_Page 38_
*TUKUICIN SO💞*
*NA*
*BILLY S FARI💎*
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
______________________________
Basu bar juna ba sai kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare, shima yanayin muryar Janan mm yasoma jin sauyawarta izuwa ta bacci shiyasa yayi sallama da ita, don kuwa in ta tashi za a bi baiƙi su kwana yana jin zazzaƙar musayar ta dake matuƙar tafiya da dukkanin tunanin sa, ya jima zauna yana ƙiyasta yanda yake son abubuwa su kasance masu tsakanin shi da ita kafin bacci mai nauyi shima yayi awon gaba dashi,Washe gari Janan ta tashi cike da farinciki a zuciyar ta bayan tarin mafarkai da tayi masu matuƙar daɗi da take fata su zame mata gaskiya, kasancewar weekend ne babu school yau yasa koda tayi sallar asuba haɗe da azkar ɗin safiya rana na hudowa takoma kan gado abunta ta kwanta taci gaba da baccin ta hankali kwance, bata farka ba sai kusan ƙarfe sha biyu, da alama shima yunwa ce ta tashe ta, toilet ta fara shiga ta wanko bakin ta agurguje ba tare data tsaya watso ruwa ba ta sauko ƙasa riƙe da wayar ta tana ƙoƙarin kiran Amira don taji ya mahaifiyar tata da jiki, saboda a cikin mafarkan da tayi jiya hadda nata sai da bata fahimci inda mafarkin ya dosa ba, haka kuma bata maida hankali akan sa ba saboda ta ta'allaƙa hakan ƙilan da zuwa dubata da take yi da kuma yanayin da ta ganeta aciki, sau kusan huɗu wayar na ringing amma Amira na kallo taƙi ɗagawa saboda haushin abunda ya faru jiya akanta da take ji har sai da umma dake kwance ta juyo tana kallon ta, ta ce
"ALLAH ya shiryeki Amira ya rabaki da mugun hali, waye haka ke faman kiranki kika ƙi ɗagawa?"
"Wani ne umma ƙyaleshi damuna zaiyi da ɓaƙin iyayi da surutu.." kafin ta rufe baki Al-amin dake kusa da ita zaune ya miƙa wuya ya ga mai kiran nata, ya ce
"Laaa..umma wlh ba wani bane, Janan naga an rubuta" ce ki da takaici ta yunƙuro da niyar kai masa duka Zarah ta janye sa tana dariya,
"Jimun aunty Amirar nan, daga faɗan gaskiya sai duka?, ALLAH shiyasa nace aunty Janan tafiki kirki, da alama fa umma kiranta tayi ta tambayeta ya jikin ki amma take yimata haka, ALLAH ba kyau ki dena, don wlh da nice ita da tuni na barki"
"Ƙyaleta zarah, muƙamin wayar"
Turo baki tayi tana makawa Zarah harara haɗe da cewa umma,
"Kiran fa ya tsinke, kuma bana da kati awaya" ta ƙare zancen tare da miƙa ma Umma wayar, girgiza kai umma tayi haɗe da cewa,
"Zarah jeki ɗauko ɗari biyu na nan kan madubi ki siyo kafin na Naira ɗari, ina laifin yarinyar nan wlh ki sauya hali in kina sauyawa, inba haka ba wannan halin da kikeyi mata wata rana shi zai kaiki dajin kunya da kuma nadama" ƙafafuwa Amira tashiga shurawa tana faɗin,
"Kai umma, kai Umma, yanzu fisabilillahi baki kike mun akan ta?, Kenan tafini awajen ki"
"Ko ɗaya, Ni ba haka nake nufi ba, yarinyar nan ba kida aiki sai aibanta ta da musguna mata bacin tana biye dake da alkhairi akoda yaushe, ina guje maki kada wuɗan nan abubuwan da kike yi mata su janyo maki faɗuwa ita kuma ɗaukaka, kinga alokacin dole kiji kunya kuma kiyi nadama"
"Amma umma wanda nake so fa taje ta rabani dashi, kuma don munafunci zata riƙa shiga jikina da sunan tana so na, to a ina aka taɓa so haka?"
