30

796 52 3
                                    

30

Kamar a mafarki ummi ta ga abun da raihan yayi, ba ta taɓa zaton zai aikata abun da yayi mata ba.

Ƙirjinsa har wani zafi yake yi, ji yake tamkar ya koma ya saurareta, amma ya dake, ya samu wuri ya tsaya yana hangen ta, ta fito jiki a sanyaye ta bar harabar rukunin ofisoshin.

Ya din ga jin kamar ya bi bayanta, amma ya tattara dukkanin jarumtarsa yaƙi bin ta.

Ummi ta daɗe tana tunani, me raihan ya yi wa malam isa, da kai tsaye ya ce ya fara aurenta haka, duk zumuɗin da yake yi da rawar kai a kanta.

Ta tura wa raihan saƙo ta what's app "Raihan, na zo wurinka mu yi magana shi ne ka yi mini wulaƙanci, abun har ya kai haka?" Yana online bayan gama karanta saƙon yayi blocking ɗin ta gaba ɗaya.

Ɗan ƙaramin sauro, mai hana giwa bacci, duk wata hanya da ya san zai bi ya kunna ummi, ya ɓata mata rai ya din ga bin ta.

Sai dai kusan kullum yana kan waya, yana duba hotunanta ta tare da chat's ɗin su.

Yana sashen hajiya yayi ɗai-ɗai, ta saka an kawo masa abinci amma ko taɓawa bai yi ba, Ta ce "Babban mutum, wai sai abincin ya gama hucewa zaka ci?"

Ya sake kashingiɗa ya ce "Ba irin wannan nake so ba"

Ta zauna ta ce "To wanne ka ke so? Duk ka rame wallahi, anya ma kuwa kana cin abincin?" ya kwaɓe fuska ya ce "Ba mijinku ne duk ya ja nake ramewa ba"

Hajiya tayi dariya ta ce "Ƙaniyarka wato mijinmu"

"Eh mana"

"To tashi ka ci abincin"

"Hajiya ki ƙyale abincin nan, bana jin daɗin komai wallahi, ga gajiya ta dameni, abincin ummi nake son ci, kuma mun yi faɗa"

Hajiya ta ce "Wacece kuma ummi, da abincinta ya fi na hajiya, bani labari"

Ya tashi zaune ya ce "Ina ga hajiya auren nan fa zan yi, amma wadda nake so zan aura"

"Ahh Alhamdilillah ai haka ake so, fatanmu kawai ka kawo mana ta gari, mai tsoron Allah"

"Baku da matsala da wannan, amma dan Allah hajiya ki yi ta yi mini addu'a, Allah ya tabbattar mana da alkhairi"

"Addu'a kullum a cikinta muke ai, Allah ya shiga lamarin ku"

Ya ce "Amin ya rabb Hajiyarmu ba irin ta kowa ba" yayi maganar yana zuba ruwa a kofi.

Salim ne yayi sallama, suka amsa masa baki ɗaya, ya ƙarasa gaban hajiya ya ce "Dan Allah mukullin motarki zaki ara mini, zan je wani wuri ne"

Hajiya ta kalleshi ta ce "Ina taka?"

"Tana wurin gyara, batirinta ya samu matsala"

Hajiya ta ce "Ka je ka hau ta haya, ba zan baka mota ta, ka rugurguzo mini ita ba, ba zan iya tunkarar Alhaji canza mini wata nan kusa ba, ko ka ɗauka a sauran biyun da kuka lalata"

Raihan ya ce "Dan Allah ki bashi mana"

"Ba zan bayar ba"

"Ai Allah na ce, i will take the responsibility idan ta samu matsala"

"Iyee, ka fi son ɗan uwanka a kaina, ba zan bayar ba nace"

Raihan ya ce "A'a ba haka bane ba, amma dai a taimaka, baki san me zaki samu a sanadin hakan ba".

"Ni fa lallaɓa mota ta nake yi, idan na bashi duk sai ya lalata ta".

Raihan ya din ga yi mata daɗin baki, har ta bawa Salim mukullin.

Rabon da a canzawa hajiya mota, kusan shekara biyar, motocin ta uku na hawa ɗaya ce ma mai tsada, sauran duk yaran gidan sun kashe su, duk babu wata latest, mami kuwa kusan duk shekara sai ta saka Alhaji saya mata mota, ta sayar da nata, ko tayi kyautarsu, hajiya kuwa babu ruwanta, dan haka raihan yayi niyyar yin surprising ɗin ta.

CUTARWA!Where stories live. Discover now