_Page 49_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
Da sauri Abba ya taso hango Jazz daya tura a ɗauko Hajiya suna shigowa biye da ita a baya, ya ƙaraso wajen cike da biyayya yana yimata sannu da zuwa tare da riƙo hannun ta suka ƙara so cikin falon tare, a inda ya tashi ya yiwa grandma data bi falon da kallo tare da mutanen dake ciki wurin zama sannan ya zauna ƙasan ƙafafuwanta yana gaisheta,
Fuskarta a sake ta amsa haɗe da kallonsa ta ce,
"Usman lafiya tun daga waje naga motoci ga gida cike da mutane da kuma kayan arziƙi?"
Murmushi ya yi tare da juyawa yana kallon kayan dake shaƙe acikin falon sannan ya maido da kallonsa ga Hajiya yana sosa ƙeyar kansa ya ce,
"Ammmm.. Hajiya kin dai gani, arziƙi daga sama kin san in kafi wani wani ya fika, shiyasa ma na aika a ɗauko ki saboda ki ganewa idanuwan ki tare da sanya albarka, faɗin malam ba haushi ya ce daka tara arziƙi ka barwa yaro ƙara ka haifesa dashi, duk da dai ban sanar dake zancen da wuri ba saboda ina son naga tabbatuwar lamarin"
"Ban fahimceka ba Usman, ƴar lelen taka ta samu mijin aure ne?, Ko zaɓin nata ne ka nemo mata" saida ya yi dariya sannan ya ce,
"A'a ba ita bace, takwarar ki dai ce, ai ita muna addu'a ne har yanzu tunda lamarin yaron ya zamo gaibu.."
"Kuma akace dole sai shi zata aura ba" Hajiya tayi saurin katsesa tare da bashi wannan amsar cike da takaici, jin haka yasa Abba saurin cewa
"ALLAH ya baki haƙuri Hajiya, ba haka nake nufi ba, amma kinsan ai komai lokaci ne dashi, kina addu'a kema sai kiga ALLAH ya kawo mata shi har gida, yanzu dai bari na gabatar maki da aminina ambassador Hussain gaya can zaune nasan kin sanshi, to ɗan wajen sa ne yaga Janan tun a shekarun baya ya ce yana so, kwanaki ya bijiro da maganar saina bashi damar zuwa ya nemeta don na tabbatar da zancen sa inda gaske yakeyi, kin san halin abokin nawa? Yana jin haka shi kuma sai ya kwaso kaya suka zo gaba ɗaya don su nuna mani cewa eh da gaske ɗin suke" ya ƙare zancen tare da ɗagawa Asgar hannu alamun yazo, tunda ya fara magana Hajiya ke kallonsa cike da mamaki har ya gama, bata ce dashi komai ba sanadiyar ambassador Hussain daya ƙara so wajen yana gaisheta cike da girmamawa, cikin sakin futska shima ta amsa haɗe da tambayarsa ya iyalin nasa da sauran ayyukan duk lafiya, ya amsa mata da komai lafiya yana murmushi,
Dafa Asgar Abba yayi daya zauna kusa dashi yana gaida Hajiya shima, ya ce
"Hajiya wannan shine Asgar ɗin dake son Janan, babban soja ne da ƙasar sa ta Ethiopia ke alfahari dashi" murmushi Hajiya ta yi tana danne wani takaici dake taso mata daga ƙasan zuciya haɗe da cewa,
"Au kace shine maigidan nawa?, Kun zo lafiya?"
"Lafiya klw" Asgar ya amsa mata yana sinne kai cike da kunya, cikin ƴar tsokana Hajiya taci gaba da cewa,
"To kai ga ni me zakayi da Janan yaro, ko baka ga na fita kyau da kuma ƙarko ba?"
"Ah Hajiya ai ke ta musamman ce, ki bari idan na riƙa matata a hannu sai muyi wannan zancen, amma dai kiyi ƙasa ƙasa da muryar ki kada taji tace ta fasa yina" ya bata amsa yana dariya, kasancewar grandma nada son barkwanci yasa tayi dariyar itama haɗe da cewa,
"To ashe kai ragon namiji ne tunda kake tsoron ta, ai ba'a san soja da tsoro ba musamman na macce"
"Kai, ai Hajiya ita ko soja ke tsoro don babu abunda ke tsorata soja aduniya kamar macce, take ne zata narkar da busasshiyar zuciyar sa idan sukayi arangama"
"To masha ALLAH, ALLAH ya tabbatar da alkhairi, mudai amincewar junan ku shine muradin mu, matuƙar aka samu haka tsakanin ku to muna farinciki tare da sanya albarka" ba asgar ba hatta Abba da mahaifin sa sun yi farincikin yanda Hajiya ta karɓi zancen hannu biyu, a tsammanin su matsalar su ta kau don indai ta ɓangaren Janan ne ganin suke kamar ma ta gama amincewa idan ta zo, nan yake sanar da ita cewa ai tare suke da baƙi mata suna wancan ɗayan falon bari a kira su su gaisa ta ce a'a ya bari ta ƙarasa can su gaisa dasu, tare suka miƙe har ambassador da Asgar suka nufi falon da su yaya Jalila ke ciki har lokacin suna mita akan tabbas in Nihal ce wacce ɗan nasu zai aura baiyi mata ba,