PAGE__22

148 5 2
                                    


"Janany sister in jin dai basu jimasa ba?"

"Sun yi hakan Adda"

"Shine kuma naga farin ciki a fuskar ki kina dariya?"

"Ya zanyi Adda tunda soyayyar da muke yiwa juna ta kasa bari mu fahimci hakan, gaba ɗaya girman soyayyar da yakeyi mun ya hana ya nuna mani damuwa ko ɓacin rai akan abunda akayi masa, damuwar sa kawai nazama cikin farinciki, kin kuwa ga ai dole nayi hakan washi don faranta zuciyar sa"

"Tirƙashi, lallai son gaskiya yakeyi maki, amma ya kamata ace kin yiwa kanki adalci shima kinyi masa Janan, tunda kin san Abba bazai taɓa bari ki auresa ba kada ki bari a riƙa gana masa wahala haka, ki haƙura dashi mana ki samu daidai ke wanda zai zamo daidai da ra'ayin Abbanmu"

"Point of correction Addah Nihal, ba mm kaɗai ke yimun son gaskiya ba, ni kaina ina yi masa son gaskiya fiye da yanda kike tsammanin nasa, zancen kuma haƙura na barsa magana ce da bata da wani tasiri a ƙwaƙwalwa ta balle kuma ta samu muhalli a zuciya, mm rayuwata ne, saboda haka no going back akan sa" ta ƙarar maganar tare da ɗora hannunta akan kafaɗar ta tana rolling idanuwanta, ganin yanda ta saki baki tana kallonta cike da mamaki yasa tayi murmushi haɗe da wucewa ba tare da ta sake cewa komai ba,

Ta fi Nihal ta yi tare da jinginawa a jikin bangon ƙofar shiga part ɗin sannan ta ɗora hannayenta data naɗe akan ƙirji tana faɗin,

"Wow fantastic! yau she kika koma haka Janan?, Kenan kina nufin zaki bijirewa maganar mahaifin ki ne kibi zaɓin ranki?" Cak Janan ta tsaya daga bakin ƙofar da take ƙoƙarin shiga tare da juyowa ta kalli Nihal, girgiza kai tayi tana murmushi haɗe da sinne kanta ƙasa, tafi sakonni biyar a haka kafin ta juyo gaba ɗaya hannayen ta na akan ƙirji tana kallon yayar tata,

"Adda Janan wai ni kike kira zan bijirewa mahaifina nabi zaɓin raina?, To ai inaga wannan ba ɗabi'a ta bace, don haka idan ma nayi hakan sai ayimun uzuri, kefi kowa sanin so ba ƙarya bane?, Ko don na kasa bayyana nawa yasa ake kallonsa tamkar wasar yara har ake ƙoƙarin nisan ta ni dashi? Yayin da ke kuma kullum ake kokuwar ganin an inganta naki son ta hanyar matso maki da abunda kike so a kusa dake ba dare ba rana, koma dai meye Adda ni ina son mm ko Abba baya son sa, haka kuma zan iya rayuwa dashi koda kowa zai rabu dani"

"Haka kike gani kuma zaki iya?"

"Sosai kuwa, wai ma meye matsalar soyayya ta Adda?, A zatona kece ta farko da zaki fara bani goyon baya tare da sharemun duk hawayen da zasu kwaranya a idanuwa na saboda kin san meye so, kin san zafin sa da kuma raɗaɗin sa, amma wai sai gashi ke da kanki ke neman yi mani kashedi da abunda kika san ke bazaki iya haƙura kiyi sa ba, anan ma kin bani mamaki"

"A'a Janany sister, baki fahimceki bane, ko ɗaya bana jayayya akan soyayyar ki, halin da zaki shiga aciki ne nake tausayin ki a kansa, i don't want you to be suffer anyi more, rayuwar ki zata shiga garari ne aduk lokacin da kika faɗa hannun wanda bazai iya kulawa dake ba kamar yanda ni Abba muka kula dake, i know zaki ce ai bashi ya laƙawa kansa takaicin ba, but remember kowane tsuntsu kukan gidansu ya kamata yayi, sannan ko hausawa sukan ce kamata yayi ace ƙwarya tabi ƙwarya ba wai akushi ba"

"Adda kenan, wannan zance ai ba karatu bane balle ƙwaƙwalwa ta iya fahimtar sa, sannan bai zo a rubuce ba, bai kuma zo a aya ko hadisi ba, taya kike tunanin zan riƙesa a matsayin makami da zai bani kariya ko kuma tudun dafawa a rayuwata?, shi so babu ruwan sa da wannan ƙwarya ce wannan kuma akushi ne, ba akushi bama Adda, hatta kwando shi so zai iya haɗawa da ƙwarya babu abunda ya damesa, saboda haka in dai wannan tunanin shine ya hanaki supporting soyayyata to ki ajiyesa gefe, domin tuni zuciya da gangar jiki sun riga sun shirya tsaf da amsar ko wane irin kalar sauyi da zai zo a cikin rayuwata" tana gama faɗar hakan ta juya ta shige abinta, don ita kam shirye take da fighting da kowa akan soyayyar ta tunda har ya iya jure komai akan ta,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now