*CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)P13
Iya ta ce "A'a Yahaya, kar mu yi haka da kai, wannan abu ne na cikin gida da yakamata a sasanta shi, wannan ai sai asirinmu ya tonu, duniya ta zage mu"
"Iya zagi na nawa kuma? Kalli jikin yarinyar nan fa, baiwar ubansa ce ita? A gabanki a gaban ubansa yake aibata ta yake cewa baya son ta, baya ƙaunarta, wallahi dole ya saketa, zan je da ummi ta cigaba da karatunta".
"Gaskiya ban lamunta ba yahaya, ba zaka ɓata zumunci ba da abun da na ƙulla dan ƙarfafa zumunci ba".
Hashim da bai yi niyyar sanya baki ba, sai da ya ga abun na iya yaƙi ci ya ƙi cinyewa ya ce "Iya wane zumunci kuma banda wanda aka ɓata?"
"Rufe mini baki dan ubanka, ai duk kai ne munafikin da ka kunno kowacce wuta, ban yadda a tafi da ummi ko ina ba, ko auren ya mutu, muna nan a bar mini ita".
Yahaya ya kalli Iya ido cikin ido ya ce "Wallahi iya idan ki ka hana ni tafiya da ummi, zan ɗebowa idiris hukumar kare hakkin ɗan Adam, su bi mata hakkinta, kuma idan suka tashi, har ke ba zasu bari ba, da duk mutanen gidan nan, na farko ga child abuse, by forced marriage, kun mata auren dole da ƙanan shekaru, ga dukanta da ci mata mutunci, deformation of character ɓata mata suna, ta hanyar yaɗa larurar da take fama da ita a cikin mutane, wanda duk ya zo kunnena tun kan na zo nan na samu lanari, kuma mariya ma zata iya shigowa cikin lamarin nan, ƙwace mata ƴa babu dalili da ki ka yi, dan dai suma ba su san ƴancin su bane, da sun haɗa ki da hukuma, da sai kin basu ƴar su".
Saminu ya ce "A'a yaya yahaya, ba za ayi haka ba"
Cikin rikicewa Iya ta ce "Yahaya ni zaka kai ƙara hukuma ka saka a rufe ni?"
"Ba ƙararki zan kai ba, ƙarar wannan sakaran zan kai, idan kuma na kai ƙararsa su hukuma zurfafa bincike zasu yi, ina gaya miki abun da hakan ka iya haifarwa ne, kai kuma ɗauki takarda da biro, ka sakar mini ƴa, ko daƙiƙancin naka bai bari, ka iya rubutun ba?"
Cikin kumbura baki ya ɗauki takarda da biron, ya rubutawa ummi saki biyu.
Kawu yahaya ya karɓa, ya kalli ummi ya ce "Tashi in tayaki ki haɗo kayanki mu tafi"
Magaji ya ce "Bari na tayata" a hankali ta ce "Ai kayan suna can gidan, sai kuma kayana da ke ɗakin itace"
Kawu Yahaya da kansa ya tashi, ya je ɗakin itacen, ya ɗaukko vivar kayan ummi, sai dai ya ga tsummokara ne kawai, dan haka ya ce ba za su tafi da su ba.
Iya ta din ga harar ummi, amma ummi tayi kamar bata gani ba, magaji ya kawo kayan ummi.
Jama'ar gida suka taru, suna kallon ummi za ga tafi birnin kanon dabo gidan kawu yahaya, wasu na tausaya mata, wasu kuma na yi mata murna.
"Yahaya" Iya ta kira sunansa.
Ya amsa mata, ta ce "Ka yi mini alƙawarin ba za ka kai ummi wurin mariya ba, dan idan haka ta faru, abun da zai biyo baya ba zai yi mana daɗi ba".
"Abu ɗaya na sani, na ɗauki ummi tsakani da Allah dan inganta rayuwarta, ni ban san a in da mahaifiyar ta take ba, amma akwai lokacin da lallai dole a nemi dangin mahaifiyar ummi, ta gansu, dan babu in da shari'a ta ce a yanke alaƙa tsakanin uwa da ɗan ta, ko da kuwa kafura ce, abun da yake tsakanin ki da mahaifiyar ta daban, kuma bai kamata ya shafi ummi ba" Iya tayi muƙus, dan ba ta son yi wa kanta sagegeduwar ɗan abun duniyar da yake bata.
Sosai kawu yahaya ya yi wa ƴan uwansa ta tas, a kan abubuwan da suka faru a kan ummi, kasancewar shi ne babba suna girmama shi, duk da kaf ɗin su sun riga shi yin aure, dam su ba karatun boko suka yi ba, wasun su ma shakara sha tara suka yi aure, amma suna girmama shi sosai mussaman da yana da abun duniya.
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...