_Page 60_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
Kallo Janan ta bita dashi har ta ƙaraso kusa da ita tana ci gaba da kukan, ganin supervisor ya shigo lab ɗin har lokacin Amira bata dena kuka ba ya sa Janan tayi saurin tura invitation card ɗin auren su agroup watsApp nasu na department sannan ta kashe data ta jefa wayar cikin jikka ta kaita can gefe ta ajiye, ta dawo ta ɗora hannunta saman kafaɗar Amira da bata ma san kusa da ita take ba, cikin sanyin murya ta ce,
"Amira meke faruwa?" Da wani irin shock Amira ta ɗago ta kalleta jin muryar ta akusa da ita tayi wani irin janyewa da sauri tabar wajen ta kuma kusa da wata sai ya zamana akwai mutum ɗaya a tsakanin su, wani kallo Janan ta bita dashi cike da mamaki da kuma rashin jin daɗin abun da tayi mata, daidai lokacin supervisor ya kawo gare ta tare da aza mata question paper da kuma booklet yana faɗin, "Janan lafiya?, Is any thing wrong?" ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa,
"No sir" tana mai ɗaukar questions paper ɗin har lokacin idanuwan ta nakan Amira data kasa haɗa idanuwa da ita sai faman share ƙwalla da takeyi, daga ita har Amirar rubuta jarabawar kawai suke yi amma ba cikin daɗin rai ba, kasancewar wacce ke kusa da Janan sai faman regen booklet ɗin ta take yi tana satar amsa yasa supervisor ya ɗauketa daga wajen ya maida ta can baya, ya rage tsakanin Amira da Janan ba mutum ko ɗaya, daidai lokacin Ingaski ya shigo wajen don couse ɗin sa ne akeyi, line by line ya shiga bi yana tambayar su if there's any question tare da gyara masu apparatus ɗin da suke amfani dasu yana duba quantity ɗin kowane chemicals da suke haɗawa har yakai inda Janan da Amira suke, idanuwa ya ƙura wa Janan yayin da Amira ta riƙa ja gefe daga tsakiyar su ɗin da yake tsaye yana jefo ma Janan tambaya haɗe da mayen kallo, ganin tayi banza dashi ya sa ya yi murmushi ya bar wajen, ɗan tsaki Janan tayi haɗe da rolling idanuwan ta kafin ta miƙa hannu zata ɗauki wani chemical ta haɗa don fara amsa tambaya ta gaba, da sauri Amira ta miƙa hannu itama zata ɗauka, amma saboda hannun Janan ya riga kaiwa sai ta riga ta ɗauka, saurin wafce chemical ɗin Amira tayi a hannunta cike da ɓacin rai Janan ta ɗago kai, enough is enough ta faɗa cikin zuciyar ta saboda Amira ta fara kaita bango, ta fara ƙure haƙurin ta, don haka kawai itama ta wafce kwalbar tare da balle ma Amira wata irin harara, sake yunƙura wa Amira tayi da niyar karɓa supervisor ɗin ya daka mata tsawa haɗe da pointing ɗin ta yana mai yi mata gargaɗi akan idan ta sake yin wani misbehaving zai kece takardar ta ya kore ta,
Ingaski kuwa yana fita shugaban makarantar ya nufo lab ɗin shima yana amsa waya, wacce ba da kowa yake yi ba sai mahaifin Janan, zagayen ɗaliban ya shiga yi har ya kai kan Janan, tsaye ya yi yana kallon yanda take amsa tambayoyin a natse kafin ya miƙa hannu yana jujjuya kwalaben chemicals ɗin dake gaban ta sannan yabar wajen, yana ɗagawa Amira ta sake miƙa hannu zata ɗauki cikin chemical ɗin kawai Janan tasa hannu ta ɗauke ba tare data kalli inda take ba tana duba reaction ɗin da sauran chemical ɗin data haɗa suke bayar wa tana observing amsar ta aciki, wanda ta ɗauko shine na ƙarshe da zata zubawa ta samu amsar da take buƙata, don haka tana zubawa wani irin hayaƙi ya taso sai ga idanuwan ta, saɓanin na sauran ɗaliban da suna zubawa zai basu reaction mai kyau da kuma amsar da suke buƙata, kalmar innalillahi wa inna ilaihirrajiun ta fara furtawa da ƙarfi kafin can ta saki wata irin ƙarar da sai da tasa sauran ɗalibban firgita sannan ta faɗi ƙasa tana wayyo Amira idanuwana, wani irin cira Amira tayi jikinta na rawa haɗe da rugawa zata bar lab ɗin, in tayi nan tayi nan su kuma sauran ɗaliban musamman mata suka yo kan Janan suna ƙoƙarin taimaka mata, jin sunanta da Janan ta kira da ganin yanda Amira ke ƙoƙarin guduwa ya sa supervisor ɗin ya ce a kamata, kafin ya rufe baki har ta fice daga lab ɗin aguje, nan take cikin mazan ajin nasu wani ya bi bayan ta haɗe da ci gabanta ya ɗauke ta mari kafin ta dawo hayyacin ta har wani ya sa ƙafar sa ya sharɓeta ta faɗi ƙasa kanta ya bugi dutsi, suna ƙoƙarin rufeta da duka malaman dake kusa suka dakatar dasu ganin yanda jini ke zuba daga kanta sai faɗi suke a bari su illatata itama don Janan nada good contact da dukkanin ƴan ajin nasu, ba tada abokin faɗa haka kuma abunta bai taɓa haɗa ta da wani ba, shiyasa ran kowa ya ɓaci saboda yanda ƙarara ta bayyana ko ma meye yafaru da Janan ɗin ita ce, musamman yanda supervisor ɗin ke masifa yana a kama Amira kada a bari ta gudu,