CHAPTER 11

527 20 1
                                    

                       *CUTARWA!*

*BRIGHT PENS (FREE BATCH)*

Mafaka gidan ƙamshi, na da kyakywan albishir ga amare uwar gida, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

P11

Haka a ka kai ummi, mata suka gama surutansu, wasu daga cikin maƙwabta da suka san irin rayuwar da ummi take yi, suka din ga tsinewa iya, mussaman ganin ɗakin da aka kai budurwa, da tsohuwar katifa, ko zanin gado babu.

Aka din ga ƙananun maganganu, sai dai babu wanda ya isa ya iya tunkarar iyan, ya gaya mata hakan, saboda iya bala'inta da tashin hankali, haka kowa yayi maganganun sa ƙasa-ƙasa.

A hankali kowa ya watse aka bar ummi, ƴan matasan yaran da aka bar ta da su, suka gaji da zama, ango bai shigo ba, suka watse suka bar ummi ko fitila babu.

Wani irin tsoro ya mamaye ta, da ta ji motsi kaɗan sai ta razana, shiru-shiru babu idiris babu dalilinsa.

Ji ta din ga yi a ranta, kamar ta tashi ta koma gida, dan wani irin tsoro take ji, kamar ace kyat ta zura da gudu, saboda duhun da ya mamaye ilahirin gidan.

Dare ya cigaba da yi, duhu ya sake mamaye ko ina da ko ina, ta yadda ko tafin hannunta ba ta iya gani, tun tana jin motsin mutane sama-sama, har gari ya koma yayi tsit, sai kukan ƙanan ƙwari. Cigaba da kuka ta yi cikin firgici, ta tashi a hankali ta leƙa tsakar gida, ta hango ƙofar gidan a buɗe, tsakar gidan kuma sai ta yi ta ganin abubuwa na yi mata gizo, saboda a tsorace take, kuma ga duhu.

Da sauri ta koma can ƙuryar ɗakin ta takure, bacci take ji sosai da sosai ga gajiyar aiki, ga ta biki, ga tashin hankali ga kuma dukan da ta ci jiya da daddare a wurin Iya.

Babu tsammani ta ji rugugin hadari, da walƙiyya ko ta ko ina, fashewa tayi da kuka, tana son tashi ta fita da gudu ta koma gida, amma tsoro ya hanata.
Tana nan zaune ruwa ya kece ya din ga zuba kamar da bakin ƙwarya, ta tashi da nufin ta rufe ƙofar ɗakin, amma ƙarfin zubar ruwan, da kuma tsawar da ake yi, ya sanya ta koma ta zauna tana cigaba da kuka.

Ruwa ya din ga feshi cikin ɗakin, wani irin sanyi ya mamaye garin.

Ruwa ya shigo ɗakin sosai ya jiƙe, sai dai bai kai kan katifarta ba.

Kasancewar bacci ɓarawo ne, ya kwashe ummi a nan zaune ba tare da ta shirya hakan ba.
sai da gari ya waye ya fara haske, sannan ta tashi a razane.

Ruwan da aka yi duk ƙasa ta shanye, ta zama taɓo, wani kofi ta gani a tsakar gida, ya cika da ruwan da aka yi, tayi alwala da shi, ta koma ɗakin tayi sallar asuba.

Tana nan zaune cikin zullumi da fargaba, aka yi sallama, wasu daga cikin ƴan biki ne suka zo, hakan ya sanya ta ji daɗi.

Suka din ga rafsa guɗa, ummi dai da ido kawai take bin su.

Suka kawo mata abun karyawa, ake tambayarta ina angon? Tayi shiru ba ta ce komai ba, dan kuwa ba ta san me za ta ce ɗin ba.

Suka ƙara yi mata ƴan gyare-gyaren da zasu yi mata, suna ta hira suna yi mata nasiha, da azahar suka ce za su tafi.

Ummi ta ɗau hijjabinta ta ce za ta bi su.

"Ki bi mu ina? Ai ko ƙofar gida ki ka fita babu iznin mijinki, Allah zai ƙona ki a wuta, ki koma ki zauna, shima yana ango amma safiyar fari ya fice, har azahar bai dawo ba?" Cewar wata dattijuwa.

CUTARWA!Where stories live. Discover now