_Page 25_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
Ta gefen idanuwa Janan ta kalli Amira cike da jin haushi kafin ta saita mirror ɗin motar saiti da fuskar mm dake sun kuye da kai yana latsar wayarsa tace,
"Yallaɓai, kabari in saukeka gida, daga can kaga sai na gaida momy da Razina"
A ɗan Razane ya ɗago kai jin abunda ta faɗa idanuwan su suka yi karaf da juna ta cikin madubin ta kashe masa ido ɗaya haɗe dayin murmushi,
"Yes, ko akwai wani abune?"
"Ko ɗaya ranki shi daɗe, gidanmu ai gidanku ne, saboda haka babu buƙatar sai kin tambaya, yanda duk kike so haka za a yi"
"Awwnn..that's my golden man, in sha ALLAH zan je amma ba yau ba saina shirya, saboda yau muna da baƙi agidan kuma nasan za a jira dawowata"
"Dama nasan ai bada gaske kike yi ba" ya faɗa tare da sauke ajiyar zuciya don har ga ALLAH bai shiryawa zuwanta gidan ba,
"Haka dai kake tunani, amma zan baka mamaki wata rana"
"Ina jiran haka, amma kafin nan ya kamata ki aji yeni a bakin gate da mun fita saboda na tuna akwai inda nake son zuwa, ke kuma kinga kince kunada baƙi a gida kar ya zamana na ɓata maki lokaci"
"Babu ɓata lokaci acikin kasantuwa tare da masoyi, uzurinka kaɗai zaisa na ajiye ka ɗin kamar yanda ka buƙata, saboda ban sani ba ko wani babban aiki ne zaka je nemo mana ko kuma wani alkhairin ne ke kiranka, badon haka ba bazan sauke ka a ko ina ba sai inda ya kamata"
"Nagode nurul alb, shiyasa kike daɗa shiga zuciya ta, Amira ki tayani godiya ga ƙawarki, kirkinta ba kaɗan bane, haka ma karamci da mutuntakar ta sun shallake tunanin mai rai, ina matuƙar jinjina wa halaccin ta da yanda take gudanar da rayuwarta a tare dani ba tare da ganin fifikon kuɗi ko wani abu a tsakanin mu ba, a gaskiya ita ɗin ta daban ce, a mata kaf banda kamar ta kuma na tabbata bazan taɓa samun kamarta ba, kai ko kusa da irinta bazan taɓa samu ba arayuwa" ya ƙare zancen yana kashe mata idanuwa ta madubi, murmushi tayi mai cike da jin daɗi haɗe da kallon gefen da Amira take zaune tana ji tamkar ta haɗiye zuciya ko ta kurma ihu tsabar baƙin ciki, sai da tayi 'yar gyaran murya ganin gaba ɗaya Amiran ta shiga wata duniyar sannan ta ce,
"Hubbin ruh kenan, ai indai Amira ce ko ƙinka bata yi, da alama yau 'yan surutun nata basa kanta"
Sai alokacin Amira ta juyo tana kallon ta tare da sakin murmushin da ya zame mata tamkar an sakata dole ne haɗe da cewa,
"Janan kenan, ai yin shirin shiyafi zama alkhairi a wurina saboda bansan me zancewa ba, tsakanin ki ne dashi ko ba haka ba mm"
"Eh..amma kuma ai ya kamata ki tofa bakin ki tunda na sakoki aciki"
"Acan dai, wacce kafaɗa don ta ai na tabbata taji kuma ta yaba, don haka ba sai nace komai ba"
"To shikenan, godiyar fa? Itama bazaki tayani yi ba?" Karaf Janan da haushin firar da yakeyi da amiran ya fara kamata ta ce,
"Yallaɓai kadena tunanin akwai godiyar da zatayi tasiri azuciyar masoya sama data junan su, tuni zuciya ta amshi saƙon ɗaya fito daga ƙasa zuciyar ka, haka kuma kunnuwa suka saurari mafi soyuwar kalamai masu matuƙar daɗi daga bakin ka, ni Janan matar Muhriz ina godiya da tarin yabonka agareni, ALLAH ya nuna mana ranar da mafarkin zai zamo gaskiya, a ranar zan baka TUKUICIN SO na wannan kyakkyawan yabon da kayi agareni"
"Ajiye ni anan Janan" Amira ta faɗa daidai lokacin da suka kawo bakin gate ɗin makarantar tana ƙoƙarin danne ɓacin ran daya gama cika mata zuciya,
"Kiyi haƙuri har miƙa rasa fita daga wajen tunda shima hubbin ruh anan zai sauka, koda yake ke bazan ajiye ki nan ba tunda round kika ce zaki sauka" ta ƙare zancen tare da jan wani irin wawan burki a daidai lokacin da suka fito ɗin sanadiyar motocin da taga sun tari gabanta har guda uku sun sakata a tsakiya, kafin tayi yunƙurin yin wani abu har guard ɗin na mahaifinta sun fito su wajen tara sun zagaye motar ta suna mazurai, cike da takaici ta sauke glass ɗin tagar gaban ta na faɗuwa saboda gudun abunda zai iya faruwa ga masoyin ta, cikin dakewar murya ta kalli ɗaya daga cikinsu ta ce,