama ta zauna ta tanƙwashe ƙafafuwa tana kallonta kamar mai shirin ɗaukar karatu ko cin abinci tace,
"He's quit handsome, very wealthy and classy, kallo ɗaya zakiyi masa kisan cewa shi ɗin cikakken namiji ne abun son kowace macce, to be Frank sister I'm in luv with him"
Dariya Janan ta kwashe da ita har tana tuntsirawa kan gadon jin yanda auntyn tata ke expressing irin haɗuwar wannan mutumen tare da fallashe sirrin zuciyarta wa ita, sai kace ba Nihal ɗin data sani ba mai yaƙuna samari da wulaƙanci, ciki kuwa hadda wuɗanda keda tarin dukiya saboda ɗai basu cika qualities ɗin da take son namiji dasu ba,
Ganin haka yasa Nihal jin haushi tare da janyo pillow tayo kanta, da sauri ta miƙe tana ci gaba da dariya ta bita suka fara zagayen ɗakin da gudu tana son maka mata shi....
_Hmmm tirƙashi, ƙara-ƙara-ƙaƙa, yanzu fa za'a soma littafin, ga dai Janan masoyiyar Muhriz wacce ga alama itama ta fara sonsa, ga kuma Amira ƙawarta dake masifar sonsa, sannan ga Nihal yayar Janan itama ta ɓullo da tata salon soyayyar agaresa, shin ko waye a cikinsu zata lashe kambun TUKUICIN SO daga wajensa?, Ku biyo ni sannu a hankali domin samun amsarku ta hanyar zafafan #comment #like #share da kuma #voting, it's just the beginning 😁💃💃_
*ALLAH KAJIƘAN IYAYENMU 👏😭*