CHAPTER 2

793 37 1
                                    

                     *CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube Cool hausa novels
What's app 08081012143

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P2

Yawan kyara da hantara, haɗi da kushe halittar ummi, ya sanya ta zama yarinya mara karsashi ko a cikin sa'aninta. Dan wasu har iƙrari suke ko mayya ce, saboda launin ƙwayar idonta da ta sha banban da ta sauran mutane.

Wasu lokutan mariya duk sha'anin da za ayi na taron mutane, ta kan iya haƙura da zuwa saboda ummi, ba ta son mutane.

Abubuwan da wasu daga samarin gidan suke yi mata ne, ya sanya ta sake tsorata da lamarin mutane, ta fara ganin tamkar ita ta ta duniyar daban take, dan idris ne kawai yake amfani da ita wurin biyan buƙatar sa ba.
Mariya bata taɓa fuskanta ba, wasu lokutan har tsoron nuna wa ummi kulawa take yi, a gaban iya, saboda yanzu zata hau masifa da faɗa, wai tana nuna wa ƴar fari soyayya saboda ba ta da kunya. Ko yaya ummi ta ɗan sake a cikin yara, sai su fara cin zalinta, ko su din ga jan dogon gashin ta, ko jan kumatunta da suke tamkar doughnut ya ji yeast, ko yi mata dariya da ihun baƙar tukunya mai ƙyalli.

Takurar yara ya takureta a gida, a gidan ma iya sashinsu, shi ma fitowa tsakar gida idan ba tare da mamanta ba, ba ta fitowa saboda hantarar da kyarar da iya take yi mata.

Haka rayuwar gidansu ummi ta cigaba da garawa, iya kullum tana cikin haba-haba da ƴaƴa da jikokinta, masu kawo mata abun duniya.

Yayin da ta tattara cin kashinta, a kan balarabe da iyalin sa, tamkar ba ita ta haife shi ba.

Ummi ta ɗan ƙara tasawa, kusan kullum sai ta tambayi babanta, yaushe za a kaita makaranta.

Ganin ta ɗan tasa, kuma idan tana tare da mahaifinta, ko mahaifiyarta, ta kan yi hira da su. Sai dai da tayi yinƙurin gaya musu, abun da su Idris ke yi mata, sai ta kasa ta tsorata idan ta tuna suna cewa za su yankata.

Babanta yana bata lokacin sa, yayi wasanni da ita, har da ƴar tsere a tsakar gida. Da iya ta ganshi kuwa ranar ya shiga uku, da masifa da gori.

Kasancewar garin sun ɗan samu cigaba da wayewa, yanzu ana yin karatu sosai, akwai makarantu, ya sanya balarabe ya kai Ummi makarantar gwamnati, aka saka ta a ECC.

Ta din ga murna ganin an saka mata sabon uniform, fari da kore, ga jakarta baba na gode, an saya mata sababbin litattafai, sai washe fararen haƙoranta take yi cike da yarinta.

Tun sha ɗaya da rabi, mariya ta cewa iya zata je ɗaukar ummi a makaranta, iya ta ce "Mariya wai meyasa ba ki da ta ido ne? Ni zan ƙarasa girkin kenan, ki bari ta biyo yara, ko idan su Auwwalu sun dawo sa ɗaukkota. Ni kaita makarantar ma, Allah ya sa ba asarar kuɗi ba ne ba, kar aje yadda fuskarta take haka ƙwaƙwalwar take, ayi biyu babu".

Wani abu mai ɗaci ummi ta haɗiye, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ta faki idon iya, ta ɗau mayafi ta fice ɗaukko ummi, duk da babu tazara sosai, amma yarinya ce ƙarama, ba ta san hanya ba.

Sai dai da ta je ɗaukar ta, ba ta ganta tana wannan murnar kamar lokacin da za a kaita makarantar ba.

Tayi zaton kawai ta gaji ne, dan da yawa yara na ɗokin makaranta, sai an kai su kuma, su ga ba abun da suke so ba, su ce ba sa so daga baya.

Mariya tana cire mata uniform ta ce "Mamana, me aka koya miki a makarantar yau?"

Cike da yarinta ta ce "Lemo aka zana mana"

Tayi murmushi ta ce "sai kuma me?".

"Bana son makaranta, ba zan sake zuwa ba?"

"Subhanallah, ummina meyasa?" Ta yi maganar cikin kulawa.

CUTARWA!Where stories live. Discover now