PAGE__46

143 8 1
                                    

_Page 44_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎
  
TUKUICIN SO FAN'S GROUP, JOIN 👉 https://chat.whatsapp.com/EhMxwW8ey2qJHGxCgbU41L FOR COMMENT.
_____________________________
    Kwana ɗaya mm ya so yi a ƙauyen nasu amma ganin yanda abubuwan suka kasance ya sa yaƙara kwana ɗaya, acikin kwanaki biyun kuwa yaga soyayya da gata awajen dangin iyayensa, lungu da saƙo wajen ƴan uwa duka sai da Baffa Ali ya kaisa aka gaggaisa, ya kuma yi masa bayanin matsayin kowanensu a wajensa, tsabar farinciki mm har kuka yayi, sai yanzu ya tabbatar da babu abunda yakai dangi daɗi aduniya, duk da irin rayuwar da sukayi da babu abunda ya nema ya rasa sai yake ganin sait yanzu ne jin daɗin sa da kuma farincikin sa suka kammala, bai baro ƙauyen ba sai daya samu wani waje da ake cirar kuɗi p.o.s ya ciri kuɗi masu yawa ya bawa Baffa don ya rage lalurorin nauyin mutanen dake kansa, ya kuma bi sauran dangi ya rarraba masu dubu biyar biyar wai kuma goma goma ya ce suƙara suyi hidimar gida kafin ya sake dawowa, Sosai Baffa ya so bin sa don yagano inda suke, saboda tsoron kar su sake kucce masu amma sai mm ya ce yayi haƙuri in sha ALLAH bada jimawa ba zai sake dawowa shi da ƙanwar sa, saboda a ganin sa bai kamata yatafi yabar garin ba tunda kusan shi kaɗai ne namiji jigo da ahalin ke kallo dake taimakon su,

Haka Baffa ya haƙura yana ji yana gani mm ya kama hanya ya tafi bayan sun cikashi da abun arziƙi sun ce ya kaiwa Momy,

Ba ƙaramin daɗi Momy da Razina suka ji ba dawowar mm musamman labarin daya je masu dashi na cewa ashe mahaifiyarsu na raye bata mutu ba, duk data wata fuskar gaba ɗaya jikinsu saida yayi sanyi jin labarin halin da take ciki lokacin data ɓata da rashin takamammen wurin da za a sameta, kuka Razina ta fashe dashi tare da faɗawa jikin Momy tana faɗin, "Momy i want see even once in my life" Momy ta shiga bubbuga bayanta alamun rarrashi haɗe da cewa,

"Sorry my dota, very soo we will all see her since she was alive"

"Momy not sure"

"But we prayed so" ta bawa mm amsa tana ƙoƙarin calming nasu, ajiyar zuciya Jabir dake zaune gefe ya ƙurawa ɗan uwan nasa idanuwa ganin halin da yake ciki yayi kafin yace,

"I think wannan ba wata doguwar damuwa bace, kawai abunda ya kamata muyi shine mu samu hotunan umma mukai gidan talabijin da jaridu, sannan mubada sanarwa gidajen rediyo, ina hakan shine hanya mafi sauƙi da zamu fara nemanta"

"Haka ne JB, nima abunda nake tunani kenan, but na tambayesu ko akwai mai hoton ta ya bani suka ce a'a, amma Baffa Ali ya yimun alƙawarin cewa kafin nasake komawa zai bincika mun cikin family ko za a samu wanda ke dashi" cikin sanyin murya Momy ta ɗago kai don gaba ɗaya jikinta ya gama sanyi jin halin da ake ciki ta ce,

"Before that my soon, yana da kyau mufara gayawa ALLAH, mu bashi cigiyar baiwar sa shi da kansa kafin mukai a gidajen rediyo, Inaga wannan shi zai taimaka mana ta hanya mai sauƙi wajen cin nasarar ganinta"

"Upcouse Momy kin kawo shawara, gobe zan kai sadaka a masallatai da kuma makarantun islamiya ayi mana saukar alƙur'ani"

"Hakan ma nada kyau, kafin nan kuma kaima damu duka mu dage wajen addu'a, mu lizimci istigfari da kuma faɗar laa ilaa ha illa antas subhanaka inni kuntu minazzwalimieyn, na ji malaman sunnah da yawa na faɗar cewa babu abunda yafi istigfari saurin warware matsaloli, haka ma duk girman matsala da damuwa idan bawa ya taso istigfari agaba yana yi ba safe, rana, dare to ALLAH zai warware matsalar kuma ya buɗe masa ƙofofin alkhairi da suka toshe masa, don haka sai mu maida su abokanan firar mu daga yau, sai kuma azumi, idan son samu ne ko sau biyu ne zuwa uku muriƙayi gaba ɗaya mu a sati, sai muyi tawassuli da wannan azumin muroƙi ALLAH ya bayyanar mana da ita, Ni nayi imani da ALLAH cewa matuƙar muka koma ga ALLAH gaba ɗayan mu muna masu sanar dashi damuwar mu da buƙatocin mu tabbas zai amsa mana domin shine waraka kuma maganin kowace matsala da damuwa saboda shi nariƙa alokacin da duniya tai mani ƙullin goro, yayin da dangi na suka guje ni, dangin mijina suka kore ni suka juya mani baya, sai gashi ALLAH da baya gudun bayin sa ya riƙe ni irin riƙon da su dangin nawa bazasu iya yimani ba, yayi mani gata irin gatar da dangin miji bazasu iyayi mani ba ya kuma zame mani kariya jigo na rayuwa daga ƙarshe ya fiddani aƙuncin da nake ciki ya dawo da ahalin mijina agareni, kuma ina da tabbaci da yaƙini akansa cewa suma dangin nawa zai dawo mani dasu in Sha ALLAH" ta ƙare maganar tare dasa gefen hannu ta goge hawayen da suka zubo mata tunawa da iyayenta, don idan tace basa cikin ranta to tabbas tayi ƙarya,

