*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
39
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Alhamdilillah ala kulli halin, ina amfani da wannan damar, wurin isar da ɗimbin godiyata ga ƴan uwana marubuta, tarin masoya makaranta, da sauran al'ummar da suka yi mini ta'aziyyar rashin kakata, ina fatan Ubangiji Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, ya kuma bar zumunci, yayi mana jagora a rayuwa baki daya, Allah ya sanya kaburburan magabatanmu ya zama dausayi daga aljanna, idan tamu ta zo ya sanya mu cika da imani*
39
Alhaji ya ce "Jidda ya haka ne? Wace irin magana ki ke yi kuma?"
Hajiya ta ce "Kaga ƙyale ni na faɗa, ai a baya ban taɓa yi ba, sai mu gani idan dabarar mutum za ta ƙwace shi, me aka yi da maza ko sati uku ba a rufa ba fa? Baki ga komai ba"
Mami kuwa kumfar baki ta din ga yi tana cika baki, Salim ya tashi tsam ya fice, dan baya son hayaniya, hajiya ma ficewa tayi ta bar ɗakin.
"Ka gani ko ka ga abun da ka janyo mini ko?"
Kamar raihan zai fashe da kuka ya ce "Mami me kuma na yi?"
Alhaji ya ce "Raihan bai yi miki laifin komai ba, ke ki ke ƙoƙarin koya masa rashin gaskiya, da kuma raina ki, wuce ka jirani a mota, mu je a kashe wancan case ɗin da ka ɗaukko" Raihan ya fita yana satar kallon mami.
Alhaji ya sake mayar da idonsa kan mami ya ce "Gaskiya hajiya ta gaya miki, na sha gaya miki mu maza idan muna kan wannan gigin da rawar kan, ba a cewa za a tanƙwaramu ta ƙarfin tsiya, ko da kuwa iyayen da suka haifemu ne, ke meye ban yi ba a kanki?
Ko kin manta yadda na ɗauke ki, na bar ƙasar sama da wata uku na bar hajiya, na toshe kunnena, na ƙi saurara kowa sai yanzu dan abun ya zo kan ɗanki ki ce ba ki san zancen ba? Shiyasa a kowane ƙadami ake so ka zama mai adalci, ko dan gaba, baki nuna mini illar abun da na din ga yi ba, sai daga baya da na gane kuskurena dan kaina, ka kwanta da mace kawai ba shi ne aure ba, wannan abu ne na lokaci, managarciyar mace mai tsoron Allah, da kuma biyayya ita ake fata. Amma idonki ya rufe dan ɗanki ya auri bazawara, sai me qualities ake dubawa ga mutum mai hankali, ba wai abun da ku ke tunani kawai quality na mace ba" da farko faɗa yake yi mata, daga bisani kuma ya koma nasiha, ya gama ya fice daga ɗakin ya bi raihan.Ko kaɗan mami ba ta ji nasihar Alhajin ta shige ta ba ma, babban burinta a yanzu kawai, shi ne raba ummi da raihan tun kan ta kanainaye shi gaba ɗaya.
Ba dan tare da Alhaji raihan suka je station ba, da sai raihan ya ja case ɗin, dan kuwa babbar headquarter hukumar ƴan sanda yasa aka kai su, kuma ya tafi da wayar ummi a matsayin shaida.
Alhaji ya ce wa raihan, ya kai shi gidansa, yana son yin magana da shi da ummi gaba ɗaya.
Suna tafe yana yi wa raihan nasiha.
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...