CHAPTER 13

548 30 4
                                    


*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS
FREE BATCH

P13

Ihu ummi take yi, tana yi musu magiya su yi haƙuri, amma cike da mugunta da zalunci, rahama ta danne ummi a ƙasa, ta cusa mata ɗan kwali a baki, ta yadda sautin ihunta ba zai fita sosai ba, ta ɗage wa ummi riga, farida ta din ga nana mata iron ɗin nan a cikinta da zafinsa da komai.

Wata irin miƙa ummi take, saboda azabar da ta ratsata, take ta saki fitsari, saboda azabar zafi da ya ratsa ta.

Abdul har ya je ɗakinsa ya tuna ya ƙona rigar maama, kuma ƙila ummi zata hukunta, dan haka ya juyo da sauri, ya dawo falon.

A gigice ya ƙarasa wurin, ganin bala'i da izayar da ake yi wa ummi.

"Maama dan Allah ku bari, ba a yi wa mutum azaba da wuta".

Fitsarin da ummi ta saki, ya sanya rahama cikata, ta rufeta da duka, saboda ta ɓata mata jiki da fitsari, ta fizge hijjabi da hular kan ummi, a take dogon gashin ta mai matuƙar santsi ya zubo har fuskarta.

Rahama ta ce "Kut, wannan gashi ko attach" tayi maganar tana jan gashin ummi da ƙarfin gaske, ummi jikinta ya din ga rawa, ta kasa ihun saboda azaba, ta riƙe gashinta da rahama ta cika hannu da shi.

Abdul ya fara ƙoƙarin ture rahama daga kan ummi, farida ta kai ƙafa zata daki ummi, ta zame da ruwan fitsarin da ummi tayi, ta faɗi.

Wani irin ihu ta kurma, rahama ta ɗaga ummi, ta nufeta a gigice, ummi ta samu ta lallaɓa ta tashi da gudu, ta tafi ɗakinta.

Banɗaki ta shiga, ta cire rigarta ta din ga zuba ruwan famfo a cikinta, tana jin tamakar wurin ci yake yi da wuta, ga wani irin azaba da kanta yake yi, har wani jiri take ji.

Kan ka ce kwabo jini ya fara zuba daga jikin faruda, jikinta ya fara kakkafewa, rahama ta ce "Abdul yi sauri ka je ka taso abbanku" Abdul ya tafi da gudu ɗakin da mahaifinsa yake ta bacci, saboda a gajiye yake sosai, duk wainar da ake toyawa bai sani ba.

"Abba, Abba ka tashi maama ta faɗi ƙasa"

Da ƙyar ya buɗe ido, ya kalli Abdul ya ce "Meyafaru?"

"Maama ce ta faɗi a falo" agogo ya kalla, ɗaya saura na dare, me ta je yi falo a yanzu?". Ya saukko daga kan gadon, suka fito falon tare, falon sai ƙauri yake yi saboda iron da aka bari a jone.

Jini take zubarwa sosai cikin gushewar hankali, da sauri kawu yahaya ya ɗaukko mukullin motarsa, da ƙyar suka ɗaga farida, saboda nauyin cikin ta suka bar Abdul a gida suka tafi asibiti.

Ummi ba ta san abun da ake ciki ba, tana can tana jinyar cikinta da suka ƙona da dutsen guga.

Ta zauna ta yi shiru tana ta tunanin, me ta aikata da ya sanya kowa ba ya son ta ji daɗi, kowa babban burinsa shi ne ya ga ya cutar da ita ta yi kuka?

Ta ɗauki vasaline ta shafawa wurin, duk da haka sai da ya fara ɗurar ruwa, duk fatar cikin ta tashi.

***
Idiris a tunaninsa tafiyar ummi, shi ne samun sassauci a gare shi, ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda.

Hashim kuma Iya ta sako shi gaba da cin mutunci, ko gaisuwarsa ta daina amsawa, saboda haushin gayawa kawu yahaya abun da ake ciki da yayi, ya sanya yahayan yana yi musu kallon azzalumai.

Idiris ya lallaɓa ya cigaba da zuwa wurin hindu, yana son ya hilace ta su aikata alfasha, tun da iyayenta sun ƙi ya aureta.

Gulmace-gulmace suka din ga yawo, a kan azabtarwar da Iya ta yi wa ummi, da wanda idris ya yi wa ummin, tare da ƙoƙarin bankaɗa asirin dalilin da ya sanya aka fasa auren idiris da hindu, ana ta zaginsu a unguwa, aure wata ɗaya ya mutu.

CUTARWA!Where stories live. Discover now