_Page 43_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
Daidai lokacin itama Amira ta jawo wayarta bayan ta kammala sallah cike dasa ran ganin amsar sa koda kuwa ta baƙar magana ce, amma ga mamakin ta sai taga bai turo komai ba, hakan ya sa taji haushi sosai ta shiga shirin zuwa makaranta cikin nuƙura, kallonta Zarah tayi haɗe da cewa,"Aunty Amira lafiya kike ƙunci?, Meya faru ne" saida ta maka mata harara sannan ta ce,
"Ubanki ne ya faru" saurin rufe baki Al-amin dake zaune cikin shirinsa na makaranta yana karyawa yayi haɗe da kallon umma dake miƙawa Zarah kokonta a kofi ya ce,
"Umma aunty Amira tayi zagi" bai rufe baki ba shima ta mangaresa gefe tana faɗin,
"To uban ƴan gulma da shedi, ka faɗa ka ji daɗi" cikin ɓacin rai umma ta ce,
"ALLAH kika sake taɓamun yaro sai ranki ya ɓaci, ka barta ai sai tayi ta yi in anfaɗa mata cewa zagi da zafin rai abun ƙwarai ne, ke kenan kullum bakyada aiki sai baƙar magana ga ƙannen ki, babu ranar da zata zo ace gaki zaune waje ɗaya tare dasu baki hantare su ba, wannan wace irin rayuwa ce haka da ba'a gane ana ci gaba?"
"To umma meye yasha ruwansu dani?"
"Babu, amma ai ba laifi bane don an tambayi mutum meke damun sa, ko addu'a ce ai ayi masa"
"Ni bana so, su ƙyaleni kawai" ta faɗa tare da ɗaukar jikkar ta tayi gaba,
"ALLAH ya baki haƙuri Aunty ya kiyaye hanya" Zarah ta faɗa cikin ɗaya murya, ita kuwa umma dariya tayi haɗe da cewa,
"ALLAHu ya shiryeki Amira, da alama dai wannan kumburi ga doki ne sakkiya ga jaki, ai sai kizo ki karɓi na abun hawanki ko ƙasa zaki je muƙara a cefanen abincin namu na rana?"
Har ta kai tsakar gida ta juyo ta dawo ta karɓi kuɗin sannan ta cewa umman ta tafi, ta ce da ita "ALLAH ya kiyaye yasa adawo lafiya" ta amsa da amin sannan ta wuce, batafi mintuna uku da fita ba itama Zarah ta riƙo hannun Al-amin zata kaishi makaranta tana faɗin,
"Umma mun tafi"
"ALLAH ya kaiku lafiya, ungo ga ɗari biyu idan kin kaishi ki bashi Naira hamsin, saiki siyo mana ƴan kayan miya da albasa na ɗari da hamsin idan zaki dawo"
"To umma, busasshe?"
"Eh mana, waya riƙa mana cin ɗanyu yanda sukayi tsadar nan"
"ALLAH" Zarah ta faɗa ataƙaice tare da ficewa, ko da suka iso baki titi sun tadda Amira tsaye acan gefe har lokacin bata samu abun hawa, da yake sai sun tsallaka acan gaba makarantar su Al-amin take yasa sai da Zarah ta tsaya ta tarar wa Amira mashin da tun ɗazu ma sai latsar wayar ta takeyi tana gwada kiran mm ko ALLAH zaisa ya ɗaga a wannan karon don itakam ta kasa haƙura da rashin jin Muryar sa, mm na ɗagawa mai mashin ɗin ya tsaya da sauri tayi masa alama daya tafi ta koma gefe tana faɗaɗa fara'ar data bayyana a fuskarta yanzu, Zarah na ganin haka ta girgiza kai tare da tsallakewa abunta suka barta a wajen,
Sallamar daya ji tayi yasa bai taso mata da fitina ba kamar yanda ya ƙudurtawa ransa, Muryar sa ba yabo ba fallasa lokacin yana tattaka matattakalar jirgi ya amsa sallamar haɗe da cewa,
"Pls dawa nake magana?" Yayi kamar bai san ita ɗin ce ba, marairaice fuska tayi kamar tana agabansa tare da gyara jikkar dake rataye a kafaɗar ta, ta ce
"Haba ya Muhriz, yanzu sai kace baka gane muryata ba, Amira fa ce"
"Oh! Wace Amirar kenan?"
"Hmmm wace Amira kake da ita bayan ni masoyiyar ka, ALLAH bana jin daɗin yanda kake yimun don kaga na bayyana sirrin dake zuciyata akanka, ni fa da gaskiya nake son ka bawai da wasa ba"