PAGE__33

118 4 0
                                    

_Page 33_

*TUKUICIN SO💞*

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*
______________________________
Suna kammala cin abincin Abba ya shigo falon ransa a ɓace kamar zai tashi sama, kallo ɗaya Janan tayi masa ta sadda kanta ƙasa ganin yanda ya nufo wajen yana nuna ta da yatsa kamar zai daketa saboda tsananin ɓacin rai,

"Dama ke shashashar yarinya ce ban sani ba?, Har yaushe kika zama marar kunya haka da bata san kima da darajar mutane ba da har kike da zimmar ɗaya hannu ki mari yaron mutane don kinga yana son ki?, To bari kiji in faɗa maki, ko kina so ko bakya so aure tsakanin ki da Asgar kamar anyi ma an gama ne, ya rage naki ki koyawa kanki son sa da kuma martaba sa ko kuma akasin hakan don na lura so kike yi ki wulaƙantani tare da maidani ba abakin komai ba a bainar jama'a, kuma wlh baki isa ba, baki isa ba kinji na faɗa maki, shashashar yarinya kawai"

Sai alokacin ta ɗago idanuwanta da suka cika tafi da ƙwalla tana kallon mahaifin nata ta ce,

"Abba don ALLAH kada kayi haka, kayi tunani wlh ba mutumen kirki bane.." kafin ta ƙarasa ya katse ta ta hanyar katsa mata tsawa tare da ɗaga mata hannu ya ce,

"Rufe mun baki anan ko nazo na tattakaki a wurin, ke ɗin kirki ne dake da har kike da ƙwarin guiwar faɗar haka akansa, ina ke yanzu jayayya kike yi dani akan abunda na zaɓa maki, to taya 'yar kirki zatayi haka wa mahaifinta" cike da mamakin kalamin sa na ƙarshe take kallonsa kafin can cikin karyewar murya kamar za tayi kuka tana girgiza kai ta ce,5

"Abba ba haka bane wlh, a yanda naga ka dage akan zaɓin daka yimun da ace wani ne daban ba shi ba to dana haƙura da nawa zaɓin nabi naka, amma gaba ɗaya a mahangar hankali da tunani wlh akwai tangarɗa da ƙaramcin tarbiya ga wanda ka zaɓa mun, shiyasa ko mutuwa zanyi bazan taɓa yarda na auresa ba balle har na iya rayuwa da shi"

Wata uwar tsawa ya daka mata data matuƙar tsoratata tare da kaɗa mata ƴan hanjin ciki kafin a hasale ya ce,

"Enough Janan!, Ni kike maidawa magana saboda kina ganin kin isa da kanki yanzu? To ai kece keda ƙaramcin tarbiya ba Asgar ba, don haka tashi ki ɓace mun da gani, kafin na ɓuɗe idanuwa na" ya ƙare zancen yana nuna mata hanyar fita,

"Abba.."

"Ki fata nace" ya faɗa da ƙarfi kamar zai dake ta, cike da tashin hankali da tsoro ta miƙe ta bar ɗakin aguje tana wani irin kuka mai tsima zuciya, daidai lokacin grandma da isowar ta kenan ta zo duba Nihal kamar yanda ta alƙawarta ɗazu ta turo ƙofar falon ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, muryarta da Janan ta jiyo ta sata juyowa da ƙarfi daga upstairs ɗin da take ƙoƙarin hawa ta nufo wajenta aguje tare da faɗawa jikinta tana sake sakin wani kukan kamar ranta zai fita,

"Subhanallahi, lafiya Janan?, Me yake faruwa ne?, Ina Nihal ɗin ne?" ta jefo mata tambayoyin a jere ba tare data bari ta bata amsa ko ɗaya ba saboda tsananin ruɗewar da tayi, ganin bata da niyar bata amsa sai faman kukanta takeyi yasa ta ƙara so shigowa cikin falon tana ƙwaƙwalwa Madam florence kira, da sauri Madam dake saye da kayan shiga kitchen tana gyara inda tayi aikin abinci ta iso haɗe da duƙawa har ƙasa tana gaishe da grandma, ba tare data amsata ba ta jefo mata tambaya cike da son jin bayani daga wajen ta,

"Me yake faruwa ne agidan na tadda Janan tana kuka florence?" Ta kai ƙarshen zancen idanuwanta akanta tana ƙoƙarin fahimtar ko akwai wani abu daya faru,

"Hajiya ina kitchen ina aiki ban san meke faruwa ba, na dai san a gabana Janan ta shiga part ɗin alhaji ta ce zata je dubo Nihal.." kafin ta rufe baki Hajiya tayi saurin katse tta ganin Abba na fitowa part ɗinsa riƙe da hannun Nihal,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now