*CUTARWA!*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)arewabooks ayshercool7724
Watpad ayshercool7724
Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovelsP7
A guje mama ta koma tsakar gida, tana ƙwalawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi.
Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo maƙwabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti.Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ƙafar ummi, ya ƙarasa da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi.
Wani irin baƙin ciki ya turnuƙe masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar ɗan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba.
Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa mari, yana ball da shi, yayi masa dukan tsiya, sannan ya ɗaukko ummi ya shiga da ita gida.
Gaban iya ne ya faɗi ganin yadda ya shigo da ummi, ta miƙe tana faɗin lafiya?.
"Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje"
"Saboda iskanci, me tayi masa?"
"Oho masa"
"Kema uban waye ya ce ki fita?" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye.
Ya ce "Dan Allah iya ki yi haƙuri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaɓi"
Ya karkaɗe mata ƙasar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita ɗakin gwaggo ya kwantar da ita.
Iya kuwa mita take tana "Na rasa wannan baƙin jini na yarinyar nan, ƴa sai ka ce mujiya, ƴan uwanki yara ma gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba ɗaya kalarki ba irin ta mutane ba" Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa tsoronta yake ji.
Duk yadda likitoci suka yi ƙoƙarin ceto ran mariya da yaronta, Allah bai yi ba, yaron ya zo babu rai, kuma alamu sun nuna ya kwan biyu da mutuwa a cikin ta, saboda yadda fatarsa ta fara marmasowa.
Sai dai har kusan kwana biyu da haihuwar ta, an kasa samo kanta yadda yakamata, da magani ya sake ta sai jini ya sake hawa.
Sai suka shafe sati uku a asibiti, sannan aka sallame su, suka koma gida, sai dai abu idan ba ya zama dole ba, ba ta magana.
Tunani kawai take yi, ko ta saci jiki ba a sani ba ta je ganin ummi, amma ta tuna wulaƙancin da iya ta yi wa yayyenta, ta san muddin ta je, ba abun da zai sauya, kuma hakan tamkar watsawa mahaifinsu da yayyenta ƙasa a ido ne.
Ummi ba wanda yake kula da bata magani, sai idan magaji ya shigo sashin Iya, ya sanya ta a gaba ta sha, duk da iya ta ƙwace kuɗin da kawunsu ya bawa ummi, da kuɗinsa ya saya mata yadin uniform, ya canza mata nata da suka yayyage suka yi mata kaɗan.
Ummi ta ji daɗi sosai da sosai, ga sabuwar jakarta dan haka cike da ƙwarin gwiwa take zuwa makaranta.
Kafin kwana bakwai, tuni kan ummi ya cika da gashi, kamar ba ayi mata aski ba, kalar wanda ya fita kalar sa ne dai yake sake fitowa a kanta, ba baƙi ne wuluk ba.Duk wannan murnar da take yi na komawa makaranta, da tarin ƙoƙarin da ummi take da shi, ya zama a banza, saboda ko tambaya aka yi a aji, ba ta iya bayar da amsa, saboda gudun cin zarafi da tsokana da ƴan uwanta ɗalibai za su yi mata, koma malaman da kansu.
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...