_Page 62_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
Tafe yake a zuciyar sa yana yiwa kansa wuɗan nan tambayoyin daya kasa samawa kansa amsoshin su kafin ya fiddo wayar tasa ya sake kiran Sajan Maryam, bugu ɗaya ta ɗaya haɗe da cewa,
"Yes sir"
"Where's is the woman?" Kafin ta bashi amsa ya ci gaba da cewa, "just allow her to see her"
"Sir she's already gone"
"Ok, next time zaku iya barinta ta ganeta, zan yi magana da shi inspector Sadeeq ɗin"
"Ok sir, thank you"
Kashe wayar ya yi tare da shafa kansa yana jin maganganun Umma na sake dawo masa a ƙwaƙwalwa, so yake yi ya tuna a ina ya taba jin shegen muryar baiwar ALLAH nan amma ya kasa, jin da ya yi kansa na ƙoƙarin fara ciwo sakamakon matsawa ƙwaƙwalwarsa da tunani da ya yi yasa ya kunna ƙira'ar sudaisa yana bin karatun a hankali har ya ƙara sa gida, yanda Momy taga fuskarsa kamar ɗauke da damuwa yasa ta zaunar dashi tana tambayar sa meke faruwa, bai ɓiye mata komai ba ya sanar da ita yanda sukayi da Janan akan case ɗin Amira dake kulle, shiru tayi haɗe da cewa,
"A gaskiya ya kamata ka duba zancen ta, takan yuyu kayan aikin ne aka samu matsala ƙilan sunyi expired"
"A'a Momy, hakan bazai taba yuyuwa ba saboda ba ita kaɗai ce a kan ɗin ba, taya za a yi ace na kowa lafiya suke amma nata ya yi expired, dole fa akwai wani abu a ƙasa"
"To idan haka ne kaga bincike ya kamata a fara yi daga can makarantar tasu don samo bakin zaren"
"Haka ne Momy, shiyasa binciken mu ya fara akan Amira, domin tafi kowa kusanci da ita acikin makarantar kafin su fara samun matsala daga baya ta sanadiyar ita Amirar data nuna cewa tana sona, duk da Janan bata nuna damuwar ta akan hakan ba, kawai ita kaɗai ke shirmen ta kuma na tabbatar da tana jin haushi sosai ganin Janan ɗin nake so ba ita ba, kinga kuwa dole bincike ya fara ta kanta"
"Eh gaskiya dole a tuhume ta, koma dai meye abu abun a hankali, koda ba zakayi kamar yanda Janan ɗin ta ce ba, Ya kamata kabari ko mahaifiyar ta ce ta riƙa ganin ta, kasan mu mata muna da rauni, dole zata shiga damuwa sosai akan halin da ƴar tata take ciki"
"Shikenan Momy, Bara naje na kama masu Mu'azzam hotel ɗin da zasu sauka, don munyi waya dashi ya ce sun sauka suna kano har ma sun kamo hanya"
"Masha ALLAH, ALLAH ya kawo su lafiya tare da iyalin nasa suke tafe?"
"A'a gaskiya, kin san yanda abun yazo kwatsam a ƙurarren wuri shiyasa bai zo dasu ba tunda bai shirya komai ba, tare dai suke da wasu abokanan namu"
"ALLAH sarki, to ALLAH ya kawo su lafiya"
"Amin Momy, ina Jabir ne da Razina"
"Na aiki Razina, shi kuma yana can gidan na turasa yakai kayan kitchens ɗin da aka siyo, kayi waya da baffan ka kuwa?"
"Eh munyi waya ɗazu, ya ce ma su Umma Mariya na nan tafe suma"
"Eh haka ya faɗa mun, har ma an gyara masu ɗaya ɓangaren can da zasu sauka, ALLAH ya kawo su lafiya"
"Amin Momy, thank you so much" ya faɗa tare da rungume ta, murmushi tayi haɗe da cewa,
"Yau kuma ni yaro na ke yiwa godiya, for what?"
"For everything Momy, I love you so much"
"Luv you too my boy" ta faɗa tana ƙara jin ƙaunar sa aranta, bata dai san yanda mahaifiyar sa tayi ta haifesa ba amma gaba ɗaya abubuwan daya kamata ace ita yake yiwa ya kasance ita yake mawa, a hankali bayan ya fice daga falon ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa " ya Ubangiji ALLAH ka bayyanar masa da mahaifiyar sa aduk inda take matuƙar tana raye domin ta mori ɗan ta da nake cin ga jiyar sa" adduar ta kenan akoda yaushe tunda ta samu labarin mahaifiyar tasa tare da fatan tana raye bata mutu ba, haka kuma ko yaushe cikin aikawa da sadaka take a masallatai da kuma makarantun islamiya tana cewa a taya su addu'a, shi kanshi mm duk dare baya bacci dashi har Jabir, Razina ma haka suna masu tsananta addu'ar da Momy ta koya masu haɗe da istigfari ALLAH ya bayyana mahaifiyar su duk inda take, wanda ko shakka babu hakan yayi matuƙar tasiri akan lamarin shiyasa sauyuwar abubuwa keta wakana ba tare da sun fahimci hakan ba.