CUTARWA!
AYSHERCOOL
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
45
PAID ADVERT
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
45
Raihan ya rasa ta ina zai fara kare kansa ma, haka yayi shiru Alhaji ya gama faɗan ya kashe wayarsa.
Kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa, haka ya ƙarasa cikin asibitin, ya taimakawa ummi ta wanke baki, ya haɗa mata tea da dankali yana bata. Cikin ɗari-ɗari take ci, dan ta san ƙarshen abun ta amayar da abun da ta ci, ga yunwa tana ji sosai.
"MD ka ga wancan cikin ban san ma da shi ba, ban yi laulayi ba wannan kuwa sai wahala nake sha"
Yayi murmushi da ƙyar ya ce "Wancan kin ci bonus"
"Wai ya na ganka duk wani iri ne? Na san zaman asibiti da gajiya, ba daɗi shiyasa gara ka mayar da ni maiduguri"
Raihan ya ce "No, ba gajiya na yi ba, da ke da babyna kuna buƙatar kulawata. Ai gazawa ce in ce ki koma gida dan baki da lafiya, ni zan yi abun da ya dace na kula da ku"
Tayi murmushi ta ce "To aikin fa?"
"Shima duk zan iya"
"Ɗan Aljannana, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya barmu tare har aljanna"
Ya amsa mata da Amin, ƙasan zuciyarsa yana fargabar hukuncin Alhaji, dan daga ji ya ɗau zafi sosai.
Yadda ta gama cin dankalin nan, sai da ta amayar da shi gaba ɗaya, abun har tsoro yake bawa raihan, duk ta rame saboda laulayi.
Yana nan zaune tare da ita, har ta samu bacci, bayan wasu awanni ta din ga jin hayaniya kamar a mafarki. Ta buɗe idonta, ta ga Alhaji a ɗakin tare da Salim, ga raihan a gefe ransa a haɗe sai kuma likita a tsaye da file.
A hankali ta tashi zaune, tana mamakin zuwansu ta ce "Alhaji sannu da zuwa"
Ya dubi Ummi ya ce "Sannu ya jikin? Dan Allah kalli yadda duk ta bi ta ƙare ta rame, meke damunta ne? Ko kuma duk tsiyataku da rashin mutuncinka ne ya sanya ta rame" Yayi maganar yana kallon raihan.
Likita ya ce "Ahh ba wani abun damuwa bane, laulayi ne na mata, ba ta iya cin komai shiyasa muka ajiyeta mu ke ta saka mata ruwa"
Alhaji ya ce "Ka rubuta mata sallama, gida kano zamu tafi, za a cigaba da kula da ita a can"
Ya mayar da idonsa kan ummi ya ce "Banda abunki ummi, gani menene amfanina? Ko dr. Ba ya nan wani abu ya haɗaku sai ki zo ki gaya mini, ni ƴa ta ce ke ba sirika ba, kawai sai ki biye masa ki tafi wani wurin ace ba a san ma in da ki ke ba? Kuma dan baka da kunya ka lallaɓa ka mayar da ita ka taho da ita nan ba wanda ya sani, hankalin mahaifinta na can a tashe bai san ina take ba, ka bani kunya" daga ummi har raihan aka rasa mai magana, ummi ba ta taɓa zaton Alhaji ya iya faɗa haka ba, saboda kullum fuskarsa cikin murmushi yake.
Haka aka sallami ummi, suka nufo kano, raihan ya sha faɗa a wurin Alhaji,kuma yayi shiru bai ce komai ba ummi gaba ɗaya ta ji babu daɗi.
Asibiti suka zarce da ummi, aka cigaba da ba ta kulawa ta musamman, saboda suna tafe a hanya ma tana amai.
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...