CHAPTER 1

2.2K 75 3
                                    

CUTARWA!

P1

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

⚠️⚠️
*Ƙirƙirarren labari ne, duk abun da aka gani a ciki, yayi kamanceceniya da wani abu, na zahiri ko makamancin haka, arashi ne*

*Haƙƙin mallakata ne, ban yarda a juya mini shi ta kowacce irin siga ba, sai da izinina"

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

Gagarawa Jihar jigawa.

Kasancewar wata ya nausa, domin kuwa watan jumada ula, ya kai kwanaki ashirin da biyar, wanda yake dai-dai da watan Nuwambar shekarar miladiya.

Mislain ƙarfe biyu da rabi, dare ya tsala, duhu ya mamaye ko ina, baka jin sauti ko motsin komai, sai kukan ƙananan ƙwari, da sautin busassun ganyen bishiyu, da iska ke kaɗawa lokaci zuwa lokaci.

A dai-dai wannan lokacin da kusan galibi mutane ke kwasar bacci, ni kuma har a lokacin idon ta tamkar an soya, babu alamar bacci a tare da idanun nata, sakamakon bushewar zuciya da raɗaɗi da take ji.

Sai yau ta tabbatar da cewa, nutsuwar zuciya, da kwanciyar hankali, da ƙarancin tunani, suke haɗuwa su haifar da daddaɗan bacci, mai cike da annashuwa.

A hankali ta tashi daga kan katifar da take kwance, na nufi tagar ɗakin, ta buɗeta, wani sanyi ya daki fuskarta, ta kalli ƙaton tsakar gidan, da baka iya gane komai a cikin sa, saboda duhu.
Ta ɗaga kanta, ta kalli taurari, yadda suka yi wa sararin samaniya ado, ƙudura da iko na Ubangiji na riƙe da su a sama.
Tayi ajiyar zuciya, tare da kamanta rayuwarta da wannan baƙin daren, mai cike da duhu, da ban tsoro.

A lokacin da karin maganar bahaushe ya yi amsa amo, a tsakanin ƙabilar ta hausawa, na cewa dauɗar gora ciki ka sha ta, sai dai kash! Zamani ya zo mana da cigaba, ta hanyar nuna mana muhimmancin lafiyarmu.
Duk da cigaban da aka samu, hakan bai hana a tauye ta ba, a shayar da ita dauɗar gorar ta ƙarfin tsiya ba, wanda hakan yake CUTARWA! Domin kuwa ya zame mata tamkar guba, domin ya zama silar sanya mata ciwon da take ta fama da shi, ta rasa maganin sa, wanda tun yana ɓoye, sai da ya fito yayi tsiron da mutane suke yi mata tambari da shi.
Haka zalika, azancin hausawa na ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ya samu gindin zama a da yawa daga bakunan mata, sai dai ita a nata ganin, ciwon ƴa mace, na ta ne ita kaɗai. Wataƙila ko a cikin ta ta rayuwar ne Allah bai sa ta yi katari da waɗanda ciwon ƴa macen yake zama nasu ba.
Duk iya ƙoƙarin da ta yi wurin haɗiye yawun bakinta, ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi, wani irin zafi zuciyarta ke yi mata, wanda ya haddasa numfashina fita cikin huci.

A hankali ta furta "Me ya rage? Tun da duniya cike take da rikici, da tarin ƙalubale, kowa kansa kawai ya sani, kuma kuɗinka shi ne mutuncinka, tabbas! Tura ta kai bango, na ɗaura aniyar fito na fito da duk waɗanda suka cutar da ni. Tun da babu sani babu sabo, dole in fasa ƙwan da warinsa ka iya sanadiyyar tarwatsewar zumunci, idan ya so na gani, ko suma suna iya jure ɗaɗɗake dauɗar gorar a cikin su, kamar yadda suka yi mini, daga nan na ƙara gaba, na basu wuri tare da gwagwarmayar nemawa kaina mafitar rayuwa.

*****
La'asar sakaliya, wata matashiyar mace ce da ba zata gaza shekaru sha takwas a duniya ba, zaune a ƙaton tsakar gida, tana ta ƙoƙarin tsince waken da zata daka, ta zuba a cikin miyar yauƙin da take yi, cinyarta wata yarinya ce ƴar kimanin shekaru uku da rabi a duniya a kwance, ta saka babban ɗan yatsanta a baki ta na sha, hannunta ɗaya kuma tana wasa da cibiyarta.
Idan ka kalli yarinyar sau ɗaya, sai ka sake kallonta, tare da son sanin daga wace ƙabilar wannan yarinyar take?.

Baƙa ce sosai, mai ƙiba, tana da ɗan goshi, sai dai yalwataccen gashin girarta ya rage fitowar goshin nata, tana da manyan idanuwa farare, sai dai ƙwayar idonta brown ce, maimakon baƙa, bakinta ɗan cukul, sai dai laɓɓanta jawur, tamkar an saka mata jambaki. Babban abun da zai baka mamaki, bai wuce yadda take da dogon gashi ba, baƙi wuluk, mai tsayin gaske, ba curkukuɗaɗɗe irin na baƙaƙen fata ba, tamkar gashin larabawa, kalba aka yi mata guda biyu, amma ta saukko har cikinta, hancinta ba shi da wani tsawon kirki, saboda kumatu ya shanye su.

CUTARWA!Where stories live. Discover now