"Banda abunki ai ba ita tahana ya soki ba, shi ya zaɓe ta ya barki sai kiyi haƙuri har kema ALLAH yakawo maki wanda zai so ki kema"
"Ni umma bazan taɓa haƙura da mm ba, yanda take son shi haka nima nake son shi, don haka zanci gaba da addu'a ALLAH ya mallaka mani shi koda ya aureta nima ya soni fiye da yanda yake son ta"
"To alhamdulillah, indai addu'a zakiyi ai ba laifi, nima sai in tayaki ALLAH ya zaɓa maki mafi ƙololuwar alkhairi"
"Umma kenan! Ai mm alkhairi ne gareni, kawai ki roƙamun ALLAH ya mallaka mani shi, zanyi farinciki sosai" da mamaki umma take kallon ta, don ko a mafarki akace mata Amira zatayi irin wannan shirmen bazata taɓa yadda ba, amma sai gashi agabanta takeyi ba tare da ta ji kunyar taba, gaba ɗaya tarasa wane irin so ne haka take wa yaron nan, sallamar Zarah ta dawo da umma hankalinta dake faɗin,
"Umma Sa'idu mai shagon baya nan, sai dai in can bakin titi Al-amin zai je ya karɓo"
"Bashi yaje, ka siyo duka na ɗari biyun, inyaso ta bani naira ta ɗari inta samu"
"A'a Umma, ni ba ruwana da kati in dai ba sos zanyi ba, duk wanda ya damu da son waya dani ya kirani kawai"
"Eyyeeee, to sannu ƴar gwal, koda yake wazai kiraki in ba Janan ba tunda itace mai iya haƙuri da halin ki?" Turo baki tayi tana ƙoƙarin sake magana sai ga Janan ta sake kira, "ungo Zarah miƙa mata wayar ta"
Zarah na karɓa taga Janan ce ta sake kira da sauri ta ɗaga haɗe da karawa a kunne,
"Hello aunty Janan, Ina wuni?"
Cike da fara'a Janan dake zaune a ɗaya daga cikin farare kujerun dake cikin guiden ɗin dake can bayan ɗakunan su ta ce,
"Ahhh...Zarahty kina lafiya?"
"Lafiya lau aunty Janan, ya gida ya gajiyar jiya?"
"Alhamdulillah, ya jikin Umma?"
"Ta samu sauƙi sosai"
"Masha ALLAH, ina Auntyn taki? Na kira sau barkatai bata ɗaga ba" saida Zarah ta kalli gefen da Amira take zaune sannan tayi dariya haɗe da cewa,
"Tana tsakar gida tana wankin bayi (toilet) shiyasa..." Kafin tarufe baki ba Amira data zaro idanuwa tana sauraren ƙaryar da take sheƙa mata tayo kanta, aikuwa da sauri ta miƙe tare da miƙawa Umma wayar tana faɗin,
"Wayyoo...., Aunty Janan ga Umman" ta kwasa aguje tana zagayar falon Amira na biye da ita tana cewa,
"Yau sai kin faɗa mun uban waye ya sani wankin bayi"
Haka ta riƙa binta aguje suna ta gudu har tsakar gida tana ƙoƙarin kamata, sai da Zarah ta gaji don kanta sannan ta tsaya haɗe da duƙewa ƙasa ta tura fuskarta cikin cinainanta tare da ɗago hannayen ta tana faɗin,
"Wayyo Aunty Amira don ALLAH kiyi haƙuri bazan ƙara ba"
"Badai kin rena ni ba, ALLAH yau zanyi maganinki" ta ɗaga hannu tare dakai mata dundu a baya, har zata sake kai mata dundun a karo na biyu Umma ta ce,
"Karki kuskura ki sake dakar mun yarinya, zo ki karɓi wayar ki Janan na akan layi, babbar banza babbar wofi" duk da haka saida takai mata ranƙwashi akai haɗe da cewa,
"Zamu haɗu ne yarinya" girgiza kai kawai Umma tayi tana mai addu'ar ALLAH ya rabata da zafin rai, da biyema ƴan ƙannen nata da takeyi akoda yaushe.
Tana karɓa Janan dake faman dariya jin abunda Umma tafaɗa ƙarshe, ta ce
"Kai Aunty Amira, in angirma asan angirma fa, ya kina takurawa yaran umma haka?, zafa mu saidaki mu huta" cikin ɓaci rai Amira ta ce,
"To ku saida ni tunda akuya nake ko shanuwa" tayi tsaki sannan ta kashe wayar cike dajin haushin ta, dariya Janan ta riƙa yi sosai har saida tayi hawaye, ire-iren wannan saurin fushin na Amira wani zubin akan abunda baikai ya kawo ba kan bata dariya wani lokaci kuma ya bata mamaki, shiyasa sam bata ji haushin abunda tayi mata ba yanzu sai ma dariya da abun ya bata, wai tunda ita shanuwa ce ko akuya, ta sake saka wata dariyar, tana a haka Nihal ta iskota,
Ɗan turo idanuwa tayi haɗe da cewa,
"Tofah! Janany sister yau soyayyar ta dariya ce?, Tun fa a falo nake jiyo wannan dariyar taki"
"Bari Adda, Ni da ƙawata ce Amira"
"Au na zata ma da mm ne daɗin soyayya ya sa kike wannan ƙyaƙyatawa haka?, Mtssss...da alama kuwa in kika ci gaba da biye mata zata mai sheki mahaukaciya" ta ƙare zancen cikin ko in kula tare da wucewa ta haye kujera ɗaya itama tana latsar wayar ta.
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭*