_Page 39_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
______________________________
Sun jima a cikin guiden ɗin ko wace na abunda ke gabanta har aka kira sallar azahar, Janan ce ta fara miƙewa ta nufi cikin gidan kafin itama Nihal tamiƙe tabi bayanta,Suna kammala sallolin su suka dawo falo suka zauna suna kallon wani shiri a tashar zeeaflam da Nihal ke matuƙar so wanda sanadiyar hakan yasa itama Janan tafara kallonsa, wani saurayi aka nuno aciki Janan tayi saurin cewa, "Adda wannan gayen yana bala'in yanayi da mm ɗina, hadda shi yasa nake ƙara son kallan shirin nan don ba komai nake ganewa aciki ba" dariya ta aza mata har saida tayi mai isarta sannan ta ɗago tana yimata wani irin kallo haɗe da cewa,
"Lallai Janany sister yaron nan ba ƙaramin kamaki yayi ba, anya ma ba asiri yayi maki shiyasa kika ga yafara yi maki gizo a fuskokin mutane? Yanzu fisabilillahi taya za a yi wannan talakan baƙauye yayi kama da haɗaɗɗen ba Indiya nan?, Hmmm ni kam dai akwai wanda na sani ajin farko da gayen nan ke kama dashi amma ko waye na manta shi gaskiya" kutun-kutun Janan tayi da fuska tare da haɗe rai tana yiwa ƴar uwar tata wani irin kallo mai cike da ban mamaki da kuma takaici, badon tana ƴar uwar ta ba da yau ta mayar mata da maganar da har ta mutu bazata taɓa manta taɓa, ba tare da ta ce mata komai ba ta ajiye remote ɗin dake hannunta akan kujera tamiƙe tabar wajen gaba ɗaya, tana jin yadda take ƙwala mata kira tayi banza da ita tare da ficewa daga falon ranta aɓace,
"Mtsss...matsalata dake kenan Janany sister, wani lokacin ki fiye ɗaukar abunda ba wani abuba da zafi" ta sake sakin tsakin akaro na biyu tare da janyo remote ta gyara zamanta ta cigaba da kallon ta, ita kuwa Janan part ɗin Hajiya zee ta nufa tana mai sake jin ɗacin kalaman ƴar uwar tata akan masoyinta idan ta tuna, koda ta shiga kitchen ta samu Hajiya zee tana ɗauraye kayan data gama girki dasu yanzu, cikin girmamawa ta ƙara sa daga ciki tare da karɓar foodflaks ɗin da take wankewa tana faɗin,
"Barka da rana Aunty zee, ina wuni?"
"Lafiya klw, Janan ya kuke?" Ta amsata cikin sakin fuska da fara'a, saida ta ɗauraye foodflaks ɗin dake hannunta sannan ta juyo tana kallon ta, ta ce
"Lafiya lau nake"
"Adda ɗin ki fa, taji sauƙin?"
"Eh taji" ta bata amsa ataƙaice tare da cigaba da ɗauraye mata sauran kayan, kasancewar Hajiya zee macece ba mai yawan surutu ba yasa daga haka bata sake cewa da ita komai ba, haka itama bata ce komai ba har taƙarasa ɗauraye kayan gaba ɗaya, ta shiga goggoge mata ita kuma tana maida su inda ya kamata, bayan sun gama Hajiya zee ta kalleta tana murmushi haɗe da cewa,
"Sannu da ƙoƙari Hajiyar gida" don haka take kiranta wata ran idan tana jin tsokana, musamman idan ta ganeta ba daidai ba saboda sunan grand ma da take dashi, ɗan murmusawa Janan tayi haɗe da ficewa daga kitchen ɗin ta dawo falo ta zauna tana faɗin,
"Hmmm! kar muyi haka dake Aunty zee, ai kece Hajiyar gida, uwa maba ɗa nono sukutum da guda"
"Au! To ai shikenan kin rama, agaisheki ALLAH yayi maki albarka" ta faɗa tare da ajiya bowl ɗin data zubo cake da samosa aciki akan center table ta tura mata agaban ta, sannan taje ta buɗe fridgeyta ɗauko fresh yougurt da gorar ruwa ta ajiye mata itama ta zauna a ɗayar kujerar dake kallon ta, sunkuyar da kai Janan tayi haɗe da cewa,
"Nagode da addu'ar ki Aunty zee, Amin ALLAH ya karɓa"
"Ba komai, yau Auntyki kwaɗayi bata yi abincin kirki ba, gashinan ki taɓa"
"Kai Aunty, kullum bakya gajiya sai kiyi ta maidani tamkar wata baƙuwa"
"Ai kamar haka kike Janany, da yaushe da yaushe nake ganin ki in ba ALLAH ya kawo mani ke ba?"