_Page 6_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
_Follow me on wattpad@Billysfari9 httpson a userhttps://www.wattpad.com/1231665142?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=EwW9KlBM7lslQDR9ocKvcHE2Kh6HObz4smPNFZjvFoyf%2BzVLltD0tBsHM2bvRyWMIhmS%2FlPhBh9EqHHKEAerqqhmLTO6zBBU0VHXVkUXcNWnJxk274crMybs6d0iQKcE_
______________________________*S* hiru duk sukayi har sai da ta sake maimaita tambayar data yimasu a karo na biyu sannan Jabir ya ɗago kai yana kallonta, har zai yi magana tayi saurin ɗaga masa hannu ganin Muhriz na susar gefen kunnensa da ɗan yatsa, ɗabi'arsa kenan aduk lokacin da zai faɗi wata magana mai muhimmanci, hakan yasa ta dakatar da Jabir don tasan maganar da zai faɗa sai tafi tasa,
"Muhriz kada ka Ɓoyemun komai, faɗamun ko meye kaji ko?"
Sai daya ɗan muskuta tare da sakin sanyayyiyar ajiyar zuciya yana kallonta sannan ya ce,
"Ammm...Momy kiyi haƙuri mun yanke shawarar aikata wani abu ko ince na yanke shawarar aikata wani abu bada sanin kiba don nine nakawo wannan shawarar kuma na hana Jabir ya sanar dake saboda sanin bazaki taɓa yarda ba"
"Muhriz, har akwai abunda kake tunanin zaka faɗamun akan wani lamarin daya shafi kasuwanci ki ko rayuwarmu nakasa yarda? Nifa na reneka kuma nabaka tarbiya! Ai matuƙar na yarda da tarbiyar dana baku to bazan taɓa hana kuba sai idan har nasan zaku cutu aciki, je kai tsaye ka faɗamun ko meye ma, in sha ALLAH zan fahimceku, wannan yanayin ne dai da nake ganinku aciki bazan lamunci jurar ganinsa ba"
"Eh to! Dama ganin halin da ɗan uwana ya faɗa ciki wajen neman matar da zai aura ne yasa nayi tunanin yin basaja don samawa kanmu mafita, ma'ana na sauya kaina daga Muhriz pilot da aka sani yanzu zuwa Muhriz maraya ɗan asalin ƙauyen caranci ta hanyar ajiye business ɗin da mukeyi da aiki na wani ɗan lokaci muka koma sana'ar saida dabino da kwakwa a makarantar kwalejin ƴan mata ta wannan garin..."
Tun kafin yaƙarasa maganar Momy ta aza hannu a ƙirji haɗe da cewa,
"Oh my god, why? Why naa!"
Ta ƙare maganar kamar zatayi kuka, ta sowa yayi ya dawo kusa da ita haɗe da riƙo hannuwanta ya ce, "pls Momy calm down!, Ba wani abu bane, damu dake da kuɗin da wuɗanda ke irin sana'ar duka ɗaya ne, all we want from you shine addu'a"
"I know mu son, amma kaga yanda kuka koma ne?, Akwai hanyoyi da dama da zaku bi kusamu matayen aure, amma wannan sam bata dace daku ba, look at your hands yanda suka koma" ta ƙare zancen tare da juya hannunsa tana kallon cikin tafinsa da yayi jaa sosai har da kanta"
"Momy this one is nothing as much as za'a samu abunda ake so, just pray for us"
Juyawa tayi tana kallon Jabir daya maida hankalinsa gaba ɗaya ga waya yana latsa shima ta riƙo nasa hannun tana kallo, bai wani nuna alamar gajiya da wahala ba atattare dashi kasancewar shi irin blacks beauty d'in nan ne, jikinsa bai cika nuna wani chanjin yanayi ba kamar na Muhriz dake da hasken fata, shiyasa ko jan da hannun Muhriz yayi nashi bai nuna hakan ba, skin ɗin ce kawai tayi ɗan tauri kaɗan ba kamar yanda take ba.
"My son, kuna ganin wannan plan ɗin da kuka shirya it work kuwa?, Kodai ku canza wani pls" ta faɗa cikin marairaice fuska don ba kaɗan take jin yaran nata arai ba, dariya yayi haɗe da kashe wayar ya jefa a aljihu sannan ya ɗora hannunsa akan nata ya ce,
"It work kuwa don har anyi wuf da zuciyar yaronki, and i'm sure soon brother zai kawo ta ta gaisheki"
Juyawa tayi fuskarta cike da farin ciki tana kallon mm daya sinne kai ƙasa ta ce,