"Alhamdulillah da samun uwa tagari kamar ki, haƙiƙa ni da ɗan uwana Jabir da kuma ƙaunar mu Razina mun fi kowa sa a arayuwa da muka sameki a matsayin mahaifiya, mun ji shawarar ki sannan mun aminta da ita, zamu riƙe ta a matsayin wasicci koda bayan rayuwar ki ne don warwarewar matsalolin mu aduk lokacin da damuwa tayi mana ƙullin goro" mm ya faɗa yana mai jinjina imani irin na Momy a zuciyar sa, Jabir kuwa murmushi kawai yayi don hausawa kan ce labarin zuciya a tambayi fuska, ko bai faɗa ba ansan dole yayi alfahari da samun nagartacciyar uwa da yayi a wannan duniyar.

Bayan mm ya gama sauke gajiya da kuma hutawa da marece ya shirya ya faɗawa Momy zai je wajen Hajiya tayi masa ALLAH ya kiyaye tare da cewa ya gaisheta, har ya fita ta kirasa ta ɗibar masa kayayyakin daya zo dasu daga ƙauye ta ce yakai mata, dama tuni ya kira Janan ya faɗa mata su haɗu gidan grandma, don haka ko da ya je ya tadda ita acan,

Cike da farinciki ta tarbe sa tare da taya sa murnar ganin ajalinsa da ya yi, har tana tsokanar sa ALLAH yasa ba a samu ƴar bafillatanar data disashe mata tauraruwa ba, cikin zolaya shima ya amsa mata da cewa, ba a samu ba amma dai ankusa, don ya baro Maryam tauraruwar ta na neman kutso wa cikin duniyar sa, nan take Janan ta ɗaure fuska tare da juyar dakai gefe tayi fushi, murmushi ya yi haɗe da juyawa wajen grandma data fito tana yi masa lale mar haban ya shiga gaishe ta yana dariyar Janan,

Dariyar itama grandma tayi kafin tace,

"To ita waccen iyayen fushin da bata gajiya me akayi mata"

"Ƙyaleta Hajiya tambaya tayi na bata amsa shine take fushi"

"Toooo...kun fi kusa dai ni bazan ce komai ba"

Saida suka ɗan taɓa fira da Hajiya sannan ta koma ciki ta basu waje bayan ta cewa mai aikinta ta kawo mata abinci saboda bata samu taci da rana ba,

Mm kuwa da yake ya kwana biyu basu haɗu da noor alb ɗin tasa ba har aka kira sallar isha yana can, dama bayan sallar magrib Jabir ya iskosa acan shima ya je gaida grandma, don haka ya zauna jiransa har zuwa bayan sallar isha, ganin dare ya yi ya matsawa Janan tawuce gida su kuma suka zauna suka ci gaba da firarsu da grandma har ƙarfe tara da rabi na dare yayi sannan sukayi sallama da ita, suna fitowa daga falon Abba na ƙoƙarin shigowa shi kuma, wani irin mugun kallo ya bisu dashi ɗaya bayan ɗaya yana ƙoƙarin tunano inda yasan fuskokin su, mm ne yayi ƙarfin halin rissinawa ya gaishe shi, shi kuwa Jabir ko inda yake bai kalla ba ya wuce abunsa don kar ya gane fuskarsa, kallo Abba ya bisa dashi ba tare daya amsa gaisuwar da mm keyi masa ba ya wuce ciki ransa nayi masa suya,

Yana shiga cikin fushi da ɓaci rai ya fara magana,

"Hajiya su waye wuɗan nan yaran marasa tarbiya, musamman wancan ɗayan dake saye da wasu ƙazaman ƙananan kayi ajikinsa amma yake ɗaukar kai kamar wani isasshe, sai nasa atumurmusa mani shi yanzun nan, matsiyacin banza da wofi, Inaga babu manya agidan su shiyasa baisan darajar mutane ba" ya ƙare maganar tare da tattara babbar rigarsa sannan ya zauna yana hucci,

Tsaki Hajiya tayi da duk inda ranta yake ya gama ɓaci tare da cewa, "sannu kai wanda kasan darajar manya, ai naga kai daka shigo ka fara gaishe ni kafin kafara wannan baƙar fitinar taka da bata ci bata canyewa, haba! Kai ko gajiya baka yi? Na rasa sai yaushe zakayi hankalin gane cewa Annabi ya faku, idan shi wancan bai gaisheka ba kake masifa, to shi wannan da ina kallo ya gaisheka ka ƙi amsawa me zaka ce?, Wlh Usman ka kiyaye ni da wannan halin naka domin ya fara kaini bango, har kake cewa babu manya a gidansu baisan darajar su ba, to taya za ayi yasan darajar tasu tunda sun yakice sa ajikin sun wofantar dashi sannan kuma sun zubar da tasu darajar da suke da ita agaban sa, ai barewa baza ta taɓa yin gudu ɗan ta yayi rarrafe ba" ta ƙare zancen cikin ɓacin rai haɗe da miƙewa ta shige bedroom ɗinta ta barshi falon zaune.....

*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now